Sashe 33
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
(Ikon Allah )abinda malamin ya fada ke nan ya dago kai ya kalli kawu dauda da iya da suke zaune gabanshi cikin damuwa tare da son sanin ainihin abinda ya kawosu. Ga mamakin kawu dauda dake sauraren malamin zancen Yanda ce ya kawosu saiga malam ya fara wasu zantutuka na daban da bai shafi ita Yanda din ba sai yayan mama dubu. Yana faman fadin umm,umm subbahanallahi Allah ya kyauta ya dago kai yana ajiyan zuciya yace wanene fari dogo haka matashi a gida ? Su biyune guda yafi guda haske a cikinsu dan tsayi kawu dauda ya kallo iya kafin ya mayar da kallonshi kan malamin yana fadin mun ganesu yayan mune saidai don Allah malam idan akwai wani matsalane a game dasu abari mu gama na wanan yariyar a yanzu kafin a furta nata take mutumin ya fahinci me kawu yake nufi. Sai malam yayi murmushi yana fadin gaskiyane ita wanan da tana tabuwa malam dauda aida tuni an gama da ita ko saidai labari to saukin abin dai yaran nada tsarin ubangiji a jikinsu. Saidai ayi ta raunana cikin da take samu amma ba ita ba wanan hayaki zan bata da rubutu yanzun nan ta shaye insha Allahu ba abinda zai faru da cikin jikinta data sauka lafiya kai malam dauda kazo nan ka sheda min daga wanan karon za a daina bibiyanta amma turene da akai mata na iska da suke son lalata cikin jikinta din . Zata dage kuma sosai da addu,a shi kansa wanda keyi yasan yaran suna da wani baiwa da Allah yai masu wana da wuya a iya cin masu da sauri barma yar uwarta da tafita karfin tsari a tare da ita. Ya dai bata abinda zai bata sun aje zance kawu zai dawo karban abu yake fadin ai matsala da sakaci yakai ga hakan amma yaran nan da nake zance uwarsu ce da laidin komai don akwai wata mace dataso taimaka mata amma ya kasance uwar bata mayar da hankalinta ba. Sam kawu baison zancen a gaban yar uwata hakan yasa ya kau da maganan akan zaije ya dawo sukai mashi godiya tare da dan bashi abinda zai bashi na goron sadakan taimaka masu din suka bar wajenshi suna godiya. Hankali iya yai matukar tashi amma kawu ya kwantar mata da hankalin hakan ba komai bane ai suka bar zancen. Kawu bai kaunar komai za a fada kada wata mace daga cikin sarakansu taji zai kasance abin sirine da iyasune zasu iya jin matsalan a tsakaninsu yasa ya hana zancen gaban yar uwata. Shima a tsorace yake da abinda malamin ya nuna don baisan abinda ke shirin faruwa da diyan yar uwar tashi ba lokacin da sunanansu ya fito a zancen malamin . Don shine bai tsaya yayi bin kwakwafi ba a lokacin kan zancen don Yanda dake kusa ga yanda din bata cikin kwanciyan hankali kan matsalanta. A gida kuma bin kwakwafin tambaya suke min don saiba taga fitan su iya gidan da yayata saidai bata san inda suka dosa ba da ita hakan yasa tazo tana fadawa kishiryarta . Wace yau ayi fari gobe zama duk da shirin bai wuce na yan mintuna ayi fada a shirya don dokan da mijin nasu ya saka akan duk wace ke ja mashi matsala zai rabu da ita a cikinsu. Asmau ce take bugun cikina taji inda suka tafi na nuna mata bansan fitansu ba ai ina daki suka fita hakan yasa ta kyaleni da zancen. Sun kai wani lokaci kafinsu dawo gidan ina part din antyna na kara gyara ko ina dan shigowan da akayi din yasa na kara tsabtace wajen tas. Har cikin falon iya ta rakota tana mata sannu kafin iya din dan matsa kusa ds ita tana fadin ki kula kada kowa a gidan nan yasan halin da kike ciki ki kumayi yadda aka ce kiyi din . Ta amsa a galabaice ta samu waje ta kwanta abincima sai da kyat na samu taci saboda damuwa da take ciki a lokacin hakan dana ganta cikine ya dan daga min hankali sosai ban dai nuna a fili ba. A cikin dare mijinta ya shigo gari daga misalin karfe tara saura muna falo zaune ya shigo horn din motarshi taji take fadin yaya Habu. Na dago na dan kalleta a inda take zaune naci gaba da kallo tunda batayi magana ba nayi mamaki sosai daya tabbata shi dine ya dawo a lokacin. Banyi shishigin tashi ba na dai gaidashi da dawowa na nufi kitchen na dauko mai goran ruwa kodana kawo na sameshi ya rankwafo saman kanta yana magana da ita na aje ruwan da sauri tare da nufar daki. Don kada insha hakkinsu a yadda na gansu din ba don niba a lokacin tugimar matarshi zaiyi a jikinshi kayana duba na dauki abinda zan dauka zuwa part din iya. Na fito na barsu nan a falon bayan fitana kuwa abinda danake zargi ya faru don rugumeta yayi a jikinshi yana fadin Maria hope ba abinda ya taba lafiyan ki dai yanzu ? Tayi na rai narai da idanu tana fadin ba komai ya Habu saidai yawan mafalkin da nakeyi shine ke daga min hankali sosai. Kara jawota yayi zuwa jikinsa yana shafan kanta yake fadin ba abinda zai faru dake wanan karon da yardan ubangiji Allah ya fishi yafi mugun nufinsa akanmu insha Allah. Nan ya zauna tana masa bayanin irin yadda take wahala sosai a cikin mafalkin haka kuma yayi ta kwantar mata da hankali yana karfafa mata zuciya akan ta yarda ba wani mahaluki da ya isa yaiwa dan uwansa mutum wani abu sai Allah. Su anty Sare na samu a falon suna kallo na shigo sai lokacin suka sanda dan uwansu ya dawo gari ban tsaya falo kallo ba na nufi daki don in gyara inda zan kwanta a lokacin. Nasan ba lalai bane in samu dakin yadda nake so Allah yayimu fulani da tsanda da tsabta don akwaimu da tsabta sosai nima din haka na kasance a cikinsu lokacin. Banji motsin mama ba har na kammala gyaran dakin na sake fitowa falo na zauna ina tambayan mama nan suke fada min aita koma gida tunda akai magariba. Mun dan taba kallo muna hira jefi jefi dasu a wajen nakoma daki na kwanta tare da tunanen halinda yar uwata take ciki a lokacin. Don nasan baffa mugun mutumne baida imani ko kadan a rayuwansa tunda kuma tace tana ganinsa ko wani lokaci a mafalkinta dole akwai wani mugun abinda yake aiwatarwa akan mu lokacin. Amma yar uwata mai tayi mashi da mahaifinmu yake fadanshi tsakaninsu don me zai taba min yar uwa kuma a yanzu wani irin tsanar baffa naji kasan zuciyana irin da ban taba masa ba sai a ranan duk ko da wahalan da mugasha a hannunsa ? Haka barci ya daukeni washegari dana falka banyi sanyin jiki ba wajen gyara ko ina dana saba gyara kafin na shiga nayi wanka na gyara jikina. A yanzu ban damu da yin abin karyawa ba a part din iya kamar yadda nakan yiwa iya idan muna mu kadai daga sai ita don ganin masu part din sun dawo hutu a lokacin. Don haka yasa na koma na kwanta bayan nayi wanka na gyara jikina tsab sai barci ya dan daukeni ban sani ba. A cikin dan barcin dana dan samu nayi wani irin mugun mafalki daya firgitani na tashi ina zufa ina bin dakin da kallo. Muryan iya na tsinkayo a falon naji tana fada da yan matanta kan basu fito sunyi mata abin karyawa ba har rana wanan lokacin haka ? Mikewa nayi a cikin sanyi jiki na fito falon na samesu fada tsohuwar keyi sosai dasu suna zaune suna kallo an rasa mai motsawa a cikinsu ta shiga kitchen din a lokacin. Nima ban shiga ba na samu waje na zauna ina gaida ita da kwana ta amsa take fadin . Ke dai yar nan kedai sannu da kokari kinfi min mutanen banzan nan da basu san ciwon kansu ba gidan nan suna koyi da halin wa yan can shashashun matan dan uwan nasu. Inda mace zatayi kwance cikin lalaci da kiuya ba zata zage ta tsinanawa kanta komai a rayuwanta wai a haka kuma mace zatace aure takeyi don lalaci ? Da kece iyanzu nakai ga abin karyawa a gidan nan amma su wai yanzune zasu dora min abin kari da rana tsaka kiri kiri haka ? Sallaman ya Habu ya katseta take fadin kai kuma yaushe kadawo garin tana mashi kallon mamaki ? Saida ya karasa shigowa falon yace tun jiya da dare mana nasan kinyi barci a lokacin yasa ban shigo nan ba ai. Antyna ce tashigo a bayanshi tana dauke da kayan karya kumallo data hada a hannunta tana gaida iya da kwana sai binta takeyi da kallo cikin mamaki. Yar nan har kinyi karfin halin tashi shiga madafi yin giki a yadda kike din nan hankalina ya daga matuka da zancen yarinyar nan jiya . Abin tausayi wai ace kuma yar nan mai hankali har akwai wanda ta tarewa wani abu a duniyan nan yake binta da sheri. Wai, nakane yau yake kokarin illanta ka haka don bakin ciki an daiyi mutum banza a wajen nan wallahi wanan mutumin da zan gashi saina tsine masa albarka. Kina zaginsa mugune fa iya kada yazo ya waiwaiyeki habu ya fada yana zama a saman kujera sai naji iyan tace meye hadinshi dani kuma da zai dawo kaina ? Wayace ki zageshi yanzu yana iya jinki ai koba haka aka fada maku ba a can inda kuka je jiyan ba zaginsa nayi ba habu halinsa na fada ai yanzu . Muryan Yanda cetace Iya ki kyaleshi ga abin karyawa na kawo maki ta fada tana aje bowl din data riko a hannunta ta samu waje itama ta zauna a kusa dashi ta fara gaida iya dake fadin Allah yai maki albarka yar nan kinji. Yanzu nake sababi da yaran nan suna daki sun mimike kafa wai sai yanzu zasu dora muna girki ta fada tana kiciniyar budan kwanan gabanta din. Nan Sare ta taso tana dariya ta karbe kwanon tana budewa iya ta soma fadin kingani ba, ki duba ba kunyane dasu ba ai, ace mace na kwance wai tana barcin