← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 306

Sashe 171

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

tace mubar zuwa gidan tunda ko muje bamu samun taron arziki a wajensu. Tun wani zuwa da mukayi da sallah uncle yace a dibar muna nama muda maman mu a gabanmu tace an raba nama ya kare har muka fito bata bamu ba . Habiba daga yau karna kara jin kin tsoma baki cikin irin maganan nan abinda akayi ya wuce ina ruwanki da kawoshi yanzu ki daina bana so don Allah. Shiru falon yayi na dan lokaci sai can iyan ke fadin kinji tarbiyan kwarai haka ake son ya kasance kanayi kana kwabon bakin yaro ko yaushe baka kyale yaro na tsoma baki a zancen manya ba shine matsalan dake damun uwarku. Kada ki kara bayan haka duk uwa tace bata kwaba yaro duk abinda ya fada shine daidai a wajenta to itako da zaman lafiya sunyi ban hannun makafi ke nan. Ki bari gaskiya ta fada maki ko ita da zancen ya shafa inkin kula bata fadan kallal kahu a ciki idan anayi don haka kada ki kara kinji. Iya idan na kyaleta watarana a kaina zatayi kuma ta dauka ai hakan daidaine ban taba zama dake ba habiba ina maki zancen wata a gidan don haka ki daina don Allah hakan ba halin kwarai bane kinji. Bazan karaba anty ko yanzu ma subutan bakine mamanmu ta kwabeni da hakan kullum naje kuma sai tayi min fadan hakan ta fada a dan maraice. Saida mukaci muka sha donshi bai tsaya yaci abin kwarai ba na kwashe kayan tare da biba kafin mu fito iyan ta shiga dakinta na leka ina fadin har zata kwanta ke nan ? Tace meya rage min kuma yar nan baku barni da komai ba sai godiya ga Allah Allah dai ya tashe mu lafiya kuma ya karawa mai nemowa dake mai dafawa lafiya na amsa da amin na kalli biba ina fadin saura ki kwanta da kayan nan baki sauya ba don har yanzu kina da matsalan haka biba kije ki watsa ruwa kiji dadin kwanciya don Allah. Akwance na sameshi yayi shiru jin motsina ya kalloni na karaso ina fadin a hadoma ruwan shayine naga bakaci komai ba kai ? Naci abinci da habu a wajenshi ya dawo da yamman nan anfito da abinci ya matsa sai naci shiyasa banjin yunwa. Ashe ya dawo ke nan yace ya dawo dazun ashe maria din bata jin dadin jikinta shine ya dawo da sauri nace bata fada min ba kuma munyi waya da yamman nan tana fada min zancen haihuwan yar mijin ummah a kaduna. Ta boye makine gobe sai ki shiga ki dubata idan zaki dawo school amma taji sauki don naga tana aiki da kanta ai.
Chapter 171 · 0% Book details