← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 306

Sashe 104

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da yarinyar nan. Ko kuma har naka auren shima ya samu matsala akan wanan zancen da kukeson jawo min a yanzu ? Saida ya dan gyara zama ya shafo kansa ya sauke wani shu,umin murmushi a fuskanshi kafin habun ya kallo iya yana fadin a dai tsaya gana J shida yasawa kansa son yarinyar nan da karfi da yaji. Don dai Rahama Allah ya gani bata bada son ranta ko ra,ayin yar uwarta aka daura auren nan da Jafar ba tunda baiyi soyayya da ita ko ya nemeta wajen wani ba. Allah ne kadai ya nufa akwai hakan a tsakaninsu shawaran na zuwa mashi muka yanke shawaran daukan kawu muje wajen yan uwansu ko hakan yana yuyuwa sai gashi munyi sa,a muna zuwa har auren aka dauro lokaci guda saboda nisan waje. Asalin zancema wallahi duk kansu har yanzu basu sanda zancen auren nan ba don banji ita maria tayi min magana a kan zance ba kunga ke nan bata sanda labadin auren ba itama ? Ikon Allah abin farin ciki ashe yana zama na tsiya Dubu ? Na dauka wanan zance ke zakifi kowa farin ciki da alfaharin faruwan hakan a cikin mu ai don kece kika san halinda danki yake ciki na bukatan abokiyar zama tagari da zata bashi kulawa da kwanciyar hankali? Amma kaiyya dai abin takaici sai gashi kece tafarko da kike nuna halin uwayen zamani akan danki don kawai ya zabawa kansa farin cikin rayuwansa . Iya ba wai naki zancen nan bane sai duban irin yadda za a fassara wanan zancen a waje yar uwarta fa tana gidan nan tana aure iya yanzu kuma ace shi jafar ya auri kanwarta ? Zargin matansa saiya tabbata tunda dama sunce yana kula yarinyar har a gabansu bai son ranta kona yar uwata ya baci inaga yanzu ace ya aurota ? Dubu ban soki da wanan rayuwan ba a cikin yayanki kada ki manta ke dai ba ayi maki irin haka ba dagani har mahaifinku bamu takurawa rayuwan ku ba a baya. Yanzu ki duba bayanin yaron nan Habu yaran nan basu san da zancen nan ba daga tambaya akai masu halarci aka dauro auren nan ko wanan abin bai isa ki gane Allah dayane ba dubu ? Iya ina son ki tuna Jafaru hakkin yan uwansane a hannunshi yake juyawa suma yaran nan suna da bukata akan dukiyan su . Nina tauyesu na bashi dukiyan nan ya juya yau iya yana ta faman aure aure yaran nan bai aurar da kowa a cikinsu ba banda shi habu su sauran basu bukatan dukiyansune iya ? Kina kallo ko abu zaiyiwa yaran nan daidai dana matansa zai basu hakan fa ina kyaleshine kawai iya amma a gaskiya raina yana sosuwa da hakan wani lokaci. Au tanan kuma zaki fitowa dan naki kice min tun farko bakin ciki dashi kikeyi ko kuma yar kice ta zugaki akan hakan yanzu ? Wanan ma mai saukine ai mama in dai dukiyansu suke so nasan ko yau din nan aka bukata Jafar zaiba kowa kasonshi in sha Allahu iya ta amsawa habu da kwarai kuwa dan nan. Iya rabu da wanan tunda an kashe masa baki a yanzu komai zai fadi game da dan uwan nasa don bakinsu daya akan zancen. Amma gaskiya mama duk wanda ya canza maki ra,ayi akan yaya jafar zai iya cutan mu da dukiyan mu yayi maki mumunan hudu ba arayuwa. Ni sam ban taba wanan zargin akanshi ba mutumin da yake tsaye a kan mu da komai namu gidan nan shine za ace yana facaka da dukiya yanzu ? Rufe min baki salima tun ranki bai baciba wajen nan idan an tashi zance ki hana mutum yai magana don wani ra,ayi naki na daban. Gaskiya take fada maki mama don kuskuren da kike nema ki tabka a yanzu babbane da nan gaba zai dame mu bake bama don duk ranan da Jafar yaji zancen nan ba za asha da dadi ba. Kai dukiyan nan dai ina nina danka masa da hannuna ko nayi shawara dakai da zan bashi don haka ka kyaleni ba zan yarda Allah ya tambayeni kan hakan ba. To shike nan mama a samu lokaci a zauna dashi kan hakan amma ina bukatan ku cireni cikin zancen nan don Allah . Daga hakan ya mike ya fita daga dakin cike da bacin rai part dinsa ya koma cike da tunanen yadda zai tafi yabar yanda a cikin wanan cakwakiyar hakan yasa ya daga tafiyansa a ranan. Zama yayi da matanshi ya fara fada mata abinda ke faruwa tiryan tiryan inda ta kasa fahintar abin don a zatonta yana nufin yaya J yana son ya nemi Rahama da aure yake nufi. Inda ta fara fadin haba dai yaya habu ina hakan zai yuyu don Allah kabar zancen nan kafin ya kai ga zancen har an daura aure don haka Rahama a yanzu tana matsayin zaman matar J ce a gidan nan. Cikin tashin hankali ta fashe da wani irin kuka tana fadin amma bakuyi muna adalci ba yaya habu haba dai Rahama fa ? Rahama za,ace ta auri yaya Jafar don Allah ku daina wanan zancen saboda Allah don ba abu bane da zai yuyu garesu shima ya sani. Duk yadda yaso ta fahinci zancen ta kasa sai kukan tashin hankali da takeyi tana neman layin Rahaman data kasa samun layin. A lokacin wayan na wajen anty na barshi don haka bansan duk wainar da ake toyawa ba a kaina lokacin. Bai san ya akayi ba ya daifi zargin Saarece ta fada har matan J sukaji sai ashar yaji yana tashi muryan Saiba na zunduma zagi daga wajen part din tana kiran su da munafukai. Abinda yake gudu ke nan har ya hanashi tafiya a ranan dama yasan sai hakan ya faru a gidan idan labari yaje garesu duk da mama ta bar gidan a ranan da yarta saare . Sai iyace tayi karfin halin fitowa tana tambayan meke faruwane haka suke daga murya ? Kaji tsohuwar nan zakice baki san makircin da aka kulla bane gidan nan don kawai aga an tozarta mu ? To ai gamu gani idan gidan nan na shiguwa ga Rahama tazo gamu wanan kuma yanzu meye idan ance zarginsu mukeyi a baya ?. Jin yadda take fadawa Iya magana yasa ya bude kofa ya fito ya tsaya yana fadin iya ki koma daga ciki ki zauna. Suje suyi abinda zasu iya anyi aure da Rahama in ma baki sani bane ki sani an daura aure a shekaran jiyan nan kuma aure ya tabbata mai zama ta zauna . Wallahi baka isa ba idan ma nufinka kenan dama ka aurawa kanwar matarkashi kayi kuskure yin hakan habu gara tun wuri ku rufawa kanku asiri kawai zaifi sauki. Koki rufawa kanki asiriba a yanzu mijin dake da cuta kike gudun ya kamaki Nusaiba don yanzu ya samu wace bata gudunsa kome ke gareshi har zaki tsaya kina kumfar baki akansa yanzu. Sai hakkuri don aikin gama ya gama faruwa saidai ina son ki sani duk kika sake kika zageni ko matata a cikin zancen nan sai kin kwana a gadon asibiti ranan . Idan kuma kin dauka karyane ko wasa ki gwada ko a yanzu kigani abinda zai faru dake a wajen nan . Yaja wani guntun tsaki tare da jefa mata wani kallo ya juya zuwa ciki baiko tsaya ya fahinci tashin hankalin data shiga ba a lokacin. Don da farko ba aure suke zargi ba kamar nemanta sukaji ance yanayi shine ta kasa hakkura don ranta daya gama baci a lokacin. Sai gashi zance ya banbanta Habu ya fito yana fadin wani magana na daban da bata taba tunanen faruwan hakan ba wai jafar ne yayi aure ? Auren ma auren yarinyar data gama sanin sirinsu gaba da bayansu waiko da gaske habu ke wanan zance ko kunuwantane basuji meyace kan zancen ba ? Ta juya a fusace zuwa cikin part dinsu hankali tashe Asmau dake tsaye tana mata magana akan su tsaya su bincika gyale ta dauko da waya ta nufi hanyar fita daga part din. Wai ina zaki don Allah nusaiba ki natsu mana abi komai a sannu habu yana iya fada maki hakan don ranki ya baci kawai tunda ba shiri tsakanin mu dashi. Ko juyowa ta kalli Asmaun dake magana batayi ba ta fice gidan kai tsaye ta hau abin hawa sai tudun wanda family house ta samu mama da abin duniya ya isa lokacin. Da kyat ta daure suka gaisa da wasu daga gidan ta fada dakin mama Saare ce a waje tana wanke kwanaku tana ganinta ta mike tana fadin daga ina haka saiba ? Mama na ciki ta iya fada tana nan Saare din ta fada ta fada dakin ba gaisuwa sai kukan data fashewa mama dashi wanda ya jawo hankalin mutanen gidan. Suka nufo part din mama din mama dai tana zaune ta zuba mata ido gashi sai tambaya meya faru akeyi duk sunyi shiru sai Saarece ta iya fadin. Yaya jafar ne yayi aure ya auri Rahama kanwar matar yaya habu lokaci guda suke fadin Rahama dai Rahama aure yaushe hakan ya faru ? Haba yar nan akan wanan kika shigo da kuka haka me yaya zata iya yi akan hakan tunda anriga da an daura aure yanzu meya rage kuma bayan hakkuri inna ke fadin hakan. To ba a aure ita tayi ina mijin kawarta ta aura amma ai ita wacan batayi tashin hankalin nan ba da tayi hakkuri gashi an zauna lafiya . Duk wanda zaizo sai yayi kwatance a kanta da cewa hakkuri akeyi ai itama ai wata ta sama kuma tayi hakkuri haka ta mike bata iya fadan komai ba ta fice kuma direct ta nufi wajen shiga motan zuwa kaduna. Baifi yan mintuna da hakan ba yaya Habu ya dora yadda akai daurin auren a rugga ya rubuta Jafar and Rahama Allah ya bada zaman lafiya abin median nan danan aka san da zancen auren aka fara yadawa masu dorawa suna dorawa a saman wayansu. Ganin hakan Jafar ya kira habu yake tambaya yake cewa dashi yanzu kan ai kowa ya gama sanin abinda ke nan ya kwashe komai ya fada mai saidai ya boye mashi zancen da mama tayi game dashi don gudun
Chapter 104 · 0% Book details