Sashe 88
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasamu na gama exam dina haka na dukulo na dawo gida da ciwon kai ga yunwa da nake tunanen shiya haddasa min ciwon kan don ban iya cin komai idan na taka school sai idan na dawo gida. A haraban gidan na gansu zaune yadda suka sabayi wani lokaci idan sun bushi iska hakan zasu fito nan farfajiyan gidan su zauna a dasa daban hira da tsokona. Irin wanan zaman na fahinci da gaiya sukeyinsa wani lokaci idan suna da kudirin cin mutunci ga wani a gidan suke wanan zaman. Shigowana yayi daidai da karan budan get din gidan mota ta shigo hakan baisa na juya inga mai shigowa gidan ba a lokacin saida akai horn na gane ya J ne ashe ya fita ya dawo a lokacin. Daidai inda ya sameni kiris ya rage inkai lungun mu ya dakata da mota ya sauke glass sunana da naji ya ambata yasa na dakata na juyo ina gaidashi. Ko ban kalla ba nasan idonsu yana kan mu a lokacin shiko gaisuwan tawama bai amsa taba sai cewa da yakeyi dani wai Rahama meye matsalan da kike gudana a yanzu. Murmushi na dan sauke ina fadin yaya gudunka kuma wallahi exam muka fara sai yau din nan muka karasa wanan yasa ka daina ganina. Ya maki kyau shiga zanyi maganin ki ai daga ke har Nafisa zan zauna daku ku fada min idan kuji wani abu daga garemu ne kuke wanan halin sam banji dadim matakin da kuka dauka ba wallahi. Nagode yaya na fada ina dan rusunanwa na hau step ina murda kofan mu na shiga ban san ya akayi ba dai bayan sallah isha,i saiga Nafisa a part din mu tana fada min wai yaya J yana neman mu wurinshi. Yadda nake dagani sai wata dogowar riga mai v neck mara hannu sky colour hijjab dina fari danayi sallah na fito daga part din mu nake ce mata dama dazun yace zai zauna damu ashe da gaskene. Ok dama dazun din da gaske ya tsaya dakene rikici sukeyi da matanshi akan hakan nidai naji yashigo yana fadawa mama a hasale har ya tashi dukan Saare iya ta hana. Shi yaya har yaji sauki duka haka ke nan iya abinda na iya fada ke nan don ni zargin nasu ban daukeshi da wata manufa ba tunda a gabansu dai na tsaya dashi din suna gani. Kuma meye a ciki don ya tsayar dani na tsaya shine kuma zai zamo abin fitina har da zancen duka a ciki ? Kin gane Rahama wallahi yau ina ganin za ayita ta kare a gidan nan kila na bar gidan nan a yau din nan don ba zan lamuci zancen banza ba bari dai muje din muji kiran zakisha mamakina wallahi. Rashin mutunci da iskanci nida na taso gidan yawa kowa da halinsa ana nuna min iskanci in kyale saidai idan naso hakan shiru shiru aiba tsoro bane dama. Ke kenan Anty Nafisa nikan ai kila barin gidan zasuce nayi tunda zargi ya fara shiga haka ko basuce in bar gidan ba aini zan bar masu. Akan me gidansune bari dai muje muji ai mama da kowa suna can wajen hakan ne kuwa koda muka shigo da sallaman mu falon duk suna zaune harshi dake waya a lokacin inda na fahinci zai koma bakin aikinshi a kwanan nan yadda yake fadi a waya lokacin. A jam,i nayi masu ina wuni muka samu waje muka zauna a gefensu falon yayi shiru bin ko ina nakeyi da kallo har kasan da nake ganin tun dawowansu bai samu mopping ba kayane a ko ina yasha a falon wanda nasan aikin yaransune hakan. Suna da wani hali ko yaro yana barna ba za a tsawata mashi ba haka kuma idan dan wani yayi barna har inke uwa baki kwashe abin ba a nan zai tabbata wajen. Ba karamin wahala mukasha wajen gyara falon nasu ba lokacin har ya koma daidai yadda yake son gani kullum a rayuwansa. Muryanshi ya dawo dani na dago kai da yake fadin Nafisa kin dai gani ba falon da kukasha gyara shine ya koma haka saboda na tara jakkai da basu san arziki ba sai tsiya da bakin kishin banza a rayuwansu. Haba dai daina fadan hakan jafar ke Rahama dazun kun fitane tare da yayan ku da yamma ko shi ya daukoki daga bokon da kikaje ? Kallon ido da ido nayiwa mama din cikin mamaki ina fadin wani yaya ciki mama ni kadai nake zuwa in dawo yauma aida Aisha muka dawo ita ta bani lift a motan gidansu da akaje dauko ta. Ina kikaga yayan ku nace nan gida zan shiga part din mu yadda Saiba ta gyara zama irin bata yarda din nan ba yasa na yi shiru. Ya taba daukan ki ko yakai ki wani wajene bayan haka dakata mama ina da number Aisha din bata gidan Alh wada din nan ba sai ta kira layin Aisha din. Wai ke dama kina nan yau ai nake ji wajen kanwarku din nan dazun na ganta a hanya tana jiran mota na rage mata hanya kinsan yarinyar bata da sakin fuska. Aita fada min dazun din shine na kira inyi maki godiya haba dai akan wanan wallahi salima baki da kirki ko kadan kizo ga gida ga gida ki kasa shigowa ? Bari zan kiraki anjima don Allah ta fada tana kashe wayan ta kallo kowa dake saurarensu tana fadin kun daiji yanzu ai. Kinji ko mama kinji da kunnen ki wa yan nan jakkan suna son bata wa yarinyan nan suna a banza to bari kuji wallahi. Jafar dakata iya ta fada yau koka dauki Rahama a motanka laifine hakan nace laifine a garinku ? Wai meyasa samun waje yake son zama iskanci bari kuji in fada maku Jafaru dai namijine mata hudu Allah ya halasta mashi yi akansa. Ashe kuwa matukar hakan Allah ya yarde masa ku din nan baku isa kuce sai yadda kukeso zaiyi ba a rayuwansa . Ba a kallon mata ke Nusaiba kika kutso cikin rayuwansu da danyen aurensu kika saka saida ya auroki gidan nan aka kawoki don bakin ciki kada abuyarki taci bakici ba. Dariya anty salima keyi nasan hakan ya bata haushi ta soma magana tana fadin ai gashinan iya ki tambayeshi idan nina kutso kaina bashi yace yana sona ba ? Ke rufa min baki har yaushe na taba ganinki nace ina sonki Nusaiba bayan wasikun batanci da kike rubuto min kina bata kawarki wajena ? Har kikayi nasaran hada baki da abokina kuka,,,,,, Jin irin tonon asirin da yake mata a gaban kowa yasa tayi saurin katseshi da fada tana fadin bayan duk bina da kayi a yanzu zakayi min sheri. Ya isa haka don Allah wanan kanku kuke tonawa asiri bayan abinda ya wuce koma meye yanzu ai kun zama daya a tsakaninku don haka ki koyi hakkuri da zaman tare. Kinzo kina zargin mijiki da yarinyar nan yau idan Jafaru yace zai auri yarinyar nan ke kin isa ki hana hakan tunda ke ba,a hanaki ba ? Tun zuwan yarinyar nan da yar uwarta gidan nan kuka dauki kiyayya da hassada kuka dorawa yaran nan don mijinsu yana da dubaiyane aksn dan uwansa da ankai ga yadda kukeso . Ki duba yanzu bai ko sanda shigowan yarinyar nan ba amma kince wai tare sukazo gidan nan da ita ya sauketa a waje. Ni kuma na fada a cikin mamaki kwarai kuwa abinda suka fada ke nan cewa tare muka shigo dake na saukeki a waje saidaga baya na shigo gidan hakan bai mun ba kuma na dakatar dake muna magana. Tace ko a bayansu ina kwance ina jinya abinda mukeyi ke nan dake dama sai Saiba tace ai muma ji mukayi cewa komai itace ke maka ita da Nafisa . Ba ance bane kwarai sukeyi min komai ko yanzu ma a gaban ku su din ne dai zasuyi min kome nake so wace zata zauna ta zauna wace bata iyawa kuma ga hanya nan sai ta tafi. Kaina na sada kasa abinda yar uwata dai take zargi ya tabbata ke nan a kaina yanzu sai muryan saiban naji tana fadin . Ko sunyi fa sai me in zaka iya sweety ka aureta kaga wa hakan zai dama ? A zabure ya harzuko mata yana fadin haka kikace ko tace an fada din inka isa ka aureta mugani ko ba nufinka ba ke nan ? Wanda ya fada muna in bai gani ba zaiyi karyane nan suke ma komai ai wa,,,,, Ke yarinyar nan baki da kunya yanzu ke don Allah bai zuba maki kunya a idonko ba mijin da kika kyamata a gaban mu zaki dawo yanzu kice kina fada a kansa ? Nan fa kuka nuna kuna kyamarsa don ciwon da Allah ya jarabeshi dashi don baki da kunya ko kadan yanzu kin dawo kina fadin wanan zancen banza haka don samun waje. Mikewa nayi duk suka bini da kallo falon ban tsaya jin nauyi kowa ba na fice daga dakin kai tsaye zuwa part din mu na samu maria ta idar da sallah take fadin yanzun nake fadin in biki ai. Sai gaki tun dazun wayan ki keta ringing ba tare danayi magana ba na shige dakin na dauki wayan Sa,id ne ke faman kiran layina saurayin daya lake min saidai a ganina ba a yarda in tsaya dashi ba zasuce yarone don yadda naga sunyiwa anty Salima shiyasa ban damu da kulashi ba. Sai kuma ga kiran anty Salma ya shigo wayan na daga ina mata sallama ya kuma najiki a wani mood ko baki da lafiyane ? Lafiyata lau anty kawai dai sai nayi shiru meya faru ta sake tambayana sai naji kawai in fada mata ko zanji sanyi a raina ko kadan ne. Wallahi anty Salma sha,anin gidan nan ya isheni matan yayan ya habu sun saka min ido suna kokarin bata min suna ga abinda bashi ba. Cool down Ramaah kiyi min bayani yadda zan fahinta nan na kwashe komai na fada mata Maria tana tsaye tana saurarena saida taji anty salma ta soma magana da bataji ta juya ta fita daga dakin. Anty salma ke cewa da zaran kun gama exam dinki ki taho nan kiyi hutunki ki kyalesu can yan