Sashe 163
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
barar da mutuncin nata. Yaron nan Yazidu ya kyauta min ashe duk dadewan nan aurensa yayi a can bai fadawa kowa ba sai kwanan nan ya sanar da yayansa hakan. Harda haihuwansa yanzu gashi zai dawo gida saita sake maki mara ita da magoya bayansa su farwa matar nasa kuma tunda karuwane basu so cikin zuria. Yayi aure iya na tambaya cikin mamaki tace yayi aurensa wallahi matarsa harda haihuwa biyu tayi mashi mace dana miji yara masu kyau kamarki haka ? Taso tayi fada nace fadan me zakiyi abinda yake sone yayi banga dalilin sakawa yara ido kan zama da iyalinsu ba don ita aiba haka mukai mata ba. Zai dawo dai yanzu wanan gidan na kusa daku da ake gyara a nan zai zauna shima habu ashe duk nan zasu dawo din da zama. Ai Jafar shine maganinta da yake abinsa yanzu ba shawara sai ya gama yake fada masu wai kuma sun samu hakan sun tsaya fadan jin dadi. Nayi masu tas yau haka kuma nace dashi munafukin yayi gagawan kai yar uwarsa inda sukaje can wai wani bakin ruwa wajen wasu masunta masu bin ruwa . Har can yaje ya samo abinda ya zama wahala a yanzu garesu tun lokacin na fada mai suyi hakkuri komai na Allah ne amma basuji ba Allah dai yasa su samu matar a raye ? Amin na amsa dashi yayin da gabana ya fadi don in bata raye hakan yana nufin rayuwan yaya yana cikin matsala ke nan ? Har ya dawo da kaya niki niki Biba ta fita tayi ta kwasowa har abinda muke dashi da yawa duk ya karo muna anzuba a kitchen din mu na mike mukai ma komai muhalinsa nan yayi magariba da isha,i sai wajajen tara ina daki kwance ina waya ya shigo dakin nawa. Kamshin da yakeyi yasa na dago kai duk da nasaba ganin hakan amma na danji ba dadi a raina kishi kumallon mata watau kishin nan akwai ga ko wata mace saidai ka danne kawai shine mafita. Ni zan tafi ya fada ya tsaya akaina ban dago ba nace Allah ya bamu alheri sai naga yayi tsaye yana kallona. Ganin hakan yasa na dago na kalleshi ni din yake kallo yayi murmushi ya girgiza kanshi yana fadin in fasa zuwa ke nan ko ? Da sauri nace nina isa in samesu da mijinsu ince kada kaje gunsu ai sai ace da gaske nice ke hanaka kulasu din da ake fada. Ok kin yarda ke nan kema ban kulasu ko nace ai haka ake fada don na fada shine na yarda to haka zaki sallemi idan ba fushi kikeyi ba ? Har lokacin fuskana ba annuri nace to wani irin sallama zan maka yaya ok to barin zauna idan kin tuna sai kiyi min in tafi. Ganin yana kokarin kaiwa zaune mannin jikina hakan yasa na dan zabura ina fadin wallahi ba ruwana kada kasa gobe mama tayi muna sammako a gidan nan. Bai kaiga karasawa ba naji ya hade bakin mu waje daya danasa yana tsotso na samu na kwace kaina gareshi yana fadin rowan jikin ki kike min ke nan yau ko ? Banice da jikinka ba shiyasa ban maka rowa ba aika sani haka dai ya gama dan kame kamenshi yana fadin naje na rakashi dole na taso har wajen mota na rakashi nayi mai saida safe ya tafi. Dakin iya na leka ina mata saida safe take fadin Jafarun ya tafi ko nace ehh iya na dan zauna na dan wani lokaci kafin na mike zuwa daki na kwanta.