Sashe 198
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk saurina ban manta da zancen maganin dana hada na ruwan dokin da Dange yayi min bayani ba a kwanaki bamu samu amfani dashi ba yayi wanan tafiyan daya dawo a cikin rashin lafiya. Rashin lafiyan daya zamowa kowa a cikin family na tashin hankali don ga mutum kwance sharkaf baida wani moriya ba umm,uuumm asalima baisan a hanlin da yake ciki ba na tsawon kwanaki. Za a iyacewa dai kamar ya shiga common ne ko kuma jinnu sun shafeshi kamar yadda hausawa kefada in mutum yashiga irin wanan halin da ba asan kansa ba. A iya binciken asibiti sunce su basuga wani abinda ke damunsa ba saidai suna hasashen ko kwakwalwansane ya tabu ko kuma ya bugu a kai hakan ya sameshi. Bayan hakan su basuga komai a tare dashi ba bayanin da sukaiwasu yaya Habu ke nan a karshe irin hakan wai amma zasu ajeshi acigaba da bincke ko za a gano inda matsalan yake. Jin hakan yasa hankula ya kara tashi sosai ga yan uwa kowa ya saduda a yanzu don irin hakan yana da wuya ace mutum ya mike sai yawancin rai da rabon mikewa din. Kowa kika gani fuska ba annuri don labari ya karade kowa ga abinda likitoci sukace game dashi din sai koke koke ke tashi tsakaninsu. A cikin irin hakan ne na karaso asibitin tunda na tunkaro naga yanayin fuskokinsu sai jikina yayi sanyi na rasa wanda zan tambaya meya faru dakin na nufa da sauri a zatona ko ya cikane na gansu a hakan . A yadda na barshi haka nayi arba dashi kwance shambal saman gadon ba motsi na gaidasu a tsatsaye na karasa bakin gadon ina kallon numfashinsa dake sauka wani iri. Muryan mama tudun wadace naji a gefena tana fadin yana nan ai a raye saidai lamarin nasame keta kata muni kamar dai wanan ciwon bana asibiti bane. Bana asibiti bane mama na fada ina juyawa wajenta rabin da take na sake gaida ita da wuni nakai tsugune cikin girmamawa muka gaisa na aje jakata a gefe daya inda nata yake . Ta cigaba da fadin ni lamarin nan yana ban tsoro dazun don yadda gaba daya yanayin jinyar tasa ya canza a yanzu yana sauyi da kamar iska ko hannu a lamarin. Binshi nayi da kallo a yanayin da yaken tacigaba da fadin ni a ganina kawai abar asibitin nan a koma gida dashi zaifi idan an koma sai a surka ayina gatgajiya dana asibitin. Abu daine da baka da iko a kansa da ina da ikon da zan fada aji dana bayar da shawara a kwasheshi zuwa gida ayi na gargaji yafi zaman asibitin nan da akeyi a cikin duhun kai. Ni tunda naga sun kwashi jiki sunyi tafiyan nan shekaran jiya nasan akwai inda suka tafi game da lamarin jikin nan nasa amma kin san ba fada muna kome ke akwai cokon lamarin zasuyi ba nidai abinda nagani kawai su kwasheshi a koma gida aje ayi na gargajiya zaifi wanan zaman da akeyi nan. Mikewa nayi daga inda nake tsugunne a kusa da mama din zuwa bakin gadon ina kare mashi kallo zakice ba Jafar din nan bane da kikeson karawa kallo duk ya fita hayacinshi. Ga kamsuba da suka fito mai a fuska yayi wani baki sai dogon hancinsa kawai zaki hango zaram bandashi ba wani abu daya rage a cikin jikinshi. Abin dai dana saba nayi mai addua donshi duk wani mosoyinsa zai mai a lokacin donshi yafi bukata garemu. Yayin da zuciyana yake wani irin halbawa a cikin fargaba da tashin hankali don gaba daya nikan na sallama a raina mun rasa yaya a wanan lokacin don gara wancan ciwon na baya yana a cikin hankalinsa wanan kam baisan wanda yazo ba baisan wanda ya tafi ba. Sai bayan tafiyansu mama dan yanzu dagani sai maman tudun wanda da iya muke kwana su yaya kwana biyu suna gidajensu amma basu barin asibitin sai wajajen karfe daya da wani abu na dare koshi sai iya ta matsa masu akan su tafi zasu wuce din. Iya na daga waje tana sallah bata shigo dakin ba tukun na na dubi mama a cikin karfin hali nace mama naso nayiwa yaya wankan magani a gwada a gani amma ina shakkun hakan da zanyi din. Kwana uku zanyi mai hakan amma sai abinda kikace shiyasa ban fada ba a gaban mutane ta yunkura ta mike zaune tana fadin idan zaki iya ki gwada a gani mana yar nan ai sauki ake nema ba wani abu ba dama kuma zaman hakan muke a nan din. Tana zaune tana kallona na hada komai sai naji ta mike tana fadin bari naje daga waje in tare tsohuwar nan kada ta shigo. Ta fice ta barni dashi a cikin karfin hali hakan kuwa na cude mai jiki da ruwan hadin maganin na kuma bashi ya sha sosai na mayar dashi ya kwanta a nan na kife a jikinsa ina kuka. Sai da mama taji shirun yai yawa ta leko tana fadin yayane har yanzu cikin karfin hali na dago ina fada mata angama. Sun shigo sun tsaya akanshi suna kare mashi kallo tare da fatan alheri a gareshi kafin suka juya suka samu wajen kwanciya don ni ban faye kwanciya ba ina zama a kujeran dake gefen gadon nasa koda yaushe. Tsawon kwana ukku muke a hakan dashi kullum da safe kafin su shigo zan shafa mai na bashi yasha bayan na gama mulke masa jiki ko ina da wann ruwan da doki yasha ya raga don ba karamin magani da alfanu yakewa mutum a jikinsa ba. Kamar yadda dage ya tabbatar min ni kuma na fadawasu mama da iya ance ka,idan maganin har in akwai alaman sauki kwana ukune kacal za ayi amfani dashi ga mutum aga alfanun maganin. Don mutum zai fara nuna wasu alamomi na jin sauki ko wani sauyi nadaga ciwon halin da kake ciki din Allah da ikonsa kuwa ranan na gama mashi amfani dashi na bashi yasha na zauna ina rufe goran nakai idona akanshi sai na ganshi ya kura min ido kuri yana kallona. Da sauri na cusa magani a cikin jakata na karasa wajensa ina kiran sunansa saidai bai amsa ba illa idon daya kafa min din baya kyaftawa hakan yaban tsoro na nufi su mama ina kiransu hankali tashe. Suka shigo dakin gurinsa suka nufo cikin kidimewa suna mai sallati da kabbaran iya ta karasa tana fadin Jafaru idon kane nan ? Sai ya dan lumshe idanuwan nasa kamar ya sauke ajiyan zuciya ya mayar ya rufe can kuma ya kara budewa yana kallon mama dake mashi sannu a lokacin. Ya Allah yadda ka nuna muna hakan ka tayar muna da kafadan yaron nan a cikin mu cikin salama da kudirinka ya dawo muna a hayacinsa ya koma walwala kamar kowa. Hawaye kawai ke fita min daga idanuwana na kurasa masa ido a cikin tausayi ni kaina a lokacin abin tausayi nake na sani amma duk bacin ran da bawa zai shiga matukar yana lafiya ya godewa Allah don na kwance ya fishi shiga tashin hankali. Ganin yadda ya kura min idanuwanshi din yasa iya min magana tana fadin ki daina wanan kukan ki karasa kusa dashi kiji ko wani abin yake so don ke yake kallo a yanzu din. Hakan na dan karasa gabanshi na dan rankwafa ina fadin yaya kana son wani abune da idon daya kifta min na gane yana nufin a,a sai ya maida idonsa ya rufe a hankali. Ya Allah kasa hakan saukine a gareka jafar Allah ya kaddara tashin ka a cikin yanayin nan ya baka ikon cin jarabawan nan da Allah ya aiko maka muka amsawa mama dake fadan hakan da amin. Munyi tsaye cirko cirko a kansa sai iyace take fadin ko abinci yake bukatane ni dai banyi magana ba don nasan yana da wuya idan hakanne. Saidai na karasa gaf da fuskanshi ina fadin a hado maka ruwan shayine zaka sha yaya sai naji iya tace keko dai ai basai kin tambayesa ba a dai hada mashi din a ga ko zai sha din. Shayi mai kauri na hada mashi don ya kama mashi cikin nasa na mikawa mama na kamoshi tare da ita muka bashi shayin. Alhamdullahi don yasha sosai ya maida idon sa ya rufe kuma alaman ya isheshi ba zai kara ba a haka mazan suka shigo suka same mu dashi ina zaune rike dashi na dan dagashi ya fada mai. Sunyi farin ciki da halin da suka sameshi sai mama ke fadin dama yar nan tace insha Allah maganin nan datake mashi kwanan nan ance da yardan Allah a cikin kwanaki uku za aga fa,idanshi gashi ko mun gani. Alama ya nuna wanan matsalan bata asibiti bace ke nan don haka gara in an kara ganin hasken hakan a mayar da yaron nan gida aje acigaba da neman na gargajiya a gani. Ya Auwal yace haka kowa ke fada shima Habu jiyan nan yake fadin ance wani zubin idan an rasa gane kan ciwo kawai mafita abar asibitin da mutum don shedanu da miyagu masu sihiri suna son hakan. A asibiti suke samun galaba don sunsan babu wani maganin tsari ko riga kafin da zai taresu a nan din sun daita maganganu a tsakaninsu har yan uwa suka taru asibitin kowa na murnan cigaban da aka fara gani akansa din. Lokacin tafiyana gida yayi don ganin matansa sun iso don ina kaucewa duk wani abinda zai iya kawo muna fitina a tsakanin mu a lokacin tun bayan rabon duty da mama tayi muna a kansa din. A haka kuma na kan dan samu daman leka school cikin damuwa da farga ban dai fahintar komai a hakan bayan attendees din da nake dauka kada karatun nawa ya samu cikasa da yawa a lokacin gashi zamu fara final exam din mu next week. Abu ya taru yai min yawa a kai ga zuwa asibiti ga karatu duk nabi na fige hankalina ba a kwance ba umma tazo kusan sau uku tana dubashi. Hakama mutanen abuja sunzo dubashi din don a gaskiya zance a yanzu akwai sauki sosai saidai na fahinci kamar hankalinsa ya dan gushe masa kuma bai magana bayan bude idon da yakeyi din . Gashi kusan satinsa hudu ke