Sashe 292
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda na dawo gidana ba zance hankalina ya kwanta ba don abubuwan da suka faru a lokacin nasan gidan aure wani jami,ane babba na daukan darasin ya mace. Don ba lalai bane kiyi dacen gidan miji mai kama da naku gidan da kika baro dole akwai banbancin ra,ayi dana tafiyar da rayuwa duk da yadda muke yan daji ra,ayin iyayyen dana saba zama dasu ya fita daban dana nan da yanzu nake rayuwa. Abinda ya faru babban darasine a kaina dama ke da nake ba labari yayi da kaddara ta sameki yar uwa fauwala lamarinki ga ubangiji ki bar komai gareshi yana sane zai maki gata da fitar dake cikin kuncin da kike yar uwa. Kwarai kuwa nasa da saiba kadai zan samu matsala wace ke ikirarin cewa dan cikina a lokacin shege ne don ta hanyar haramun na haifeshi. Don haka nake dari darin zuwan baby duniya sai gashi duk abinda suka kitsa zasuyi mi na tozarci ya koma kansu yadda basu zataba ma don gashi sanadin hakan gadara da isa da izza yaja mata saki kan dan karamin abu. Ita kuma mama ta shiga tozarci duk a wanan ranan duk da mutane sunsan komai amma ita uwace ba a fito fili anyi mata zunde da nune yadda aka wuni yiwa saiba shi ba a ranan. Don kuwa sa ido da hana ruwa ido da kaskancin da suka kulla zasuyi yazo ya kare a kansu karshe su suka fada a wanan ramin na tozarcin da aka shirya yi min nida maman tudu da akace itace ke goya min baya take iza jafar yake kara haukacewa don ba itace ta haifeshi ba take hakan don koma bayansa. Na yarda nice dai ba,a kauna da Jafar don matsayina ko kimata baikai na zamo matarshi ba don ko Yanda duk da nasan mama bata wani kaunanta cin fuskan da ake min yanzu ita ba ai mata irinsa ba. Duk ina wanan tunanen ne a dakina kwance bayan zuwan salima gidan mu da kwana biyu da yin suna tazo take labarta muna zancen saratu. Saratu dai ba dadi ashe zaman gidan don tunda taje ake fitina da ita mutanen gidan sun hade mata kai ga miji ashe ba wani maishi ba dan karyane kawai yana amfani da kyan da Allah yayi mai yana tara mata. Ance uwargidansa kamar tafi kardinsa don shine saratun bata samu yadda take so ba a gidan don taso tayi iya shegen datakeyi a gida na nuna daukan kai. Ita kuma uwargida tace ai bata fisu ba aurosu akayi aurenta akayi don haka aiki daidai da kowa zatayishi a gidan tunda ba funsu tayi ba. Taso nuna batayi miji kuma yabi bayan iyayyensa da matashi ya fara juya mata baya shine wai washegarin dawowan mu ta bugo waya tana kuka cewa ita tagaji wallahi bata iya wanan auren ? Don a rana mutum baida huta ko yaushe cikin aiki yake yana aikin wahala ita da bata da da amma tana bautan diya da wahala akan yayan wasu . Hankalin mama ya tashi sosai tana rarashin saratu din akan ta zauna zataga yan uwanta ta fada masu halinda ake ciki kada ta dawo tayi hakkuri ta zauna dai har ta jisu. Gashi kuma tun ranan sunan Amir da wanan fitinan ya faru yaya J bai zaunu a gida ba take fadin kamar akwai wani abu da yakeyi wanda yasa gaba a yanzu don sai dare yake shigowa gidan. Maman tudu tace me kuwa yasa a gaba kila don yarinyar nan da dubu taki barin ta fita yake hakan ai rabu da namiji idan ta tsani mace garama ke mace ki tsaneshi da sauki akan namiji ya tsaneki salima Allah dai ya kyauta abune bai faduwa kawai amma dubu tana bukatan addua sosai. Bandashi yarinya na dakinta kice sai ta koma gabanku anyi suna kinga komai yanzu da taje din riban mai hakan ya haifar don Allah ? A rayuwa na tsani sa ido da hassada ga bawa don duk ma hassada bai taba cigaba kullum a baya yake bai taba ganin daidai a rayuwanshi. Salima tace tun ranan da na fito mama ke fada min wai can Rahama zata dawo ayi suna nake tambayan saboda me tace saboda ita ta haifi danta ba zata yarda azo nan a juya mata shiba. Duk abinda za ayi azo gabanta ayishi nace a,a mama ki barsu don Allah ta dura min zagi yasa kikaga na kama bakina ban kara magana ba. Tun a lokacin nasan duk shirin Nusaibace hakan ita ta zauna da saratu suka shiryawa mama hakan ta hau gashi a karshe yadda ta kaya ai. Yanzu dai mama tace ba inda zata shi kuma yaya ko kallo bata isheshi ba tunda ya sake mama tace aita zauna zaman dubu a gidan tunda tace ba inda zata ko ? Wanan hiran tasune ya tsaya min a rai yanzu ke nan Saratu tana can cikin wani hali amma mama take kokarin ganin ni saita sakani a matsala kota halin kaka a idon duniya. Haka da take min nakayi tunanen in bar mata danta kawai in tafi amma kuma ina yi tunane shi jafar din a kullum hanyar kyautata min yake bida a tsakanin mu sai in ji wani iri a raina don banda laifin da zan fada ince yayi min a yanzu. A cikin jegon na fara yanke shawaran da anty salma taban na fara sana,a kada in zauna zaman housewife in neme abinyi ko a gidane tunda ta fahinci rayuwan mazan mu rayuwan mazan hausawane a kulle mace a gida ana juya ta kawai sai kin nema a miji. Zannuwan gado ta ban shawara na dinga sarawo masu kananan kudi don haka na zauna na lissafa yan kudin dake hannuna naga sun kai dari biyar a lokacin. Donshi na tura mata a saro min zannuwan gadon a turo min dasu duk da ba wani shiga mutane nakeyi ba hakan zai min wuya amma anty Nafisa tace min akwai matar da zata hadani da ita indan an kawo min. Sai bayan dana bada kudin daya shigo nake fada mai abinda nake son yi yace min nayi tunane kuwa nida ba fita nakeyi ba ina zan saida su ? Dana fada mai da ban tura kudin ba sai ya bayar a kasuwa a dinga juya min irin na Salima nace a,a nafison in juya abina da kaina don gudun zargin mahaifiyarshi da abokan zamana. Sati daya da bada kudin sako ya iso min wanda naji dadin hakan tun daga can anyi packed dinsu an saka a leda an mana kudin ko wani a jikinsa. Washegari Anty Nafisa tazo ta kwasa ta tafi dasu bansan ya akayi ba salima taje tagani sai gashi ta zabi har kwara biyar a ciki tazo tana min labari wai ta gida tabiyo taga Nafisa na sayar dasu ta kwaso. Sunyib kyau don yadinsu masu laushine sosai suna da quality ni kaina na zabawa yaya guda biyu a ciki na bata kudinsu. Anan take bamu labarin cewa Saiba tana nan taki tafiya wai saki biyune tsakaninsu da yaya don haka ba zata tafi ba nayi magana dashi yace hakane amma zamanta bada miyau bakinsa ba zaima dauke Asmau daga gidanne kwanan nan. Ina zasu koma na tambaya sai tace ke ki barsu kawai ba haka ya habu yayi a lokacin ba sai kawai gani mukayi suna shirin tashi suka bar gidan. Kai ranan naga tashin hankali wajen mama kamar zatayi hauka har gobe tana fadin hakan idan zance ya tashi take fada balle ace yau yaya j shima ya bar gidan nan ai kila mama sai ta kusa bugawa. Kinsan me Rahama nace a,a anty wallahi ni abin mama yana ban mamaki yau idan ance meye laifin ku dasu yaya ba zatace ga aunihin abinda akai mata. Shiyasa nake ganin laifin saratu don harda saratu cikin mayar da mama hakan itace mai zuwa ta fada mata karya da gaskiya kan mutum yanzu ai gata can tana girban abinda tayi amma mama bata son a fadi hakan. A nan na fahinci saratu tana cikin wani hali a gidan aurenta haka kuma mama na kokrin boye hakan saidai salima din ban sani ba koni kadai take fadawa zancen oho ? A nan takai magariba bayan munyi sallah ta nufi gida mama tana ta fada da ita akan tayi dare haka da subar barin dare nayi masu a waje. Nayi mamakin rashin shigowanshi ranan har goma na dare wai gashi tun safe daya shigo bai dawo ba hakan ba dabu,ansa bane sau ukku yake ziyartan mu a rana idan yana gari. Ashe a ranan suka kwashe ana can ana rikici a gidan don yana komawa yaje da mota yacewa Asmau ta fitar da duk a binda zata dauka a gidan. Ya wuce wurin mama ya sameta tare da iya suna magana kan saratu nan ya shigo ya gaidasu yake fadin to mama yau nake son Asmau ta koma wancan gidam dana gina guda. Cikin mamaki mama din ta dago tana fadin gida wani gida yace aina jima ina gina sa an gama komai dama can kusa da habune da yazid wajen kamar unguwa dayane dai zance. Jafar ni kake fadawa ka gina gida zaka dauki matarka daga gudan nan zuwa can kan dan zancen da akayi ya wuce kai yana a ranka ashe har yanzu ? Wani zance kuma ni ai nagama wanan maganan a bamgarena dama ina da niyar hakan kudine da bandashi lokacin ban gama saka wasu abubuwa ba yanzu kuma na saka shine zasu tare a ciki. To ban yarda ba ba inda zaku idan kaga Habu yayi na kyaleshi kai ba zan kyaleka ba Jafar don baku isa kuce zaku raba gida dani ba matukar ina raye. Kamar ya mama nan din fa karki manta gidan gadon mune namu dukka da yan uwana can ko nawane dana ginasa da kudina don iyalina . Kwarai kuwa shi muke fata hakan Allah ya kara arziki da rayuwa mai amfani yasa afi hakan kowa na fatan hakan a rayuwansa da zuri,ansa baki da hujan cewa ba zai daga daga nan ba yanzu dubu. Duk yadda akeson biyayya dan nan jafaru yayi maki shi a rayuwansa don haka ban son in ji ko in gani cewa kin kara tofa mashi kalman baki yarda