Sashe 55
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe tara na falka ba wanda ya motsa kowa na kwance yana barcin azumi na kewaya bandaki na fito na kitsa jikina na fito falo. Ashe iya na zaune a falon ita kadai jin motsina yasa iya juyowa gaida ita na fara yi kafin na juya zuwa kitchen don in hada kayan wanke wanke. Yadda naga kayan a wajen bakyau gani yasa na shiga hadasu har falo duk na kwaso cups din akai amfani dasu da asuba don ranan dai ba wanda yaci abinci zance a gidan. Saidana hada kayan tas na fara sharan part din nasharo ko ina har dakin Iya da mama dubu dana samu ta falka don jin motsina da tayi ina aiki. Falo ta fito ta zauna tare da iya na gama shara na koma kitchen din abincin na tsaya na kalla na tsayin lokaci kafin na juya zuwa wajen su ina fadin mama ya za ayi da abincin nan me yawa ? Ta juyo tana fadin kedai Rahama ina nasan yadda zanyi wanan iskacin na Saare aida yawa yake yarinya ki haramta muna cin abinci haka kiri kiri ? Ta mike tsaye ta biyuni zuwa kitchen din ina tsaye gefe daya na kura mata idanu ta nisa tana juyowa gareni tace ki barshi a tukunyan anjima idan Auwalu yazo yakaiwa almajiransu. Hakan akayi na wanke kayan tas na kara gyara kitchen din ina gab da gamawane naji muryan ya Habu a part din suna gaisawa na fito ina gaisheshi da kwana ya amsa min har zan wuce naji yana fadin. Ramaah ashe Abuja zakije sallah jiya suke fada min asibiti danaje da dare murmushi nayi kawai zan tafi kuma naji yana fadin . Sai kuje da salima kasuwa ki sayi tsaraba anjima gobe akwai wanda zan hadaku yakaiki Abujan nace nagode yaya. Nashige na barsu ina jin mama din tana magana saidai banji abinda tace ba wai ashe tace da alama yarinyar nan ta dauki zancen nan da zafi don banji tana zancen zuwa Abuja ba ai ? Sune suke son tazo masu sallah a can ita wace zataje gurinta ta bugo min waya jiya tana rokona Allah ya kyauta mama din ta fada. Murna yasa tun a lokacin na fara shirina yan kayan da zan dauka da sauran abubuwan amfanina da nake bukata na hada saman gado. Wanka nashiga nayi na fito nashirya zuwa lokacin sun tashi na samu salima zaune tabini da kallo tana fadin kayan meye haka kika hada ? Abuja zanje sallah anty Salima cikin mamaki ta maimaita da Abuja wurin wa nace anty Salma kinsan mutumiyatace sosai yanzun nan da safe ya Habu ke fada min ta bugo waya tana son inzo inyi sallah wajenta. Shiru tayi na dan lokaci kafin ta tashi ta mike ta fita daga dakin nagama shirina na fito falon na samesu suna zaune zama nayi gefe daya ba tare da magana da kowansu ba. Sai iyace ke fadin yar fullo ina za a hakane naga kinyi kwaliya kamar bakya jin azumin nan ke ? Murmushi nayi ina fadin asibiti naso inje iya inyi ,,,,,,, ina jiya kinje Rahama ku koyayyi zuwa asibitin nan fa kuna kanana daku mama ta fada. Naso naje kan tafiyan da yaya yace zanyi gobene kada in wuce banyi sallama dasu ba daidai lokacin ya J ya shigo yana fadin mama kinko ga gidan nan yadda yayi kaca kaca don Allah ? Inda nake mama ta kallo nayi kamar ina kallon tv da wani malami ke wa,azi akan zakkan fidda kai da za,ayi idan ansha ruwa. Sai naji tana fadin ato ita daice me sharan gidan ai tunda tazo gidan nan take wanan aikin bayan ita ba maiyi a cikinsu tana nuna yaranta mata. Suma matanka ba zasu iya komai bane wai Jafaru saidai suci su sha su kwanta su a dole ga bazan ta samu garesu yau da gobefa sai Allah jiki da jini kuma ? Yarinyar nan ta gajine fisasbillah kunga abin nan da yar nan keyi ba a banza zai tafi ba hakan duk gidan da tayi aure nakab fada ince sun huta wallahi. Mijin da zai aureta ya dace mace ba son jiki ba keta ba algus gako wani aiki ta saka kanta yi zata tsaya tayisa tsakani da Allah yarinya ce karama data san ciwon kanta. Haka zakuyi kuma a gidajen ku muddin baku gyara kada ku dauki hakan kamar wayewane kanku kuke cutarwa wallahi. Iya ta karasa fada a cikin takaici tana maida fuskanta wajen tv dake aiki balle dan mutum rana garesa ai, . Yau yarinyar nan bata kimu ba ta yaya zaku nuna baku kaunata kiri kiri haka ba kunya dan zanin da duk dadewansa yan shekaru a jikinta kuce ta kasa ramawa ? Itama fa rayuwane a jikinta kamar kowa yadda kuka rufe ido aka tozarta ta a gidan kowaye dole yaji ba dadin hakan don sai ince duk da sanin ku aikai hakan idan na debe shi namiji a cikin ku da bai bibiyan me ake ciki. Wallahi iya bansan da wanan shirin ba Rahama ai diyatace a yanzu bata da banbanci dasu Salima a wajena don itama a karkashina take rayuwa. Munafunci daine irin ta yaran nan da suka shirya komai da sanin saare aka hadashi a gidan nan makircin nan kuma yana gindinta. Kuka Saare din ta fara tana fadin mama ni ya zanyi tunda sunce ba zasu bayar ba kamar Ramaah zata saka kaya irin wanan tare dasu ? Dama Saiba har ta raba kayan a tsakaninsu ai lace din nan ne suke rigima a kansa jifa wai rigima don Allah akan abinda baku da hakki kansa mama ta fada. Ban raba daya biyu don ko rantsuwa nayi ban kaffara akan wanan zancen yarinyar nan zata tafi Abuja gobe aiba yau take gidan nan ba bataje Abuja ba saida haka ya faru. Wayan da yakeyi ya dakatar yana fadin Abuja kuma me zata tafiyi Abuja gab da sallah haka kuma ? Wai mutanen Abuja din sukace dashi ya bari tazo nan tayi sallah a wajensu niko nasan don wanan zancen suka fadi haka. Shi Habu kuma ya yarda da tafi din ya yarda mana tunda har yazo da safen nan yana fada mata ta shirya gobe akwai wanda zata bi su tafi. Ai nima goben insha Allahu zan shiga Abuja amma bai fada min ba yanzu muka gama magana dashi na shigo nan . Ku barta taje don Allah kada kuce zaku hana yarinyar nan tafiyanta iya ta juyo tana fadan hakan garesu mama dubu tace ai ba zance kartaje ba iya. Sam baiji dadin yadda abin ya kasance ba haka ya fita gidan da bacin rai wani kauye da ake kira da kinkinau suka nufa shida kawu . Wasu filaye ya saya a wajen sai daga baya kuma mai filin yake son ya tayar da ciniki don wani yazo ya kara masa kudi. Kudin da yaya ya ban ba wani sayayya nayi ba na dai sayi kayan kwaliya saura kuma na dunkule abina a jikina don banga wani tsaraba da zan kaiwa anty Salma ba daga bangarena. Sai traveling bag dana saya mai kyau don shi nake kwadayi dama na dawo gida na shirya kayana tsab ina jiran washe gari tafiya idan Allah ya kai mu. Ina barci naji Saare na kirana da dan karfi da in tashi yaya yace in fito mu tafi gabana ya fadi ina duban lokaci shida da wasu yan mintuna na safe. Da sauri na mike tsaye na shiga shiri Allah ya taimaka nayi wanka da asuba hakan dabi,atace watsa ruwa kafin na fara aiki don in samu kuzarin aiki da kyau. Simple dress nayi dogon riga sai hijab a jikina saboda sanyin safiya na fito da yar jakkata da zanyi tafiya nan na samesu falo har da yaya Habu a cikinsu suna magana da dan uwasa. Na gaidasu da kwana suka amsa min mikewa Jafar din yayi yana fadin ka barni dashi Habu nasan yadda zanyi maganinsa ai. Ramaah kin shirya ga yaya zaije Abuja yau shi zai wuce dake don shi wancan sai da karfe biyu wai zai tafi banyi magana ba shiru nayi. Rahaman ta fito kuwa mama dake fitowa kitchen ta fada na amsa da eeh mama tace toga wanan din tsarabarce da zaki dashi ki gaida muna su son Allah a kula da kai kuma aje lafiya a dawo lafiya. Na amsa da insha Allahu mama su har sun kai bakin mota a lokacin suna tsaye suna cigaba da magana da gani dai magana ce mai muhinmanci a garesu. Nida salima iya sai mama suka rakoni har bakin motan da kayana salima tayi mai magana ya bude bayan motan muka saka kayana a ciki. Kafin na zagaya na tsaya ina jiransa a gefe daya salima na min sheri da indai yaya ne yanzune zaku kai Abuja don gudu yake da mota sosai wallahi. Ai shine matsalansa ranan da ya kaimu kaduna ai fada nayi dashi sosai kamar wanda zai tashi sama damu mama ke fadan hakan nidai ina kurum sai ya Habune ya dago yana fadin bude mana ki shiga Ramaah . Baya na bude da zumar shiga naji yace a,a gaba zaki bude mana ai ina ganin kamar ba wanda zai tafi dashi ko ? Ta shiga mana ni kadai zan tafi ya fada daga mama har iya kudi suka dunkula suka ban suna min a dawo lafiya saiga ya Habu ya kara min kudi daya miko min wana rike a hannuna. Nayi masu godiya ya shiga motar suka juya don komawa cikin gida ya fara ribas da motar sai naga yaja ya tsaya. Ta karaso bakin motar rike da yarta a hannu tana fadin wacece kuma tare dakai naji yace ki fadi meye don Allah kada in makara banson rana yayi min a hanya. Lekowa tayi ta ganni kamar in shareta saidai nace da ita ina kwana anty Saiba bata tsaya amsani ba sai cewa ita kuma ina zata ? Tsuki yaja yana fadin gata nan ai ki tambayeta ya fisgi motar da karfi don maigadi na tsaye yana jiransa da get a hannunsa rike. Amma ai ka tsaya dai muyi magana sweet J bai saurareta ba ya fice yanawa maigadi horn da mota na lumshe idanuna na hankali a yadda nasan halinta zasuyi rikici