← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 306

Sashe 225

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

samu na mike nabarshi dasu na fara gyaran part din dana gama kuma wanka naje nayi na fito. Saida darene mama ta samu daman yi min fada sosai kan nayi hakkuri da yar uwata kada na yarda aji kan mu har a gane muna da matsala tundai saratu taji zancen zai juya wani abu na daban a bakinta . Na fahinci ba saratu ba har salima mama tudu ta tsana acewarta mahaifiyarsu ta sagartasu sunki aure suna abinda suka ga dama a cikin gida zaune. Dole washe gari na shirya na tafi saidai ban barta ba don yadda nayi kuka itama saida na sakata yi don na fada mata abinda ke zuciyana. Inda ta nuna ba hakana bane wai mijinta ya hanata fita saboda matsalanta yasa ta kiyayye dole dai na zage nayi abinda ya dace ace nayi a wajen duk da karfin hali nakeyi a lokacin. Saidai nasha zunde da sheri a wajen yan uwansu a ranan kowa da kalan sherin da yake min akan cikin dana samu a yayin jiyar miji ni dai nawa kawai murmushi. Ban dawo gida ba kamar yadda kowa ya zata daga gidan ya habu gidana na nufa a ranan a can na kwana don ina son gyaran gida nida Anty Nafisa da wata yar yaya Auwal mukazo gidan muka kwana. Koda mama ta kirani a waya nace dasu gani nan gidana mama ina son inyi gyaran gidan ne duk yayi kura yana bukatan gyara take fadin ga mijin ki nan yana fada dake hakan baisa na dawo ba a ranan saidai nayi mata bayani maganinsa daya dace a bashi na shafawa kuma su san yadda zasuyi. Ba komai yasa na koma gida ba sai gulman da akai min kan wai ina ha,intar kishiyoyina na fake ga sunan jinya na karbe masu miji dama mu fulani haka muke da kwatar maza . In badon cikin daya baiyana min a jikina ba da ba,a gane muna cutasu gashi najawa Saiba saki saida ya fara samun lafiya nasa an sake ta saura Asmau itama in batayi hankali ba korata zanyi in zauna ni kadai kamar yar uwata. Naji dacin wanan maganan sosai da naji hakan yasa na yanke shawaran komawa gidana tundai da naji ance Asmau dince take fadin wai sun zama yan kallo yanzu basu gane komai a gun yaya din dul na tare komai banson kowa yazo kusa dashi saini kadai ashe mun san abinda mukeyi ni dashi ? Nasha alwashin duk abinda za ace saidai ace don ba zan koma gidan ba kuma zan dai dinga zuwa in dubashi a can din iya abinda nasa a raina ke nan. Washegari na tashi da aikin sosai su anty nafisa suka tayani a yadda na fahinta kamar ta samu manemi a yanzu din don bini bini sai ya kirata a waya sun dade suna hira dashi. Misali karfe biyu na rana mama ta kira waya tana fadin har yanzu bamu gama bane karya nayi mata nace mama gaba daya gidan yayi kura saida muka fitar da koma ana kakabewa . Da dare kuma ta kira tana tambaya nace mama ina ganin sai gobe don da sauran aiki ban koma ba dai har kwana uku gana hudu nayi abinci da safe na shirya zuwa gidan. Acikin kwaliyata na shiga da basket din abincina tiwon semo da miyar egushi nayi dayaji nama na aje basket din a wajen su mama da iya. Muka gaisa tana min sheri tace kice kin koma gidane da wayau yar nan daga zuwa suna saimu nemeki mu rasa ? To meya rage yaya tunda sun gama aika aikansu dashi kuma ai saita koma gida tayi jinyar cikin yanzu kuma ? Tana jinyar ciki ita daya ga miji a nan na mike ina murmushi zuwa ciki na samu yayi fushi sosai dani hakan bai dameni ba na gaidashi da kyar ya amsa min . Duk daya ban tausayi nasan banyi daidai ba don ko kallon dakin kawai da nayi dakin ma kansa yayi missing dina don sai ince bai samu gyara ba daya kai sau biyu. Har wani dan bashi dakin keyi a lokacin zaune nakai ina gaidashi bai amsa ba ya kyaleni nima nayi shiru muryan mamace ke kirana tana fadin kizo ki dibarwa mijinki abincin nan nasan zaici sosai tin shekaran jiya yake maganan tuwo gidan nan an kasa yi mashi. Na mike naji yace No ki barshi ba zanci ba nayi murmushi ina fadin yaya fushi kakeyi dani ke nan bai daiyi magana ba harna fita. Na debo abincin a plate zuwa gabanshi na aje yadda yake kallon abincin yasa na mike na koma na debo ruwa a gabanshi na zauna na fara dibowa ina bashi da kyar na samu ya karba bayan ya gama fadanshi cikin zafin rai yana fadin nasan inba niba wazai samu yana taimaka mashi yadda nake mashi ? A tausashe na soma magana ina fadin yaya ka tuna bafa ni kadai bane matan nan suna da hakki a kanka tunda yanzu ka dan samu lafiya har kana dan iya mikewa ya kamata suma a basu hakkinsu ladan nan kowa fa yana son samunsa don Allah kayi hakkuri in zauna gida itama ta dan taba ta samu ladan hakan . Na jima da loman abincin a hannuna saida na gaji nakai bakina na sake debowa na mika mashi ya karba ya kumaci sosai ya gama na kwashe kayan. A wurin mama nake jin cewa ashe zuwan da Yazid yayi shiya turashi ya daukoni sai yaje ya samu muna gyaran gidan da gaskiya ranan tace dani. Ranan munga tashi hankali ai na zata ai inkin dawo zaiyi fada sai kuma naji shiru koda yake dubu ta taka mashi burki ai tayi mai tas tace ya barki mana idan zaki koma can ne ki koma da yake fadan mu nan ba mutane bane a tare dashi ? Ko ita Asmau bata iya mashi komai da kike mashine ta dai kwana nan din sau biyu jiya banga tazo kwanan ba wai danta baida lafiya tace . Oho dai na fada a raina ba dai zan zauna ba kuma a nan na wuni na gyara masu ko ina tas na shiga wajen kowa da yamma kuma nace ni zan tafi kada yamma yayi min. Kallona yayi Asmau tana zaune ba daman yayi wani abu yace saida safe kawai saiga iya take fadin yanzu dai kinyi hijara ke nan kardai kin gudu ke nan fa ? Iya gara ingudu inbarwa anty mijinta tunda ya samu sauki a yanzu itama ta samu nata rabon na tare waje da sunan jinya na hanasu ganawa da mijinsu yadda suke so . Kamar yaya kin hanasu ganawa da mijinsu yanzu ko da aka ga idanunsa sun bude aka san wanan da kikai wahalan ki a lokacin wayace zai kama maki hakan ? Gulman nan yazo kunneki ke nan don wanan dama kika koma can ke dai ai gulman nan ya jima da fita gidan nan yanzu da kika tafi din waya iya abinda kikeyi masa din ina zaune yake cikin takaici da kazanta kawai ya isheshi gidan nan . Zai dai tattaro ya cin maki can mamaku ma tace gida tayi tunda Allah ya kawo sauki na hanata tafiyane don in kun tafi gaba dayan ku abin bai dadi gara dai ta sauna har akwana biyu. Banda gulman me suka iya sunan son miji ne kawai abaki amma babu hus a garesu mutum bai kula da kansa ba balle wani saida yazid yayi cin mutunci yadda suka bar gaban gidansu da kazanta dazun . Murmushi nayi na saba gyalena ina fadin ni zan tafi shiru yayi kamar bai jini ba a raina nace kaji dashi ba dai zan zauna ba din a kara zagina duk a yanzu dai zagin bai kankaruwa a gareni ba riga dana shafawa kaina wanan kuma ?
Chapter 225 · 0% Book details