Sashe 73
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
dayana garin ba sai ganinsa da nayi a lokacin. Sai bayan kwana biyune Nafisa ke mun hira da nasha zagi a wajensu ranan ganina da wanan lace din da sukayi har photona aka dauka ban sani ba ana tambayan kudin lace din aka fada masu yakai dubu dari. Tace hankalinsu ya tashi sosai da jin kudin ga kuma wayan hannuna shima sunyi zance akansa wai dole zasusa a canza masu waya ba zasu yarda in rike wayan da basu rike basu. Har cewa sukayi kila sata nayowa inda naje abuja din yanzu an hada plain din cewa za a turo saratu ta kwashi number anty salma a wayata su binciketa sai sunyi min sanadin da suka gujeni a can din. A wanan lokacin anty maria tasan irin kwaran din da nake fama dashi a gidan a wajen hiran mu da Nafisa din dole na kwashe komai na fada mata abubuwan da suka faru dani tana asibiti. Ance Dan Uwa Murfin Jallo guda bayayi saida dayan don duk wanda baida dan uwa a duniyan nan yayi babban hasara a duniya. Ran yar uwata ya baci sosai har tana ikirarin dole ya habu ya canza mata gida kada suzo su illanta muna rayuwan mu. Ita kyauta daga gurin yaya J ta daina amsa koda na dantane kuwa indai shine yabada da sauri Nafisa tace kada kiyi haka Maria. Inkinyi hakan nice zasu zarga dana fada tunda sunsan tare nake da Ramaah ko yaushe dama kuma suna zargina gashi ba uwa daya nake da mazansu ba sai ace nazo don in shiga tsakaninkune ashe . Wanan yasa ta hakkura da zancen saidai itama ta dauki zafi a nata bangaren yanzu ba sakin fuska ko wani ban girma ga matan dan uwan mijin nata kuma. Zama dai ya rike a gidan inda har yakai mama dubu tazo don jin ba,asi inda ta tarasu tana tambayan me yai zafi hakane a tsakaninsu ? Bata fahinci komai a zancen ta daiyi masu fada ta kwana biyu ta koma akacigaba a inda aka tsaya muna sha,anin mu suna nasu saidai mama din ta dauki anty Saare da Nafisa ta tafi dasu inda tace salima zata dawo hutu ta zauna da iya kafin gani kuma tare da iyan. Sai zaman gidan a lokacin ya soma fita min rai don ba abokan hira a gidan yanzu da zaran na dawo ina dakin iya ko wajen yar uwata ba zan fito ba kuma sai washegari. Allah ya taimakeni iya da kanta ta bugawa mama waya da Nafisa ta dawo mata idan ban nan zama ita kadai yana gunduranta. Hakan yasa nafisa ta dawo ita kadai amma ta kiyayyi duk wani abinda zai kaita part din yaya j a yanzu har na yar uwar tawa bata shiga ko ina a gidan. Har yakai mazajensu sun fahinci akwai abinda ya faru iya yaya j yake tambaya itace take fada mashi dan abinda ta sani ga zaman matan nasu. Ranshi ya baci sosai ga abinda iyan ta fada don tace hassadane kawai da kyashin juna ya kawo masu gaba a tsakaninsu. Rasa abinda zasuce sukayiwa iyan kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyansa tsakaninsu dai komai lafiya yake tafiya koda akwai baraka basu yarda ko mahaifiyarsu ta sanda hakan amma ga iyalinsu nason kawo masu matsala kuma a hadin kan nasu. Saidai mama bata yarda da hakan ya faru ba a yanzu kan ta daura dammara wanan zuwan da zatayiwa iya data dameta ta kwana biyu bata zo ba zasu ga canj a wajan ta baki dayansu duk wace ta kuskura tayi wani abinda ba daidai ba a gidan. Basu kadai ba har saare ta shiga wanan fadan na mama a yanzu don gaba daya ta hanata shiga ko wani part a gidan. Saidai hakan bai hanasu hurdansu ba a boye tunda gulmane akwai waya a tsakaninsu sun dai kaucewa idon ita mama dubu din ne. A yanzu ko yaya Habu yana gari a nan wajensu nake kwana don na dawo da rayuwana gun yar uwata baki dai shigowa part din mu kiga wani abin kazanta a garemu ko wani abinda bai dace ba can. Yayin da arzikin mazajen nasu keta bunkasa sosai wai ashe ita anty saare ta samu matsala a karatun ta wanda yasa ta bar makarantar da takeyi a farko na gane hakan ne wajen jin ta koma da karatunta a nan F C E zaria. Saidai a hostel zata zauna tace kuma suka yarda amma tasha fada sosai wajen yan uwan nata don har shi J yana ikirarin idan bata tsaya tayi karatu ba wana katon ba zai sake bata kudinsa akanta ba. Kwatsam zancen auren ummah ya taso hakan yasa mu zuwa garinmu da tun zuwan mu bamu taba marmarin komawa ba. Munje kafin bukin inda yaya Habune ya kaimu da kanshi zamu dawo mu taresu a nan kamar yadda naji suna fada ba zance nayi farin ciki ko bakin ciki ba nidai na kasa tsayar da zance daya a zuciyata akan auren. Gaba dayan mu bamu so zuwa wajen baffa ba amma aka rinjayemu muka tafi dole ganin sa munyi arziki ya tafi Adamawan cameroon a lokacin hakan yasa bamu samu ganin shiba saidai mutumina kan Dage manga juna dashi har na karbi lamban wayanshi rakani toilet dayake shan kida dashi. Ban yarda na bar garin ba saida ya ban kata,un makaru da yayi ikirari dashi yace idan naje na juye a kyale kar na barshi a leda. Kudi na dauko na mika mai tare da gargadinshi akan kada kowa yasan hakan don na kara masa gobe nasan matsalan dan uwana wajen kwadayi. Jin dadin hakan yasa yace kai amma Ramatu kin kasheni yau to jo kiji wani magana na matsa ya soma magana kamar a cikin rada zakice yana tsoron wani yajimu duk da matarshi saida ya turata cikin gida ta samo leda ya san min dankali. Wanan daman muka samu ya fada min wasu sirika da zamu fito na dankawa matarshi itama dubu biyo don nayi mata faein sani dani akai nemanta a lokacin bayab mune akai aurensu. Na kurune da dani aka hadashi amma uwarshi tace sam bata yarda da hakan ba ita don idon mu ya bude da yawa zanwa danta wayau na hanashi aje Nagge. Nikan taimakona tayi a lokacin da irin gulman nasu da camfi na kauye da suka dora muna wanan yasa a kullum baffa ke fadin mugaye muke masu bakin jini a haka zamu kare a kiwo. Ni nasan Allah yana sonmu shine ya kawo sanadin da bamu hadu da baffan mu ba lokacin don da yaga yadda muka koma komai na iya faru a lokacin don baffa mugun bafulatanine sosai shiyasa mutane ke masa lakani da maita. Mun dawo lafiya baki alaikum da kamar ba zamu samu taro wajen yan gidan mu ba kome suka gani oho masu saiga Asmau itace ta fara shigowa yi muna sannu da zuwa. Daga baya Saiba tashigo a yatsene take muna sannu da dawowa ya hanya muka amsa mata da lafiya kalau. Acan gida mun shiryawa ummah sosai gaskiya yaya Habu yayi kokari ba kadan ba tunda ba wani sana,a yar uwata takeyi ba. Bayan dawowan mu da sati biyune ummah muta tare a gidan sabon mijinta dake kaduna a unguwar Dosa mama dubu dasu inna sukai mata rakiya a cewansu sunyi mamaki kwarai ashe mutumin ba karamin mutum bane . Ita matarshi data rasu ta barshi da yara biyar tsohuwar lauyace mai zaman kanta haka yayan nasa ma duk karatu sukeyi basu zama a gida. Nikan sai najiwa ummah tsoron hakan don yan bin nan ba ai masu shigen kutse haka duba ga yadda mu nan muke fama da facalan yar uwata a wajen kishi.