← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 279 OF 306

Sashe 279

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba cewan da akayi kauyen sokoto za akaita bane abin mamaki sai irin gidan da mota ya tsaya dasu a garin tambuwal. Daga wajen gidan kawai zaka fahinci inda sukazo gidane na gandu irin gidan yawa din nan mai dauke da tun kaka har jikoki a cikinsa in akwai. Haka aka fito da ita zuwa cikin gidan wanda ko gidan gadonsu dasu mama ke zaune a cikinsa yafi don a can family house dinsu shimfide yake da siminti lungu da sako na gidan ga baki daya har bayi a shimfide yake da siminti. Sun samu dakin nata saboda kayanta tsohuwan gidan ta tashi daga dakinta an gyara dakin an hade mata shi da nata ya koma ciki da falo mai kama da babba da jakka dakin nan da tsawo can ta kuryan uwar dakan da akaiwa kwaskwarima yana kasa. Maman tudu dake rike da ita tun tana fadi a ciki har zancen ya fito fili tana fadin ikon Allah aure shiya gaji haka yau Saratu Allah ya nufa aure ya kawota nan kasan kuma ina ji sunan garin nan a redio amma ban taba tunanen zuwanshi ba. Sai faman gaidasu da zuwa yan gidan keyi har suka kai dakin nata suka zauna kallon juna kawai suke a tsakaninsu sai yaya barakhace ta iya fadin . Shiko dai wanan mutumin a gidan yawa haka gidan kowa da kowa zai kawo saratu ina laifin ya kama mata haya a wajen gidan don Allah dai. Ke dai bari ai wanan dalilin yasa muka koma muka fadawa Dubu abinda idon mu ya ganan muna ai baki san abin takaici bama barakha ni hada ban dakin nan shine ya tayar min da hankali fiye da komai. Ga matansa kauyawa gidadawa dasu ke bari kawai abin bai faduwa dai wallahi daki ai kun samu an gyara komai dafa ciki gudane iya falon nan. Gaskiya mutumin nan bai kyauta ba wallahi haba dai a,a barakha idan baku sawa auren nan albarka kuyi shiru don Allah tana fa son abinta ita don haka ku daina wanan magana. Idan matansa kauyawane ita yar birni saita koya masu komai a sannu harsu gane ai dama shine amfanin surka auren da maza keyi yanzu. Nusaiba ce ta fito daga kuryan da suke tana fadin nikan zafi kamar zan suke wallahi dakin nan idan na kwana a cikinsa haka ai ina sankarewa kafin safe ? Meyasa wa yanda ke gidan basu sankare ba sai ke ku dai iya bakin ku a rabu lafiya don Allah irin maganganun nan babu dadi gaskiya. Mama tudu ta tarewa Nusaiban numfashi abinda take fada a lokacin yasa taja bakinta tayi shiru ta tafi tana guna guni nan mata suka fara shigo masu da kulan abinci dama a gajiye suke don nisan tafiyan da sukayo. Wasu sallah suka farayi wasu kuma neman abinci irinsu Saiba ke nan tun wajen bude abincin sukai arba da bakin miyan dake cikin katon kula girke a gabansu miyan dai ga abin miya amma gaskiya yana da wuya yakai bakin mutum ko don bakinshi. Inda Allah ya taimakesu kunun daka da aka kawo masu hade da abincin wanda yaji kayan kamshi ga suga zaikai mudu biyu da robobin sha shi suka dinga afkawa cikinsu don yunwa abinci kan abin miya suka tsame sukaci. Akwai gaji don haka suka fara shirin barci tun a can amarya saratu ta fada masu idan anzo za ayi dinner don haka kawarta da akazo da ita take tambaya zancen dinner din ? Take fadin itama har yanzu angon bai kirata ba kota kira wayanshi yana kashe bata samunshi har barci ya dauketa ba zancen dinner din. Washegari hayaniyar mutanen gidan ya tayar dasu wajen kewayawama fitina ne haka suke bin lafiya har amaryan suka dai samu sukai alwala sukai sallah. Su mama suna falo suna dan gaisawa a daidai lokacin sukaji amarya ta fasa kuka daga kuryan daki hankali tashe suka isa gareta banda mama tana zaune tana azzakar din ta na safe. Sai dai ta jefa masu baki daga inda suke saida ta idar ta mike ta samesu tana fadin shifa aure mukaddarine duk inda Allah ya nufa zakayi aure saika taka wajen. Abu guda ya rage maki a yanzu shine hakkuri wata nacen tana neman hakan bata samu ba ke kuma gaki kina son butulcewa Allah yanzu da baiwan da yayi maki. Kinsan alheri dake cikin aurenki da bawan Allah nan da Allah ya hadaku tare shine mijinki aure ba kyalkyalin duniya akajawa cikinsa ba zama na amana matukar akwai so a tsakanin ka miji. Ki bar komai ga Allah kisa hakan shine alherinki a yanzu kinsan tanadin da yake maki ai yasan gidan daya dauko ki da inda ya daukoki don haka halinki yanzu shine jarinki saratu ki natsu kibar wanan shirmen da kikeyi. Kowa nan da kalan zabin da Allah yai mashi duk abinda kika gani ya faru da bawa rubuttace tun asali gareka. Ni banga wani abin damuwa ko shiga tashin hankali ba saratu kinafa son mijinki so ba inda baikai mace a duniyan nan . Da kalaman mama ta samu natsuwa suma din su saiba dake sakin magana duk mama tayiwa kowa gugan zana a wajen kowa ya kama bakinsa. Don cewa da mama tayi da wani zaman burni ko cikin daula ai gara kauye din inda hankalinka yake kwance a san kana kauyene ba sunan kana cikin daula ba wanan zance ya tabawa Saiba rai inda tace da ita mama keyi a zuciyarta. Kamar ana koransu kafin takwasa na safe duk sun shirya tafiyan komawa zaria a gagauce ga matan gidan duk da safiyane sai dake dake sukeyi suna wakokinsu a cikin raha na nuna murnan auren daya daga cikin ahalin gidan ana fadin su jira a gama furan barna sukace akwai nisa tsakanin zaria da nan gara subi hanya da wuri. Sai wajen shiga mota suka samu ganin ango yazo sallamansu nan mama tayi mai dan nasiha yana ta godiya suka tafi suka barta a nan din cikin mutanen da bata taba sanin kalan rayuwansu ba haka ya mace ta gada dama a kaika inda baka zata ba a rayuwa Allah yasa mu dace amin. Ranan yan uwan Aminu mata da yaya barakha tazo dasu wajen bukin suka zo gidan mu dama ranan zai koma can gidanshi ya gama kwanakinsa a nan. Abinci lafiyayye na shirya masu ba wani daure fuska koma ba sakewa sosai kada raini ya biyo baya na barsu sunyi yadda suke so tunda gidan kanin uwarsune suma kuma basu wuce gona da iri ba yadda nayi zato. A can gida kuma mama hankalinta a tashe yake har saida yan kai amarya suka iso a wahale kowa na neman abinda zaici a cikinsa maman tudu bata tsaya ba ta wuce gida da ita da yaya Rukaiyya. Sai mama hafsatu da yaya barakha da Saiba data nufi part dinsu suka rage a gidan yadda suke neman abinda zasucine ya tayarwa mama da hankalinta sai dai batayi magana koma meye ai zataji su kuma basu cewa kowa komai ba kar yadda maman tudu ta kwabe bakinsu tun can din. A nan gida kan wajen mama ba wanda yai magana sun daici abinci sun kuma ce sun barta lafiya tana can sun barota ita kadai. kamar yadda ake barin ko wata diya idan an kaita gidan miji nan mama tayi shiru na dan lokaci ai kuwa can part din yaya jafar kuma gajiya bai hanasu fada ba. Don saiba na shigowa ta kula da kayan da yaci abincin rana ta soma fadin halan gidan nan sweet J ya kwana ? Asmau tace ehh cikin ko in kula daki ta nufa har ta tube tufafin jikinta kamar an tsikarota sai gata ta fito tana fadin . Asmau ya kwana a nan kuma kinsan nice da girki kika yarda ya kwana a nan ban gari ke dai yar cin amanace ta gaske wallahi ? Cikin mamaki Asmau ta dago tana fadin tau fa kaji manya don baki gari sai kada ya kwana a nan ko ai bansan haka kika kafa doka a gidan nan ba ? Aida zaki tafi saiki fada min kada na kuskura in karbeshi idan ya dawo tunda kinsan jiyan zai dawo gidan nan kuma kikayi tafiya ? Fada sosai sukayi tsakaninsu wanan kawai ya isa ya tuna maka saratu don da tana gidan da tun a lokacin ta iso part din ko kuma ta bugawa saiba din waya tun tana can ta fada mata abinda ke faruwa a gidan. Har suka gaji suka kyale juna akan a bari maigidan ya dawo tunda shine munafukin da yayi hakan saiban ta shiga tayi wanka ta fito don tunda sukaje sun kasa yin wanka a bayin gidan. Abincima da Asmau ta bata kin karba tayi tabar matashi a falo ta fito zuwa part din mama ta duba ko akwai abinci a can taci . Ta samu don mama tayi girki don isowansu din ta zauna taci tana cicika a lokacin mama ke fadin mutumiyar ki dai tana can ta zama mutanen sokoto ? Mama aida sokoto din take da sauki wani shegen gidan yawa ya kaita fa gina kamar na mutanen dauri abinda babu dadin fada gaskiya. Kai Nusaiba bakiji me maman tudu ta fada ba albarkan aure yafi riyan dake cikinsa kayi abu daidai karfinka ba karya yafi kayi karya girman ka ya zube. Meye laifin gidan tunda yana da gidansu aurene fa ba inda bakai diya mace ta mike tana fadin yaya ai gaskiya na fada . Ita mama da take fadin hakan ai ta fadane kawai tunda bata yarda akai yarta wanan wajen gaskiya kam abu daine bai faduwa kawai sai ayi shiru hafsatu ta fada daga gefe. Wai ku tsaya me ake kokarin boye min ne mama din ta fada tana duban saiba din ta mike tana fadin mama ni me zance yanzu ace kuma ina kushe aure sunana yakai tasa kai ta fita. Munafuka dadai ki fada din mana tunda gulma na ciki ai gara dashi yana da gidan ke ko gida iyayyenki nada shine balle nina dawo rakiyan yarinyar nan na kula ba mutumiyar arziki bace ita . Barakha meye laita yanzu har kina kokarin zaginta ai gara da ita ta fada min halinda yata take ciki kuda kuka boye min fa don yaya
Chapter 279 · 0% Book details