← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 306

Sashe 155

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yaran nan suka zo da zancen a fito da kudin nan a raba abawa kowa nasa to gashi an raba din sun kuma salwanta don da kudin na hannusa da yanzu tana tsakuran abinta tanaci hankali kwance ai. Kuma da duk haka bai taso ba ai irin wanan abu ina yai dadi in zaki sake hali gara ki canja akan mu,amulanki da yaran nan. Shi miskilin daki ai kinji amsan daya bada ko yace ai mijintane don yaci kudinta to meye aure kuma aiba za a hanashi ba tunda yana da ra,ayin hakan aita sani ta bashi kudinta din. Kai iya wake zancen habu don Allah koshi Jafar din ai nasan yaki saurarensane ya yanke wanan hukuncin amma Habu ai sam baiyi ba wallahi. To koke fa amma yaro yazo da abinda zai fishemu kina wani zance so kike ke kije idan su yan uwanta basu je ba kome gashi har da abokiyar zaman ki za a tafi me yafi haka dadi don Allah kin kuma san ba zai kyalesu su tafi hakana ba ai. Yanzu dai zan hada da Saratu ko salima su tafi tare don kada ya kasance nan dakin ba wanda yaje a cikin mu hakan zai kara kwantar mata da hankali ai idan taga dayan yaran nan cikin su. Yanzu dai ke akeji kuma shi dai ga abinda yazo ya fada ai idan saratun zata tafi ba sai a fada mai ba idan akwai waje ? Akwai waje mana iya tunda su uku ya lissafa zasu tafi saida ya dawo take fada mai cewa da saratu ko salima za a tafi yake fadin . Mama banson abinda za aje ayi tashin hankali a can don Allah wanan yasa ban saka kowa acikinsu ba har Nafisa. Ka dai bari dayansu taje zanja masu kunne kada hakan ya faru bashike nan ba shi dai baice komai ba saida zai tafine yace da karfe bakwai zasu wuce fon haka mai zuwa ta shirya a cikinsu din. Washegarin din kuwa hakanne ya faru bakwai na safiya suka biyo daukan saratu din don ita tace zata salima tace itama ba zata ba don zasu tsaya shirye shiryen suna a nan kafin a dawo. Yaba dukkansu dubu ashirin inda inna yabawa kudin tabawa kowa don haka saratun nashiga motan ta mika mata nata kason tayi wani kata ta bata rai alaman don me za aba inna din kudi ta bata. Haka dai suka dauki hanya karfe dayan rana suna gidan barakha din inda suka sameta cikin tashin hankali daga ita har yaran nata. Taji dadi sosai da ganinsu tayi kuka tana masu bayani inda suka bata hakkuri kan ta daure namiji yafi danan idan ya tashi kumsawa mace bakin ciki ai. Ta shareshi ta nuna ba komai tunda Jafar ya nuna zai dauki mataki akan kudin nata miliyan biyar da dan kai dayayi mata dadin baki ya karbe. Ai kafin wani lokaci labari ya karade unguwa na zuwan yan uwan Barakha din kinsan halin mutane nan makwabta suka fara shigowa suna fadin albarkacin bakinsu. Yaya Ai tace ba komai ai tsakanin miji da matane ai aure karuwane idan akwai fahinta don haka fatan zaman lafiya suke masu yanzu. Wanan zancen sai a kunnen Iliyasu ya shigo yana fadin kwarai yaya abinda naso barakha ta fahita ke nan taki fahintana aure mukkadarine banyi auren nan don in tozarta taba wallahi. Ba wani kadai bata kudinta aiba auren akace kar kayi ba kudinta dai take bukata kawai a hannunta saratu ta fada don tana kule dashi tun shigowanshi gidan. Haba saratu ke da na dauka zaki goyi bayana kuma har dake cikin wanan tunanen yanzu dai ayi min hakkuri nasan nayi laifi don Allah. Ai haka zakace dama yanzu kai don Allah dama haka amaryan zatazo ta samu yaya daki kamar zauren malam ? Daki ba komai alhalin tana da kudin ta ka rike kana kumsa mata bakin ciki haba saratu yayanki fa taki kwantar da hankalinta muyi magana. Yanzu dai kawo wani abu a shiga kasuwa ko kayan amfanin daki a saya mata sai ya kwashe da dariya yana fadin saratu hoo ? Ya shura takalmanshi ya fita matar zata fara fada yaya Ai dai ta tausheta tayi shiru sukayi sallah sukaci abinci sai suka dan fita. Kudin da Jafar din ya turo masu da suka sanar dashi abinda suka sameta ciki suka dauki babban yarta tare suka fita basu dawo gidan ba sai yamma lis. Sun sayo gado har da sabon katifa dasu zanin gado kula haka dai suka hado mata kaya kamcankam kamar amarya. Allah sarki tana ganin hakan kuka ta saka don murna dama wanan ne burin mace da za aiwa kishiya kada kishiya tazo ta sameta hondadakwai daki kamar zaure. Basu zauna ba suka shiga gyaran dakin nata hakana ko fenti babu amma ba laifi kayan saiya haska dakin ya fito neat dashi nan aka zaune hira saratu ta samu bakin fadawa yar uwar sakon mama din tana fadin ai kingani yanzu dai sai ki san zamanki da mijin nan naki. Yau badon ya J ba da kunyan duniya yaciki kan mijinki donshi ko a jikinsa bai damu da halin da kike ciki ba balle yayi tunanen hakkinki yana hannunsa ba ya fidsake kunyan hakan. Bari saratu har kunyan jafar nake ji idan na tuna da abinda ya faru yadda mukai ta sakin magana a lokacin kan kudin nan amma hakan baisa yayi fushi dani ba sai ga hawaye na zubo mata. Tana kuka saratun tace ai mama zaki godewa tunda ita ta tsaya yai hakan don badon mama ba wallahi Ya Habu ba zai bari ya kalleki ba mamace ta datse shi yai hakan . Muryan inna da basu san da zuwanta wajen bace tace ko yaya ta saka yayi in baiyi niya ba aiba zaiyi ba. Ji inna don Allah saratun ta fada tace kwarai ku dai godewa Allah daya bamu Jafar a cikin mu wallahi ya kamata a dubawa bawan Allah nan irin kokarin da yakeyi din kan yan uwa. Bawai dakinku ba kawai duk wani abu na gidan nan yanzu Jafar ne jigo ko wani daki kuma ko haihuwan matan isah shine ya aiko da komai da akayi ga hadin kan yan uwa da yake kokari yi a yanzu. Barakha a cikin kuka take fadin ai gaskiya inna ta fadi saratu ko mama ta saka yayi inbaiyi niya ba aiba zai min ba ko ? Ni sai ince auren nan na jafar alheri ya zamo muna yanzu wallahi tunda kan gida ya haduwa ta dalilinshi ba kamar baya ba da kowa yake a watse gidan. Wanan zancen da inna tayi bai kwana ba saida saratu ta faki ido taje tayi waya da mama tana zuzuta maganan ga abinda ya dace ta fada ta tsaya tana haddasana a tsakaninsu kuma. Washegari dasu da yaran anty baraka din suka taru suka kara gyara gidan tsab da wasu makwabta aka dora girki ta saka les din da mama ta aiko mata dashi ta hanyar saratu. Wanan yasa duk wani iya shegen da aka dau damaran yi ba samu yiwa barakha din ba don dan uwanta da yafitar da ita kunyan duniya lokaci guda. Sai ga kayan kallo da frdge sabo ibrahim ya shigo dashi haba anty Barakha a gaban yan unguwa tasa sabon kuka tana fadin Jafar jafar yau ka zamo min uwa da uba a cikin duniya na gane ba abinda yakai dan uwa dadi a duniya. Dan Uwa Murfin Jallo Ya J ya dinke wanan wanjen sai kuma wani.
Chapter 155 · 0% Book details