Sashe 282
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina jin irin cakwalin da akeyi cikin dangi game da zancen aure Saratu ban taba furta komai ba game da zancen shi zance a yanzu tafiya yakeyi. Bayan haka alhaki kwikwiyone don bin mutum yakeyi koshi yaya shiyasa na katseshi da irin nuna haushin ta da yakeji yana mata gwai da hakan data fada ciki. Na nuna mai tankar uba yake a gareta duk abinda ya cika da ita a yanzu ya sameshi don shine matsayin babba a bangaren mama yanzu. Ya kance dani haka kike gani Rahama amma su a bangaresu ai yanzu tunda banda komai ai basu ganin hakan kowansu kar nake kallonshi a yanzu. Habu ma yafi kowa ban mamaki yasani sarai nina sakashi a wanan harkan asalima sana,atace ta baya na bar masa amma wai habu nan nace ya cika min kudi nayi wani bussiness ko Allah zai taimaka un daga yaki ban . Nayi mamakin wanan zancen da naji duba ga yadda nasan ya taimaka masu sosai a baya koda yake ba abin mamaki bane idan ance yaya habu yayi irin hakan donshi mutum ne da bai kwantuwa ko kadan. Ko iyalinsa gaskiya din tana da hakkurine ba a jin kansu da ita don da watace yadda yake tauyeta din nan da anjisu tuni wajen irin halin nan. Mutane sukan manta da arziki na Allah ne duk akace mutum mai arzikine daga Allah bana haye irin na zamanin nan ba kabar maishi kawai kada ka jefa hassadanka akanshi. Ire iren halin rayuwan da bawan Allah nan yake fuskanta suna da yawa gana yan uwa a gida don wasu har yanzu basu san da baida hali irun na baya ba gani suke shi maishine akoda yaushe. Ga fitinan iyali a kullym sai anyi ance ya samu ya shiga wani hali balle yanzu da abu biyu zuwa ukku sune a gabanshi na farko zancen haihuwana daya nuna damuwa akai sosai tun anan nasan lalai bada kudi kamar da. Sai zancen jikin iya da shine tsaye a kai yana bata kulawa sai kuma salima dake kula da ita din da mama sai kuma zancen jikinshi da halin rayuwan matsi dake tunkaronshi. Cikin haka dai ranan na tashi da nakuda gashi ba a gidan mu yake ba gashi saboda alkunyan mu ta filani na kasa kiranshi in fada mashi duk da jaddada min da takeyi tunda watana ya kama akan in naji wani abu in buga mashi. Kasa zama dakina nayi na koma wanan dayan dakin da babu kowa ina sintiri ina gudun wani yazo ya ganni aga gazawana. Ya kira waya tun asuba kamar yadda ya saba ban daga ba har rana ya fito gashi hankalinshi yaki kwanci hakan yasa ya fito zuwa gidan namu. Kofa na rufe har lokacin ban bude ba yayi ta nocking saida kyat na iya zuwa na bude kofan kafin ma ya shigo na duka a inda nake don taso min da abin yayi a lokacin sanadin dan tafiyan da nayi din. Salati ya sake yana tambayan meya faru meyasa ban kirashi ba shi haka kawai jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa dani tun dare. Tashi maza muje asibiti ya fada a gigice na dago ido da kyat na dubeshi ina zufa nake fasin zan iya ai ? Zaki iya me kin taba sanin haihuwane common tashi don Allah muje asibiti jin hayaniyarsa yasa Biba dake ta sharan barci fitowa daga daki. Turus taja ta tsaya tana kare muna kallo tace baki da lafiyane anty ya juya wajenta yana fadin ke dauko mata wani zani daki da sauri ko kuma tsaya in kira mama dai tazo. Maman tudu ya kira ya sheda mata ta shirya gamu nan zuwa a dauketa zamu asibiti take fadin a,a yau abin yazo ke nan ubangiji Allah ya raba lafiya ya amsa da amin take fadin ai a shirye take. Saidai ka dauko zannuwa kamar uku da kayan jariri a je dashi ya amsa tare da kashe wayan a cikin sauri yama rude ya dannawa yaya Ai kira kuma. Yake tambayana ina zanga zani din da kayan baby akwaisu kaina na dago da kyar na dubeshi ina gyada masa kai alaman akwai. Ina zamu dauko zanin suna a cikin kasan closter dina don yakai sati dana hada komai don gudun irin girshi haka nayi wanan dabaran gashi yayi amfani yanzu. Da kyat muka kai wajen motanshi a nasa yaso ya daukeni naki hakan dole ya barni na taka zuwa bakin motan muka shiga yake fadawa biba ta kula da gida da kanta. A hanya muka saida ya tsaya saboda wani yunkuri da nayi kamar zan rike mai hannunsa da yake jan motan ban tsanmanin ya taba ganin matarsa tana nakuda urin hakan yasa ya gigice sosai a lokacin duk da dauriyan da nakeyi kuwa. Saidai tunda mama ta shiga motan dole na daure ga duk abinda nake jin din saboda alknyan mu ta fulani ban yarda nayi koda dogon motsi ba sai shine ke dan juyowa yana fadin sannu ya lafa ko saidai in gurgiza mashi kai kawai ban iya magana a lokacin don mama kada taga raunina a cewan mu. Sun karbeni sun duba kiran da likita yayi mai ya kara daga mashi hankalinsa inda likita ke fada dashi kan cewa yasan matanshi nada matsala meyasa basu zuwa awo ? Tana zuwa awo saidai asibitin can na mata take zuwa a dubata likita yace to yallabai gaskiya matarka ba zata iya haihuwa da kanta ba saboda yaro nason fitowa amma ba hanya. Anyi arziki ma da yaron yake da rai har yanzu bai mutu ba don haka dole sai munyi mata aiki an cire abin dake cikin nata. Zufane ya karyo mashi son haka yanzu idan ka shirya sai ka saka hannu ga takardan nan a nemo muna jini da wanan maganin muyi shirin aikin yanzu dole sai aiki za ayi mata a cetosu ita da dan nata. Zufane ya karyowa yaya din lokaci guda yacewa likitan go ahead ya mika hannu aka miko mashi takardan aikin yasa hannu sai kudin magani da sauran abubuwan da zai sayo din na aikin. Lokacin daya kira gida yana sheda masu mama na zaune dasu iya tana jin ance aiki tace jam kukan yaran nan kun daukowa kanku jamgwangwan ace mace bata iya haihuwa sai anyi aiki wanan wani irin masifa suka jajibo haka wai ? Assha dubu asha abin naki har yakaiki ga rashin tausayi akwai macen da son kai zai kaita ga askan likita inba dole ba wata mace ke fatan a fede ta don Allah ? Kema fa uwace dubu kin haifa kuma za a haifar maki ki tuna kina da yayan nan gasu nan maki har yanzu a gaban ki kike irin wanan magana. Keda ya kamata aji furcin alheri na Allah ya tashesu lafiya kike wanan maganan haka nasan ko agaban yaran nan zaki iya fadan hakan cikin rashin damuwa da abinda kika fada. Haba iya ace ga yadda yarta take ita kuma yanzu ace sai anyi aiki wanan idan an samu mai karamin karfi don Allah yaya ke nan za ayi kullum kashin kudi kan mace ? Rufa min baki don Allah mara imani da tausayi kawai Allah yana nuna maki abinki hakan baisa kin saduda kin koma gareshi ba har yanzu ? Da kike aibanrta yaran nan haka yasa mazajen nasu sun tsanesu ko sun rage son da suke masu din ke dai ki kama girman ki tun bai bare ba kin kasa kwasa. Balle yanzu ai mama wayewane ga mata mace taje asibiti ko tana iya haihuwa a fedeta don kada tayi saurin tsufa a idon mijinta balle wanan da nasu yake da dalili salima ta fada. To iya kinji ko nikan nace haba gaskiya dai a yanzu yawan aikin ga mata ya yawanta wanan wani irin zamanine muke cikinsa wai tsufan banza da komai wayau ki sai kinyishi. Ki daiji dashi idan kayane kada ki bari don Allah ki matsa kinji har su gane kina kishi dasu irin haka raini ya shiga. Kishi kuma Iyaa su zan tsaya kishi akan me zan tsaya kishi dasu suna yayana da sauri iyan tace, a,a dubu kowa yasan kina kishi da yaran nan akan yayanki maza waye gwanarki cikin sarankanki kaf ? Babu gaba dayansu kishi kikeyi dasu kowa yasani ko don ba,a iya fada maki a gabanki ? Ta mike tsaye da kyat tana fadin salima tashi ki kaini asibitin don Allah kada mu barsu su kadai a can gashi ance aiki za ayi. Ke iya ina kuma zaki keda ke fama da kanki tashi nace ki kaini ta fada da tsawa bata tsaya kallon mama da mamakin furcinta ya kashe a zaune. Duba min Yazidu idan yana nan ya kaimu in kuma bai nan mu samu motar haya mu tafi salima dai ta mike tasan mai iya hana Iya tafiya asibitin wanan lokacin sai Allah. Dole salima ta mike ta shirya suka fito duk da safiyane matan yaya na waje da yaransu suma kansu don tsamin shiyan basu faye son zama a cikin part din nasu ba wani lokacin. Yanzun ma ruwan wake da Saiba tayi alale shine bata zubar ba part din ya dauki wari su kuma basu gane kome ke wanan wari ba saboda kazanta suka fito daga waje suka zauna. Ganin su iya sun fito yasa Asmau tambayan yau iya fita za ayi ke nan tunda safen nan ta juyo tana fadin asibiti zamu abokiyar zamanki aka kai asibiti haihuwa za ayi mata aiki. Aiki kuma har abin yakai can ne shi sani gaibu aisai Allah yanzu Jafaru ya bugo waya yana sanar damu hakan suna can aaibitin dai tun dazun. Allah ya raba lafiya ya kawo rayayye Asmau ta fada samun waje itama bata iya haihuwan ke nan da kanta ko irin na yar uwarta ? Aikan tunda akace aiki za ayi kema kinsan hakane to shine don munafunci ya fita bai fadawa kowa ko yana tsamanin wani abune ? Wa zai tsaya yin wani sheri a kanta ko yar da zata haifa Nusaiba ke fadan hakan cikin hasala tana fadin shiyasa ake jin mu ni banson harka da munafunci wallahi ? Kila shima baisan aiki za ayi mata ba Asmau ta fada ta juyo tana fadin kamar ya baisan aiki za ayi ba tunda haka ta