← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 306

Sashe 97

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

illah Rahama dai kanwar matarka da matana sukai min zargin kulata wanan abinda sukai min kamar sun ingizanine ko haske min hanya akan wanan yarinyar Rahama a yanzu. Saida Habu yaja wani uban burki a saman titi Allah ya taimaka hanya ba wasu motoci a cikinsa sosai ya juyo yana kallon dan uwan nasa yace. Rahama dai Ramaah ta wajen maria matana kake nufi J ? J din ya marairaice murya tamkar zaiyi kuka cikin yanayi na kyarmar murya yace Habu mafita nake so da zancen nan don har nakai kaina gareta garesu da ita yayan nasu nacan . Ban samu matasala ga yar uwar tasu ba saiga Rahama din ita ta nuna kaduwa da jin zancen saidai nasan yar uwar nata tasa yanzu ta soma saurarena. Shiru Habu yayi yana wasu tunane da baisan iya adadinsu ba lokaci guda kafin yaji muryan dan uwan nasa yana fadin . Habu ina son auren yarinyar nan a yanzu don irin halaiyansu nagari dako wani namiji ke fatan samun mace ta kasance a hakan. Bani barci da dadi akan tunanen yarinyar nan a yanzu duk abinda nake wanan abin ne yanzu a gabana na rasa ta ina zan fara nasan akwai cakwakiya sosai da rigimar auren nan idan hakan ya tabbata din saidai na matana mai saukine tunda ba waje daya zan ajiyesu ba don gudun fitina kuma ga yarta a gidan hakan ba zai yuyu garesu ba. Ina matukar jirkita akan zancen nan Habu rasa Rahama a wajena tankar rasa rayuwatane habu ban kara furgicewa ba saida naji ita wanan yar uwar tasu tana fadin. Koda Rahama zata dawo zaria school ba dai a gidan mu ba saidai ta zauna hostel ko kuma ta kama mata campus ta zauna ina hakan zai yuyu gamu habu ? Habu ya nisa yana fadin ni a ganina wanan ba matsala bane babba haka J matsala dai dayace shine ka samu yardan yarinyar wanda nasan da wuya gaskiya hakan ya faru a cikin sauki. Duk da haka idan matanka sunji wanan zancen yaya zasu dauki hasashen su akanka na baya zaka iya jure kalubalin da zai biyo bayan zancen. Idan har zaka iya ninasan hanyar da zamu bullowa ita Rahaman da yarta dama wani da zai iya kawo cikas a cikin zancen mafita dayace shine muje muga hardo bakin mu a laikum in yaso daga baya sai a baiyana wa kowa yasani. Amma kuma ni dai shawaran da zan baka shine idan kasan matanka zasu kawowa yarinyar nan nakasu a rayuwan ku gara tun wuri kayi hakkuri ka cire wanan zancen Rahaman a cikin zuciyar ka don na fahinci har da gaiya kake son aikata hakan. A harzuke ya soma fadin wai Habu su suka ajeni koni na ajesu dubaiya nakeyi nake zaune dasu kasani amma kuma yanzu kana fada min in hakkura da Rahama ? Kai Habu ya girgiza yana fadin J kayi hakkuri ba wai bani sonka da Rahama bane nima na dade inawa wani dan uwana samun wanan yarinyar Rahama saboda halaiyanta dayayi min. Amma yanzu kai daka bullo da wanan zancen akwai babban aiki nake hango maka agabanka don fitina kake son janyowa kanka a ganin ka ita Rahama yanzu bata da wanda take sone ? Haka kuma matan ka kana ganin zasu kyaleku ku zauna lafiyane wanan abubuwan nake hango maka J don tasu mama mai saukine matukar muka samu kan kawu ai an gama zancen. Wayan J din yayi kara amma ya kasa dagawa har saida Habu din yace dashi wayarkafa na ringing J ka daga mana. Sannan yakai hannunshi ya duba Saiba ce ta kirashi bai san lokacin daya saki wani dogon tsuki ba yana fadin wai meye kike kirana haka ba yanzu na fito gidan ba ? Ya katse kiran cike da jin haushinta da takaici don yasan sauraren wayan ba zai haddasa mashi komai ba a karshe sai bacin rai . Yanzu duk fadin duniya inba Rahamace zata kirashi ba baijin zai iya daukan wayan wani a lokacin fahintar halin da yake ciki da habu yayi yasa ya dan sasauta murya ga dan uwan nasa yana fadin. Kayi hakkuri J ka bani nan zuwa safe zanyi tunanen abinyi amma kabi komai a sannu kada a gane kana cikin wanan damuwa komai zaizo da sauki in sha Allahu. Nidai yanzu abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka saboda kasan ba lafiyane dakai ba sosai gaka kuma ka rikitowa kanka wani aure yanzu. Sai lokacin yayi dan murmushi yacewa kanin nasa ai wanan yasa nake son nuna masu iyakar kyamata da sukayi akan ciwon nawa don kowan su saita gane kuren yin hakan.
Chapter 97 · 0% Book details