Sashe 178
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
maki ra,ayin kainane hakan. Banda ra,ayin zama a cikin yawa haka shima jafar din da aka tauye ya zauna ai banga wani abin karuwan daya samu ba ga haka. Abinda yakamata ace kin dage akansa mama kin kasa dage muna akan masifan dake bibiyan rayuwan mu ki sa kawu gaba zuwa garin matan nan dayaje ya karbo maki haihuwa kin kasa haka mama kin tsaya ana zugaki a kan mu don mu lalace . Ba laifi idan yau kin min baki kan na bar gidan nan na koma muhalin kaina na zauna don in samu zaman lafiya a rayuwata. Kullum kana wajen aiki hankalinka ba a kwance ba kana tsoron abinda zaije ya dawo na samu Allah ya hore muna kuma zakice baki yarda ba sai dai kiyi hakkuri donnni na tashi ke nan bafasawa zanyi ba. Haka kuma dolene muje wajen nan a wanan karon abada duk wani abinda akai alkawari bayarwa don dan uwanmu dake cikin matsalan rayuwa. Zuwa lokacin kuka sosai mama takeyi akan ya daina amma ya tsaya sai daya gama fadin abinda ke bakinsa ya kallo maria yana fadin tashi muje. Maria kinyi nasaran rabani da dana yau har yakai habu bai saurarena sai ke hakan bai maki ba kin shiga kin fita kin cusawa Jafar ra,ayi akan yar uwarki to ki saurari shirina yadda kika rabani da dana haka kema zaki rabu dashi indai harni na haifeshi. Tsoro ya kama maria din dajin furcin mama ga kowa dake gidan tsaye an fito haka ya cusata mota ya shiga yaja motar suka bar gidan . Nan suka shiga bawa mama hakkuri mai sunan zugi suna fadin aidama haka aka tsara tunda anan idon kowa na kansu ba a samu yadda akeson a mulkesu ba yanzu ko ai shike nan sai dai mama din tayi hakkuri. Jin irin abinda saiba ke fadi har tana cewa su dai da aka mayar shakatafi ai an tauyesu an hanasu walawa din ga yan kauye don samun waje sunzo sun karya dokan da aka kafa kuma ba ai komai ba. Haba keko Saiba wanan maganan bai dace ba mana samunefa koshi ya J ai ra,ayinsane zama a nan din don kowa yasan yana da halin hakan baidai da niyar dagawa nan din ne kawai. Ai dole kice haka tunda bake bace akaiwa hakan kuma ai aure zakuyi indai a tauye mutum ne kowa ai zaije gidan mijin ya gani takecewa salima. Shiko habu suna barin gidan ya hau maria da fada don me zata tsaya taki shiga mota karshe ya gama fadanshi ya kira dan uwansa yana fada mashi sun bar gidan zasu koma sabon gidansu lokacin. Murmushi J din yayi yana fadin Habu baka jin magana meyasa ka zabi fushin mama a kanka tunda tace bata yarda ba ai saika saurara har lokacin da zata amince din da hakan gare mu. J nifa ban iya daukan wanan abunda kake dauka a rayuwanka idan ba badin gidan nan nayi ba za a samu rigiman da sai Allah zai iya maganinsa don raina ya gama baci da yadda mama takewa iyalina kasani. Ko yanzu ai laifin maria din ta gani which means kaga da ita dai take adawa badani danta dana ce zan bar gidan ba irin wanan ne zakuce nayi hakkuri in bar yar mutane a gidan nan ? Maria tana da zurfin cikin tsiya da ace Rahamace zata iya zama dasu din hakana amma maria zurfin cikinta yayi yawa wallahi. Duk abin nan maria bata san gidan ba tunda bai taba kaita tagani ba saida suka shiga karamin get din gidan da hasken wutane ko ina a gidan tarara ta bude ido tana kallon mamaki. A ranta take tambayan kanta yaushe har yayi wanan gina haka bata sani ba bata da labari a bakinsa ? Bin ko ina take da kallon yadda gidan ya tsaru dan maidaidaici dashi komai na more rayuwan zamani ansa harda filin tsakar gida da wajen aje mota ba abinda ya kara burgeta irin hasken da gidan yake dashi wadattace. Saida suka shiga ciki ta kara tsunkewa da lamarin yadda komai ansaka ashe ya jima yana shirinsa ba tare da kowa ya sani ba ke nan . Bayan sun natsune tayo min text tana fada min sun tashi a family house gasu sabon gidansu yanzu haka zaune. Ina falo zaune da iya ina cin abinci sakonta ya shigo min na bude lokaci guda nake hamdalla suka kalloni nace iya wai yaya Habu ya tare sabon gidansa yau din nan. Habu fa kikace ta tambaya cikin mamaki nace yanzu maria ta aiko min da sako hakan yasa na daga waya na kirata . A cikin yare nake mata murna tare da tambayan ya haka ya faru tace kedai bari kawai Allah ya rufa min asiri yau Ramaah . Zagi da mugun fata nasha shi nidake a wajen mama na katseta ina fadin ga iya na mikawa iya wayan ta dauka tana fadin maria kun tashifa naji ance ? Tace wallahi iya ina zaune dazun da yamma yace min na shirya kayan mu ya kwasa saida ya dawo yake fada min nafito mu tafi. Akwai magana ashe Habu yakai dakare ya shamaci kowa dayin haka idan ya fada yasan ba barinsa zasuyi ba aiya kyauta daya fito mata ta hakan yanzu ai kowa zai gane gaskiyan abin ku dai kara hakkuri ku zauna lafiya da mazajen ku. Shiya karbi wayan yana fadin tsohuwa me kike fada ina nan shigowa da safe ai bamu da nisa daku da safe zanshigo in baki labarin komai. Ja,iri bakajin taro duk tangwanka da mukayi saida ka nuna halinka na gagare ka gudu kabar uwarka can ? Dariya yayi yace dolene iya matukar ana son zaman lafiya tunda Allah bai hana muna abinda zamu kula da rayuwan mu ba akan me za mu tauye kanmu haka. Sundan jima suna wayan wanan yasa ban samu wani zance da maria din ba don dare yayi lokacin da tunanen abinda ta fada na kwana a raina. Gaskiyane idan akace mutum yayi hakkuri wani lokacin hakkuri ba cutarwa bane ga bawa yinsane keda wahala. Da ace ban biyewa Saiba nabi zugin ziciyana ba da duk hakan bai faru ata sanadina ba tunda ashe dama ya habu yana da niyar tashi gidan lokacin. Amma yanzu nasan danice mama dubu zatayi kuka nice sanadin komai da har haka ya faru danta yabar gidan a sanadiyar abinda ya faru a part dinshi damu. Sam ba za a gano gaskiya ba nice dai laifin zai koma kaina zata kara tsanata nida yar uwata fiya da wanda take muna a baya. Don haka zan koyi hakkurin nan da kowa ke fasin muyi hakkurin saidai nasan hakan yana da wuya ace na iya gaskiya akan cin fuskan da saiba ke kokarin yi min a kullum. Washegari duk da ina son shiga school amma na daure banyi sammako ba don zuwa gidansu Maria din da mukeson yi. Shi yaya habu din yazo misalin karfe tara ya daukemu nida iya don habiba ta wuce ita tunda safe iya kuma a can zan barta gidan awajensu. Gida yakai gida Allah yasa da nisan kwana akaiga wanda yafi hakan gaba iya ke fadi na amsa da amin muka shiga ko ina yana nuna muna nan nabar iya na fito ya ibrahim yazo ya daukeni zuwa school. Muna hanya yake fada min yayanshi yace ya kamata na koyi mota idan ya dawo zai koya min donshi zai fara aiki dasu zaman garin a yanzu zaiyi wuya a gareshi. Dan murmushi nayi ina fasin kyaleshi ya ibrahim kullum haka yake fada amma ya kasa tsayawa ya koya min din ya zata ko ba zan iya bane. Na cirewa kaina damuwan dana so sakawa zuciyana kan mama tunda kome nayi dai ba haske zanyi a wajenta ba tunda ta nuna bata kaunana da danta. Ni kuma gani a yanzu son danta ya kamani ta yadda nake jinshi a wani bangaren na zuciyana dadin abindai ba a waje daya muke rayuwa ba balle in shiga takuranta. Koma waje dayane tunda ba zamanta nakeyi ba zan kauda kaina ga duk wani cin fuskan da suke min a yanzu din kan mijina. Miji daine Allah ya nufi aure a tsakanin mu dashi ba soyayya mukayi ba amma fahinta da kulawa yasa muna kaunar junan mu. Don haka rabamu a yanzu ganganci a wajen mama don nasan hakan zai haifar da abinda yafi na yaya habu a tsakaninsu. Sai dare iya ta dawo koshi da kwantancen da nayiwa Habiba ne taje gidan ta dawo da iyan don yaya habu din ya fita tun safe ya shiga kano. Nazata mama zatazo gidan a ranan sai gashi har dare banganta ba kuma bata kira waya ba don haka nima na watsar da zancen komai a raina. Anyi haka da kamar sati kwatsam ina hanyar school naga yaya Habu ya kira layina na dauka da mamakin dalilin kiran nawa lokacin na dauki wayan. Muryanshi ba dadi yake fadin Rahama kina school ne na amsa da ehh yaya amma gani hanya dawowa na jira yaya ibrahim ban gansa ba na biyo yar kura. To kizo nan teaching hospital ki samemu idan kin shigo muna dakin maza ki kirani zan fito abinda ya fada ke nan ya kashe wayan. Innalillahi na dinga maimaitawa a bakina tare da tunane barkatai a lokaci guda ina fadi a gigice asibiti kuma wake can asibitin kuma yanzu ? Gabana ya fadi don tunowa da yaya J da nayi rabon da muyi waya dashi kwana ukku ke nan kuma kona kira wayansa baya shiga na dauka baya wajen service ne. Mai keke nayiwa magana ya wuce dani cikin asibitin tunda dama daga school nake muka doshi hanyar shiga asibitin gabana sai faduwa yake min.