← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 306

Sashe 43

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka shiga part din ya J ita da su mama dubu da mijinta nasan sallama sukayi dasu mijin nasu dake gari shine kadai ya fito har bakin mota yana fadin gashi nan zuwa asibitin idan ya shirya. Haka suka daga suka bar gidan duk kokarin dakewana saida hawaye ya zubo min ba lokacin ya J yazo ya wuce mu zuwa part dinshi lokacin nake jin muryan Asmau na fadin wai har sun tafine ? Sun tafi Salima ta fada saita amsa da Allah ya sauwaka dama ashe bata da lafiyane take yawan zama haka lukume a daki ko yaushe? A daidai lokacin Saiba ke fadin wai har ciwo ma sai an boyewa mutum a gidan nan abu har yakai haka muna gidan nan bamu sani ba ? Koda yake ance kowa ya samu rana yayi shanyinsa cikin ne za ace za aje asibiti a zauna har sai an haifeshi ni ban taba ganin irin haka ba gaskiya. Na kula da lokacin da Saare ke nuna mata ni da idanu naji tace ai gaskiya na fada Saare shi ciki ai har ka haifishi baka taba jin dadi a rayuwanka sai ranan daka haihu. Yadda take magana yasa naji ba dadi a zuciyana itako tacigaba da fadin kudi yayiwa Habu yawa koda yake ba zafinsa bane tunda Allah ya kashe ya bashi ta dubi kishiyanta tana fadi ita kuma tayi wani irin meda baki. Sai naji Saiban na fadi a to mana ke inbashi ba dai naga mu duk lalura baisa munje mun kwanta asibiti saidai asayo muna magani a hadamu dashi kawai ? Amma ai kowa da irin yanayisa ko yanayintane yazo mata a haka ai ko ita bada son ranta taje kwamciyan asibitin ba . Tunda gashi ta fita tana kuka dadi zaisa mutum kukane Salima ke fadan hakan cikin hasala data karbi zancen da yar uwarta ta soma yi dasu din. Zo muje Ramaah kinji mama tace idan sun tafi mu gyaro wajen mu kulle masu ato nidai ga gaskiya na gani ba za a hanani yin magana ba dai kan bamu tsaya karasa saurarensu ba sai dai muna gab dashigane mukaji muryan mijinsu na kiran Asmau. Shiyasa akace matan saure sunfi kishiyar miji daya kishi wanan ba karya bane don matan ya J da suka fito fili suka nuna bakin ciki ga yar uwata ranan. Ashe bani kadai naji haushin abinda sukayi ba din har da Salima don ina kitchen ina hada kayan datace in kwashe zuwa cikin gida naji salima din tana fadin. Shiyasa suke bakin kishi tsakaninsu ai ina abin dadi a zaman asibiti ga mutum har wanan abin yakai zancen banza haka ? Ciwone ai yasan kofan kowa sanda zaizo gunka baka sani ba tunda ba sallama maka zaiyi ba ai munafuncin banza da wofi kawai ? Ni dai banyi magana ba amma na rike hakan a raina akwai ranan magana matukar muna raye na nasa hakan a zuciyata. Bamu zauna ba nida Salima abinci muka dora don mama ta gargademu da hakan mu hada abinci akai asibitin da wuri basai na can sunji yunwa ba za a kawo masu . Kafin sha biyun rana mungama miya da abinci tana zaune tana yanka salad da kayan had iya na zaune tana jan tasbaha a gefen ta . Ni kuma ina kitchen na dora ferfesun da mama ta bugo waya tace a hada na kifi. Ya Habu ya dawo yana tambayan makulin part dinsu da muka rufo masu naji iya na tambayan ya mai jikin take ? Naji yace sun bata gado sun fara dorata a dokan sun kuma hana a aita yawan sintiri a wajenta don barcin da akeson ta dinga yi ko wani lokaci saboda lafiyan abinda ke cikin cikin nata. Bakaji ba mai lafiya yana zama haka don son rai ka zauna a hanaka mu,amula da mutanen arziki su wa yancan sakarkarun sun dauka hakan wani abune har suna tsayawa gulmam hakan . Shi Jafaru ya sameku can ko zai fita don bai tsaya jin zancen nata ba ya juyo yana fadin muna tare dashi iya shiya biya kudin komai ma har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya. Ai dama nasan ba zai bi kan matansa marasa kan gado ba tunda shiba sakarai bane irinsu wai iya anyi wani abin ne ya dakata yana tambayan tsohuwar ? Anyi mana Abu matan dan uwanka ke gani wai saboda makirci yasa yarinyar nan karyan zuwa asibiti ta zauna a can don kawai ta,,,,,, Haba iya ki bar yaya yaji da abinda ke damunsa don Allah matanda basu sawa basu hanawa idan an tashiyi sune basu san Allah ba cikin zancensu Saare ke fadan hakan ga kakan tasu . Koya gane me take nufi da zancen ta yasa kai ya fice daga part din bai jima ba ya fito a cikin shirinsa nan Salima ke fada mai mun hada abincin asibiti yace har angama ta amsa da ehh mama tace kada mu makara ai da hada abincin. Ku fito dashi na kai masu don kaduna zan tafi yanzu in sayo wani magani da za ai mata amfani dashi nan ban samu oroginal dinsa ba. Allah ya tsare mukai masa bayan mun saka kayan a bayan motanshi din muka nufi cikin gida nikan Allah ya gani ban iya cin abincin ba a ranan don har lokacin ban fahinci komai ga zaman da zatajeyi asibitin ba. Mahaifiyar mu bata iso garin ba sai dare wajajen tara muna daki salima dai waya takeyi ni kuma ina kwance naji ana mata sannu da zuwa . Muryan ummah na tsinkayo a kunnena tana amsawa hakan yasa na dubi anty Salima ina tashi zaune nace muryan ummah nake ji fa ? Waye ummah ta fada tana kallona nace mahaifiyar mu tare da ita muka fito falon tana zaune suna fira da iya dake tambayanta hanya ? Sannu da zuwa muke mata saidai ni a cikin yare nake mata magana ina tambayanta yan uwana tace suna lafiya taso tazo da umar sanda ai amma ta barshi agidan hardo saboda karatunsa . Ku kawo mata abinci ko iya ta fada sai ummah din tace sallah zatayi tukun a nuna mata ban daki tayi alwala na mike tsaye don bansan inane zan kai ta ba sai Salima ke fadin kaita bandakin mama mana ta sauka a nan. Lokacin anty Saare na part din ya J bata sanda zuwan ummah namu ba ni dai a yadda na dauka shine tana zuwa dan hirane part din. Amma sai inji Salima na fadin don kwadayi da munafhnci take yawan shigewa matan yayan nasu in bashi ba sau nawa suna masu wullakanci a baya lokacin da yayansu baiyi karfi haka ba? Amma yanzu wai duk anty Saare ta manta da hakan suta koma tana shigewa don suji dadin wullakantasu ke nan kuma. Dakin yana nan yadda muka gyarashi da safe nan ta shiga yayi sallah ta jima bata fito ba salima ta dauki kayanta takai mata dakin ba wasu kaya bane sosai sai manshanu da kindarmo mai yawa datazo muna dashi da nama soyayye. Abinci ma da iya ke magana nayi murmushi ina fadin ummah ba zataci abinci ba nan iya saboda kunyanki kinsan nan gidan surukintane ai. Salima tace shine kikai shiru Ramaah ta mike ta suri kayan ta sameta dasu a daki nan ta jera mata har da jawo kofan dakin don tasan babu mai shigowa hakan yasa ta dan tsankwari abincin kadan ta aje. Bata sake fitowa ba falon sai washe gari ta fito da shirinta tana dakon yaya ya shigo ya tafi da ita asibitin da zata zauna. Inda muke ta kokarin hada masu breakfast da za a kai asibitin haka kuma iya ta lasa muna tare da mu za,a tafi mu dubasu a can. Yasa mukai komai a gurguje inda na saka nonon kindarmon a cikin fridge na rakumi datace min don yar uwata tazo dashi ta dinga sha na diba a cikin wani gora da za akai mata ta dinga sha na kada a kulan kankara. Mun shirya tsab koda ya fito yazo gaidasu iya da ummah ya samu har iya din mun shirya muna jiransa bayan an gaisa muka fito da kayan muka kwasa zuwa asibiti gaba dayan mu yan part din aka rufe shiyan. Sam ummah bata sake ba har muka kai asibitin cikin nauyi da kunya take don ta shiga motar surukinta koshi don ba wanda ya santa a zaria ne yasa har ta yarda ta shiga Ya Habu ya jata. Duk ko da dan wayewan kai da ummah kedashi wanan baisa tayarda akidan mu ta fulani ba don anty Yanda yar farice a wajenta kuma yarta ta cikinta suruki zai dauka a mota haka ? Ba laifi gaskiya don ba zakice asibiti bane ba ,a kuma kilance wajen ba dakin masu irin lalurar yar uwata din itama aka ajeta munje daidai visting hour don haka kofa a bude take lokacin. Aka gagaisa da juna tsakanin ummah da mama ana satan kallon juna a tsakaninsu sukaiwa juna jaje akai tayiwa ummah yaya hanya da mutanen gida. Gadon da anty Yanda take mukaje gaida ita ga kayan more rayuwa nan an baza gwanin ban sha,awa zakice ba asibiti bane na fada a zuciyana ina kara bin wajen da idanu. Munkai kamar minti talatin matan ya J suka iso tare dashi suma da nasu abincin nasan shine yasakasu yi dole saidai yadda suka samu yar uwata din akwance haka ya tabbatar masu bata da lafiya dai kan saidai ba wani sosai ba. Ban da sakin jiki dagani har ummah a wajen su dai keta hiransu da kuma baza ido suna gulman wasu mata da muka hango dan nisa damu masu irin matsalan nata. Shigowan yaya J dakin da ya Habu ya sa duk akai shiru inda suka karaso bakin gadon yana gaida ita nan yake tambayan mama ko anzo an mata alluran da safe mama tace anya basuyi ba kan. Ya juya yana fada ya habu yabi bayanshi suka fice daga dakin sai lokacin saiba tayi magana take fadin. Wani kan ba zan yarda in kwanta a dinga surbuda min allura haka ba gaskiya daga can inda mama take zaune ta bata amsa da fadin itama ta kwancen ba da son ranta hakan ya sameta ba ai ? Komai
Chapter 43 · 0% Book details