Sashe 24
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda yake dan adam bai gani bai tofa nasa ruwan a cikin lamarin da bai shafeshi ba shike faruwa yanzu akan Jafar . Wanda yasan jafar yasan mutumne daya taso da kwazon nema saidai ganin rufin asirin da ubangiji yai masa lokaci guda yasa mutane nata tofa albarkacin bakinsu akan cigaban daya samu inda a yanzu ya gyara gidansu da suke zaune a cikinsa don haihuwan matansa yaiwa kowa part dinta amma falo na tsakiya babba haka bangaren Abubakar da zancen Aurenshi yanzu kowa ya san da yana neman aure a Cameroon . Don har manya su kawu sun shiga zancen zuwan farko baffa yake amincewa da zancen saida suka biyu ta Alh can abuja ya fito masu ta bayan gida a dan Nageria ya hadasu da hakimin garinsu shiya aika masu da sammaci aka nemosu har can inda suke zama akan human right tayi karan baffa din. Tsoro da gudun wahala yasa baffa cewa ya yafe yaran su koma nan kauyen su gidan hardonsu don zaman kaka yake ga yaran. Yace su zauna anan tunda shi baida iko dasu dama taimakonsu yakeyi ai tunda naggen da ubansu yabari a yanzu sun zama nasa tunda shekaru ya kora shike kula dasu. Hardo yaso yayi magana amma sai su Abubakar sukace ya kyaleshi daha baya za,ayi wanan zancen yanzu zancen yarane da uwarsu su samu freedom ayanzu akeyi. Abubakar bai tsaya dogon nema ba irin na barna lokaci a dade da budurwa ana shan soyayya daga shiga rayuwansa ya fito da zancen aure. Inda mama Dubu ta kama mashi tana kuma tayashi da addua da shawara wanda a yanzu kowa yasan da zancen bafulatanan ruggace yake son ya aura. Inda wasu ke ganin ya rago kamarshi dan boko dan gaye mai jin lokacinsa zai buge ga auren yar daji jahila mara boko wace bata waye ba ? Sun manta kida Jahilace haka Allah ya tsara idan itace matar da zai aure din ba (makawa ) inkiyan kauyen zee makawa) sai ya aureta. Allah yayi za ai abin a gabar da dan uwansa ke cikin tashen Naira Allah da yardansa yadda aka saka watan auren lokaci yayi akasha buki. Bukina mai kama da dunkula irun ta fulani ba wani shagali aure kawai aka daura aka dunkulo amarya sai yan rakiya da hardo yabayar mutum biyu sai kanwata da zatazo zama da ita don ta samu wani a kusa da ita cikin garin da bata san kowa ba . Hardo ya roka kuma anyarda mai da hakan gidan su Abubakar din mama tace dama tana da niyar hakan a zuciyarta don ta samu na gida a kusa da ita. A bangaren matan yaya jafar kuma sai dariya sukewa Abubakar a fakaice tunda Saiba dake fadin duk bakin ransa da jiji dakai a bafulatan daji ya kare ashe. Ga mata birjit a gari amma ruwan ido ya kaishi daji auro bafulatana saidai basu fadi a gabanshi saidai a bayanshi basu kadai ke wanan zancen ba harda matan gidansu gidan mahaifinshi. Suma sunata sakin irin zancen nan da fadin magana akan fulani abindai kamar yadda aka saba tsegumi akan ko wani irin aure wanan ma a tofa iya tofawa da za a iya. Mutum dai bai isa ya hana abunda Allah ya nufa ga bawa ba saidai gajin hakkuri namu na yan adam yakansa mu daukanwa kanmu zunubi a cikin rashin sani. Ita kanta maria bata taba zato ko tsamani haka zata samu gidan Abubakar din ba don ya nuna mata shi baida komai a lokacin nemasa da ita. Sai gashi hadaden gidan dataga an kawota ciki ya tsinka mata zuciya ta kara godewa Allah daya duba mairaicinsu ya fitar da ita daga kuncin bautan da sukeyiwa baffa. Sai addiua take wanan auren ya zamo mai dorewa a gareta don baffa yai mata baki da cewa indai auren kado ne taje ya bata shekara tasan baffa mugune na bugawa a jarida. Don ko yan uwansu kaf fulani tsoronsa sukeyi abu dayane ke razana baffa shine hukuma baison abinda ya dangantashi da hukuma. Don bai kaunan ya cire nagge daya balle fiye da dayan a cikin garkenshi ko yaushe a cikin lissafin garensa yake a tsakar dare bai barci nan zaita sintiri yana kidayan shanun dake garken sa. Yana kuma surukullensa a ciki yanawa mutane aiken shirin daya saba wanan tunane data shigane yasa har bataji sallaman su saiba ba da suka shigo ganin amarya da safe. Sai da yar uwarta ke fada mata a cikin hausa anty Yanda ana maki sallama fa ta zabura tana fadin wa ,alaikis sallam. Kallon juna sukayi suna fadin tubarkallah amaryan ke nan ta fito tana masu sannu da zuwa sai yar budurwan dake tare dasune da ba zata gime mata sosai ba take fadin. Anty maria wanan matan Yaya J ne ana suke gidan suma ina kin gane yaya J babban yayan mu na dakin mu sune matansa. Cikin fara,a da yar kunya ta sake dago kai tana masu sannu da zuwa tare da gaidasu tana dan kare fuskanta don kallon kurullah da suke mata. Ba zakace ita din bafulatan daji bane yadda suke fada don dinkin da anty fadila tayo mata daga Abuja sune jikinta a lokacin dinkin dakosu basu saka irinsa ba dogon rigace da yaji duwatsu kamar sarka ya danne a jikinta sai dogon gashin kanta daya sha gyara an daureshi a waje daya yana kyalli a jikinta. Mikewa tayi tana fadin bari tazo taji saiba ta juya harshe a cikin turanci tana fadin muje mana me zamu tsaya yi kuma ta juya tana fadin excuse me please a cikin sallon turancin dake bakinta. Kallon juna sukayi tun lokacin suka fara mamakin anya bafulatan dajice wanan kuwa suke tambayan kansu cikin zuciyarsu. Bana fada maku ba babu inda tai kama da yar daji yadda kuke fada yaya Habu fa duniyane dama nasan za a rina kallon kowa yakeyi kar a gidan nan. Leda ta kawo masu shake da kayan buki ta mikawa Sare data santa tun jiya tasan kanwarsu Abubakar dintane ita. Ke wanan kuwa anya yar dajice wayewanta yayi yawa ko fuskanta kagani kasan wanan ba yar kauye bace. Ai ba wayewa ko kauyanci akajawa a aure ba hali ya kasance tana da halin kwarai shine zaman lafiya ga ko Asmau ta fada. A harzuke ta juyo tana fadin to me kike nufi da zancen ki da bani wanan amsan a yanzu Asmau nifa irin zancen nan naki na gugar zana kin san shike hadani dake Asmau. Nan fada yaso ya fara a tsakaninsu Sare ce ta dakatar dasu da take fadin wanan ai saiku nuna mata irin zaman da kukeyi a nan itama ta fara. Jin hakan yasa Asmau tayi gaba ta barsu a baya son ita dai bataga abin laifi a cikin zancenta ba kawai dai Saiban ce kamar a jirace take da ita lokacin. Fitowan Ramah daga wajensu mama dubu yasa su duk binta da kallo suna mamakin yaran don wanan koba a fada ba kanwar wanan amaryam Abubakar dince da suka fito wajenta. Ya Allah wa yan nan diya akwai halitta dole yaya Habu ya rude a kansu ji wanan karamar don Allah zakice itace ta halicci kanta wajen kyau. A can wajensu mama dubu baki yan kawo amarya suka sauka don iya tace ba mai zama a wajensu a bata masu part din don akwai dakuna a wajenta shine aka gyara masu daki guda suka sauka a ciki. Babu wani laifi a nan din don ina aka saka ake faman yi dasu tun jiya da suka iso garin abincine iri iri kafin su bude wanan wanan ya iso sun rasa wani zasu taba a ciki. Karasawa rama tayi cikin dakin tana fadin a cikin fulanci anty Yanda baffa yace ki fito kiyo hakan ne ya basu dariya ita da kanwar nata lokaci guda suka zauna suna hiran baffa Buga da shu,umancin daya nuna masu a baya. Allah ne ya kwatomu Ramah don babu da amanan baffa Abban mu baici amananshi ba a rayuwansa amma ya azabantar damu haka a gidansa. Kinga matan gidan nan da suka fita yanzu matan yayan Abubakar ne sune abokan zamana a gidan nan saidai na fahinci kamar akwai zaman lafiya a tsakaninsu don suna fita nan suka soma fada. Tsoro nake ji Ramaah zama da irin matan nan akwai fitina da barazana irinsu ba zasu barka ka huta a rayuwanka ba da ace ba gida daya muke a zaune dasu ba hakan yana da sauki. Babu ruwanki dasu tunda ba a bangare daya kuke zaune ba suyi harkansu a can muyi namu a nan dani dake. Murmushi tayi tana bin kanwar nata da kallo tasan Ramaah da iya fadin zance kalma daya zata fada ya wadatar da abokin zancen ta. Kwana biyu yan rakiya sukayi suka juya bayan nasiha da kuma jan kunne da sukaiwa yaran nasu da sanadin aure ya rabosu dasu zuwa nan yanzu. A dan zaman da sukayine suka har sun fahinci wasu abubuwan dake faruwa a gidan wanda suke son natsuwa da gyara a kansu donshi suka tsawatawa ita Yanda din. Sun tafi a ranan kuma Yanda ta fara girki a gidan bisa umurnin mama data bata baki data dora abincin darewa mijinta. Hakan ya bata daman zagewa ta dora girki tare da amfani da sanadaran da sukasa gidan gaba daya ya dauki kamshin dake tashi a girkin. Tuwon shimkafane da ya tuku yayi laushi kamar ba shimkafa aka sarrafa ba ga danko ga leda fara data kwashe a ciki daga nan suka kara mayar da hankali ga miyan da suka dora wanda kowa ke son ya dandana yaji dadinsa. Miyan bindin saniyace ta dora sai miyan yauki na agwano da dan karkashi kadan yaji daddawa da kayan kamshi a gargajiye. Tayi hakanne don hiran da sukaji iya nayi cewa mama ta huta da tambayan tuwo yau maciyi tuwo yakai ga matar da zata tuka masa tuwo yadda yake so yaci sai ya koshi. Sun kammala an zuba waje uku suka shige yin wanka don itace kusan karshen shiga wanka a lokacin. A falon ya J Saiba ce ta fito rugume da yarta tana fadin yau kamshin meke tashi hakane a gidan nan ? Asmau dake zaune ta dago tana fadin nima tun dazun nake jin kamshin nan yana shigo