← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 306

Sashe 224

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baifi sati daya ba da wanan rikicin Maria ta haihu ta haifi danta namiji na shiga cikin sahun yan murna amma banje barka ba. Don halin,mu na fulani daya motsa ance rikon magana sai bafullace gaskiyane wanan maganan don kuwa muna da hakan a cikin jinin mu idan kai muna abu zamu ajeshi a ran mu na tsawon lokaci komai dadewa sai mun dauki fansa akan abin gareka wanan haka yake. Nima ta haihuwanta na haketa don naki ko nuna zanje barka har akai kwana ukku da haihuwa ta bugu tana tambayana wai lafiya nake kuwa ? Amsan dana bata shine ban jin dadin jikina kawao don itama haka takan fada a lokacin Allah ya baki lafiya Ramaah ta fada ta kashe wayan don ta fahinceni. Aka kai kwana biyar yaya jafar da kansa yake fadin kinko je gidan Habu kinga jariri Rahama a takaice na bashi amsa da banje ba yaya kuma ban zuwa. Ya kalloni da sauri tare da furta subbanallah lafiya meya faru nace dashi ba komai kawai dai banjin zuwa gidan ne kawai a yanzu. Nasan dole dai akwai wani abu amma yar uwarki ta haihu zakice ba zaki ba Rahama ko akwai abinda ya farune ban sani ba yake tambaya ? Ba komai hakan dai nace ba zani ba na sake fada ina kokarin fita daga dakin bansan ya sukayi da mama ba sai gashi naji maman tudu tana min maganan tace. Mijinku ya fada min kina fushi da yar uwarki nima nayi tunanen hakan tun shekaran jiya da naga bakije gidanta ba har wanan lokacin saida raina ya bani akwai dalilin hakan ? Kiyi hakkuri da yar uwarki kada ki bari har a gane kuna da matsala da ita a gidan nan ki shirya gobe kije ki dubata in ma wani abu tayi maki ki boye hakan kada ki yarda a gano hakan ayu maku dariya. Wanan maganan da mama din tayi min yasa na shirya naje tare dasu da iya ina gidan mahaifiyar mu ta bugo waya nake ce mata ai gani gidan acikin harshen fulatanci nake fada mata abinda maria din tayi min. Take fadin wai nasan halin maria ai wanan halin nata ai yasa aka hadota dani zuwa aure katse ummah nayi da fadin dana san haka zai cika dani ta dalilinta ta kuma gudu ta barni da ban biyo ta zuwa garin nan ba. Baki yarda da kaddara ta riga fata ba ke nan ko ina kike tunda Allah yayi jafar mijinki ne sai kun hadu don haka ki daina cewa itace tayi sanadin haduwan ku Allah ne ya hadaku tun farko. Wani malolon bakin ciki na hade ina goge fuskana ban tsaya ba duk yadda taso in tsaya muyi shawara na koma gida tare dasu mama hakan yasa ta fadawa habu mijinta halin da muke ciki da ita din. Ba kunya sai gashi ya shigo da yamma gidan muna zaune saman baranda muna shan iska don ba wuta shi yasa muka fito daga wajen ginan mu samu iska. Bandashi yaya da yake ciki zaune tare da mama suna hira bayan mun gaisa dashine har dan shiga sai kuma ya dawo yana fadin zo nan Rahama ya shige ciki ya barni ina kallonshi ta baya. A dakin na samesu su ukku tare da ya J da mama suna zaune na shiga ina kara gaidashi bai karba min ba ya hau fadin Rahama meya faru tsakaninki da yar uwarki ta kirani tana kuka wai kinki tsayawa kuyi maganan komai a tsakanin ku. Saida na lumshe ido ina hadiyan zuciya nace ni din nan kuwa yace look Rahama banson irin haka dole akwai wani abinda ya faru tunda har tace hakan. A,a habu ba zaka shiga tsakaninsu kayi saurin yanke hukunci ba yanzu ka nuna kamar laifin na wanan yarinyarce ita kadai ita matar naka bata fada maka dalilinta nayin hakan ba ? Tace ita bata san tayi mata komai ba haka kawai ta tsiri fushi da ita yaushe ma maria zata tsaya yin haka ga wani balle Rahama ? Kaji ai mama ta fada niko a cikin yaren mu na soma magana ina fadin ai dole kace hakan tunda dukkan ku baku dauki hakan wani abu ba tunda niba mutum bace. In zaki fada da hausa ki fada kina muna maganan da bamu ji so kike ki tayar mata da hankali bayan kinsan halin da take ciki a yanzu. Ina jin hakan bansan lokacin da hawaye yazo min ba na soma fadin niba mutum bace ai tunda ta kasa yi min abinda ya dace lokacin da nake neman wani na kusa dani a wajena. Kamar yaya ya fada ya kura nin ido zuciya yazo min na ci gaba da fadin ashe ba dadi itama ta shareni kamar bata san inda na fito ba ? Dama ai ,,,,,, kai habu kada ka matsawa yarinyar nan don Allah kasan dai a yanzu halin da take ciki don Allah ka daina maganan nan tunda tace ba komai kasan dai ba fada maka abinda ya hadasu zatayi ba . Nayi mata magana dazun taje ina shike nan koma meye ai ya wuce dai yanzu ko so kke ta tare a gidab ka baki daya tabar mijinta a nan kwance ? Amma mama ai gaku tare dashi kinsan mama ta hana kowa irin zuwan nan da akeyiwa mace idan an haihu sai daga can gidane suke zuwa nan tace tunda salima taje taga baby bata koma kuma ace itama din bata zuwa ai hakan baiyi ba mama. Amma habu ban zace zaka shiga tsakanin yaran nan ba harka nuna kana goyon bayan matarka haka kiri kiri inma laifine matarkace ta fara mata ai kasan su fulani da riko nasan shine take nufin zata rama itama ga nata wautan ? Sai lokacin yayi magana tunda dan uwan nasa ya soma magana yana zaune ya kura mashi ido yace dashi habu bakaji me mama tace dakai bane wai ? To ka barsu kawai banson irin hakan Rahama dai dole taje wajen yar uwarta baka san sanda suka sami matsala ba haka ba zaka san shirinsu ba kuma . Yanzu kazone ka daga mata hankali kuma kome tunda dai an tillasata mata zuwa kuma ta tafi ka fitar da bakinka a cikin matsalansu don Allah. Su kuma yaran nan da basuje ba don kansu ai sun kumayiwa kansune ba wani ba suma matane ai kamarsu ko ? Shina so in fada ka rigani abinda basu kulaba shine maganar da ya J din yayi a lokacin mai tsayi wanda tunda ya kwanta ciwo zance karona farko ke nan da naji yayi magana mai tsayi irin haka ? Haka kuma kariyar harshen nan nasa a ysnzu ya rage harafin bakinsa yana dan fita daidai a cikin yan kwanakin nan tunda ya soma zama da mikewa din nan . Sai dai kuma na lura da wani yanayi idan ya mike ko yai magana zaita yin zufa yana dan haki na dan lokaci kafin ya koma daidai. Wanan karon ma hakan ne ya faru dashi idon dana kura mai shiyasa mama fadin daidai habu din yana mikewa tsaye tace. Kazo har ka saka dan uwanka magana yau yaran nan da abin dariya kuke wallahi kowan ku a nan ya shigarwa matarshi ke nan ko ? Muryan iyace ya katseta tashigo tana fadin yanzu saratu kece muna gaka nan ka shigo nasan fita zakayi abin ka kuma yasa na taso. Iya fushi fa nakeyi da kowa gidan nan yanzu fisabillahi iya ace har dake matana ta haihu bakije kin zauna da ita ba kina gida abinki zaune iya ? Yi min adalci mana dan nan iya din ta fada a marairaice tana wani irin lagabe kai tace yaron nan yana haka ai in nabar gidan nan sai a zageni ? Hakane yanzuma aida nashigo anan din na sameki bakomai ai iya don kawai na dauke iyalina mun bar gidan nan shine kowa ke fushi dani ko ? A,a habu idan kowa yayi fushi daku kasan bandani a cikin shirmen nan wanan abin dana fada shine kawai dalilina amma kai min aikin gafara gobe zan je insha Allahu in rai yakai. Sun dan jima suna zance dashi ya fita bai kara bi ta kaina ba nima ina zaune ban daga daga inda nake zaune ba tare da iya ya fita mama kuma ta mike zuwa bandaki . Hannu ya miko min alaman inzo inda yaken zaune banki ba na mike zuwa gareshi na zauna a gefenshi ya soma fadin kina son raina ya bacine Rahama. Fushin nan da kikeyi da kowa ya isa hakana nine mai laifi ba wani ba kuma nabada hakkurin ai niba fushi nakeyi ba na bashi amsa ina kokarin mikewa sai kuma na koma na zauna ina fadin. Na kula kamar maganan ka yana son dawowa daidai amma kuma kana wahala ga hakan don zufan da naga kanayi da yawa yace haka nima nagani . Saidai gaskiya ina jin saukin jikin nawa sosai a yan kwanakin nan karfin jikin daine sai a hankali amma Alhamdullahi gaskiya. Na lumshe idona ina tayashi yin tasbihi ga ubangiji subbahanahu wata,ala daya nufemu da ganin hakan . Wa zaisa bawan Allah nan zai mike haka yau shine Allah ya tayar a cikin ikonsa haka har yake iya wasu abubuwan daya shafi rayuwan sa dana iyalinshi haka. Muryan mamace data leko tana fadin to kina ciki bari na leka wajen dubu ance tana fama da kai yau tun safe data shigo bata dawo nan din ba . Hakan ya kawar da shirun namu da yake fadin agaida mama din ni dai bance komai ba don nashiga na samesy zaune da saratu suna magana da ita da saratu nagaida ita naga ta amsa min a dakile. Na saba da hakan da mama ke min tun abun yana damuna har yanzu na share na fitar da komai a raina abu dayane kawai ina kare abinda zaisa ta taba min mutuncina. Iyakarmu gaisuwa inma tazo waje ina kokari na kaucewa wajen don gudun samun matsala a tsakanin mu a bakin maman tudu na kara fahintar wasu halaiyan mama din daya kara sa nake taka tsantsan da ita. Mun jima a tare dashi dakin zaune kafin Anty Asmau ta shigo da yara suka zauna suna hira hakan ya bani dama
Chapter 224 · 0% Book details