← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 306

Sashe 53

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba game da abinda ya faru akaina gidan sun dai tambayeni ba komai konace ba matsalan komai. Na zauna a nan don na nasa irin zaman da zanyi ban bakin ciki da ko banda Saratu da bansan abinda na tsare mata ba a rayuwata ? Don haka nake bakin ciki da in girka taci a raina tunda nima yar adam ne kamar kowa gara in fito masu a mutum don a zauna lafiya. Kwatsam saiga anty salma daga Abuja ta bugo waya tana tambayan Yanda karfin jikinta suka dan taba hira take tambayan ina gida ko tace ina kusa ta mika min wayan . Mun jima muna hira in tambayi wancan in tambayi wanan har take ce min nazo mata sallah mana Abuja nace ba za a barni bane . Tace waye zai hanaki zuwa wajen mu Ramaah ? Nayi shiru take fadin naba Yanda waya sukai magana na daiji tana fadawa salma din zata fadawa mijinta idan yashigo insha Allahu zanzo din . Naji dadin hakan sosai yaushe rabona da Abuja koda Yanda taje da mijinta suka kwana hudu acan da yai wani zuwa basuje dani ba rabona da mutunen arzikin mu nida mahaifiyar mu tun rasuwan mahaifin mu da muka koma rugga da zama. Saida akai Azahar na soma shirin komawa gida na tattara kayan dana kawo mata abincin safe na fito babu abin hawa hakan yasa na soma shawaran takawa don komawa gida. Wani mai mota yazo ya tsaya ban kulashi ba yaja motarshi yayi gaba hakan yasa na soma tafiya da kafa ga kuma kaya niki niki a hannuna dukka biyu. Saida kyat na samu abin hawa nashiga ya kaini gida abin mamaki ashe mai motan nan yana biye dani a baya zan bawa dan mashin kudinsa naji yana fadin malam ta barshi kazo ka karba. Na dago kai na dubeshi shine dai ya tsareni a bakin asibiti na dangwarawa mutumin kudi na shige gida da sauri. Gidan kaca kaca ga ganin idona kaina kawar na karasa na shiga falon da sallamata suna zaune suka amsa min mama ke fadin yar halas yanzun nan nake zance ki fa a raina. Nadawo mama na tsaya rana yayi sanyi na dawo tace aikuwa yau ana kwada rana da zafi a garin nan kayan nakai kitchen na aje kayan dana dawo dasu daga asibiti. Kafin na juya zuwa dakin kwananu suna kwakwance suna barci adakin na tube kayan jikina nashiga bayi na watsa ruwa na fito na samu waje nima na kwanta. Sai barci ban tashi ba sai wajajen la,asar da karan wayan anty Salima ya tayar dani alwala nayo na dawo nayi sallah ina idarwa na fita zuwa part din anty na na gyaro don yaya Habu dake gari baya dawowa gida sai lokacin shan ruwa ko kuma idan wani abin ya dawo dashi. Kodana fito kitchen na samesu da mama din sai fada mama keyi tana fadin aiko wani rai yana son hutu a cikinsa shike nan kun mayar da yarinya yar aikatau din ku kowa ya mike kafa saidai ta girka kuci kuma babu kyautatawa. Hakan da tayi yau yai min daidai wallahi aiko shige yanzu ba awa gorin uban don da uban hanya a zamanin nan balle da gatanta mutuwa yasa kuka ganta nan tare da yar uwanta. Daga faloma iya na kada nata suna kurum nidai ban fito ba sai dana dan jima a daki na fito na samesu wanke wanken kwanonin dana gani suna fara daurayewa mama din na fadin ai in bari suyi meye amfaninsu suna mata dasu ? Saare tayi girkin a ranan don ita salima tace a raba ai idan hakane nidai ina wanke wanken ina jinsu har na gama na koma falo na zauna mirsisi da ido kuwa. Duk da nasan sun fahinceni ko basu bahinta bama nima so nake su fahinceni din zaifi sauki har aka kira sallah lokacin shan ruwa yayi bata karasa aikin ba. Sai faman fada da ita mama keyi karshe ma tunda mukaje sallah ni dai ban fito ba na zauna ina jiran ayi kiran isha,in inyi sallah in kwanta. Tun a wanjen diban kunun tsamiya dana fito yi nasan akwai matsala ranan don kawai shi nake soma sha na diba da kyat na sha rabin wanda na dibo din na mayar da saura kitchen. Na dawo na kwanta ke nan naji muryan su yaya sun shigo shan ruwa shi ya je duk da maganan da akayi anan part din yake shan ruwa har yanzu. Ita Saare din ta zubo masu abinci da kanta suna hira ya Habu ya fara kai cibi a bakinsa ya kasa hade shinkafan. Yayi shiru sai shi jafar dake magana da iya ya diba yakai shima a bakinsa furzowa yayi da sauri yana fadin wayayi wanan girkin mama ? Yana binsu da kallo suma duk kallo suka bishi dashi lokaci guda habu yace na rigaka ji shiru nayi kawai mama ta nuna saare tana fadin gata nan ita tayisa. To me girkin nawa yayi kuma tana turo baki zo nan kici kiji abinda yayi jafar din ya fada a hasale yana fadin shame of you Saratu. Badai wanan abincin aka kai masu asibiti ba ya habu tambaya yana kallon mama din a sanyaye mama ke fadin shine mana nina san tsiyan data kwabawa mutane ke nan ? Ba maggi ba gishiri komai babu a miyan nan fa mama da sauri mama din ta kallota tace na matane kila ban zuba ba. Rufe min baki sakariyan banza kamarki saratu zaki kasa dan wanan girkin da baida yawa ina ga mai yawa ke nan ? Ina wanan yarinyar ne yau da aka bari tayi wanan shirmen a hasale mama din ta juyo tana fadin yarinya kan aiba boyansu bace ko ? Da zata zaman girkawa suna ci kullum yau itama ta hutar da kantane su dandana suji wai shine wanan sakariyar ta kwaba muna abinci haka ? Tsam Habu ya fara mikewa yana fafin zai fita bai tsaya saurareb fadan da mama Dubu take yi ba lokacin da Saare. Yana fita ya tsaya ya hada wani take away da gasassun kaji biyu da drikis ya nufi asibitin dashi don yasan ba zasu taba iya cin wanan kwaban ba na saratu ranan. Hakanne kuwa don koya samesu a zaune sunyi zugun zugun sun gama magana kan abinda ummah zatayi buda baki da sahur sai gashi ya kawo masu wani abinda zasuci din. Da bai kawo ba haka zasu zauna da yunwa don ko ba zasuyi magana ba saboda kawaici irin na fulani da kunya suje tambayab surakansu ya hakan ya faru ? Shima ya J din fita yayi a hasale yana fadin wanan baki da maraba da girkin wa yancan idan zaki zage ki koyi girki ki zage har ace karamar yarinyar nan tafiki iya girki ? A hankali tana gunguni take fadin zaku hadani da yaran da suka bude ido da dafon abinci tunda zaman aikatau sukayi a abuja har suka iya abubuwa haka ?
Chapter 53 · 0% Book details