Sashe 246
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
an sakata a rest don haka kuje kawai Allah ya hada kowa da rabonsa. Don wanan abin ba zamu mayar da yarunya wajen da babu kwanciyan hankali ba alhalin mun sani kuma mun gani wani abu yazo ya sameta. Saiga iya a kasa tana hada daddy da Allah yaiwa Allah yayi hakkuri ya bar Rahama ta koma dakinta kodon mijinta tayi alkawarin ba abinda zai faru insha Allahu kuma. Tausayin iyan yasa daddy din ya sauko yake fadin tsohuwa kuje insha Allahu zata dawo amma ba yanzu ba saita kara samun lafiya za a dawo da ita. Yazid da aka hana magana sai lokacin ya samu furta don Allah Alh ayi hakkuri kodon halin da bawam Allah nan yake ciki da cewan Jafar. Sai daddy ya gyara zama ya soma fadin ai nace zata koma amma ba yau ba sai ta kara lafiya saidai ina son ku sani matukar uwarku gata a zaune bata daina wanan halin ba ba macen da zatayi marmarin zama da iyalinta. Mama din ta kallonshi yace yes ni ban tsoron kowa da kuka ganni nan ya fara karanto masu mukaman daya rike da yake aiki inda ya dora da fadin . Yau a duniya mutum ya fito filli kiri kiri ya nuna nasa yake so dan kowa ba da bane a wajensa sai duniya ta barshi da dabaranshi a hakan . Banga inda zaka dauko dan mutane ba ko danka ya dauko ka nuna naka kake kauna a fili duk mutum mai wanan halin abin tsorone gaskiya. Anso dai ayi ba dadi a wajen don daddy ya tsaya ya fadawa mama gaskiya shida iya sai gata tana kuka tana fasin a gafarce ta ita ba a a fahince ta bane yakawo hakan. An dai basu hakkuri akan su koma daddy yayi masu alkawarin shi zai kawoni har zaria da kanshi idan na kara jin dama don kada abi hanya dani a jijigani wani abu ya faru da cikin jikina. Saida zasu tafine daddy yasa na fito wai inzo mu gaisa dasu din banso fitowan ba amma don gudun bacin ran iyayyena din dole na fito muka gaisa dasu. Najin dadin yadda daddy ya nuna masu akan mu yana iya sharia da kowa koda duk abinda ya mallaka zasu kare saidai su kare din . Amma matukar aka kara muzanta ni ko yar uwata a gidan yadda akayi a baya zai dauki shari,a dakoma waye ba ruwansa da kankantan mutum ko tsufanshi. Sukayi sallama damu haka suka tafi donni tun bayan gaisuwa ban kara kallon inda yake ba asalima haushinsa naji ya karu min a zuciyana don yadda sukazo din sukayi. Ban kuma rakasu ba na koma dakin ummah na kwanta ina hadiyan bakin rai daya tokare min zuciya tare da tunanen mama ita wata irin macece wai ? Anya kuwa ko Jafar din tana kaunarsa kuwa a zuciyarta gashi ya rame ya zama baki sai kasumba daya tara a fuskanshi dama nice maiyi mashi aski yanzu ko nasan bai yardane kowa yayi mashi. Suma a mota da fada sosai aka dawo gidan inda suka taru sukaciwa saratu mutunci don kuwa suna barin gidan mu saiga wayan Nusaiba tana tambayan ance sun shigo kaduna din zasu karaso gidansune suga mimi yarta ? Nam yazid dake jin abinda ya fada ya soma fada yana kantamawa saratu zagi yana fadin idan batayi hankali ba saita rasa mijin aure tunda ta zama iblis ? Uwar taso fada wai don me zai kirata da iblis iya ta tare ta kara fadin aita zama iblis don inda rahama yake bata a wajen sai hadin hasumi shine nata. Nadai gane baku kaunar yaron nan da alheri daga ke har uwarki saratu duk yadda akayi kinkai uwarku wajen malam da kuke bi dake da yarinyat nan da har bata ganin laifinki a yanzu ? Nikan iya ku kasheni ku huta yafi wanan aibantanin da kukeyi haka ai bata karasa ba shi mara lafiyan ya juyo yakai mata mari tas sai da kowa na motan ya kadu. Cikin irin maganarsa na saurin harshe ya soma magana yana fadin kar kiga ina kyaleki ki zata ban iya daukan matakine a kanki tausayin ku nake ji ba komai ba ? Iskancin nan ya isheni daga yau ki kama kanki dani da duk wani abu daya shafeni don kinga ina kyaleki zaisa har ki wuce gona da iri ? To muzu ba dani dake a gidan nan kuma na baki nan da wata daya ki kawo miji kona aurar dake ga duk wanda naga dama a zaria. Haba dai kuyi mata fatan samun mijin mana sai mugun fata kukewa yar uwarku haka ko yaya take dai ai yar uwarce sai kuyi hakkuri da halinta. Kema bakin tsiya yayi maki yawa meya kaiki fadawa Nusaiba mun shigo tunda kinsan ba wajenta muka zo ba don kawai ki tayar da wani hasumin wa kanki kome ? Kaji ko J mama bata ga laifin yarinyar nan ba sai namu shike nan ai ranan da duk kika iskancin ki a sai kin iskamci ki tsaya dashi iyasu da saba yiwa amma bani ba don ban iya daukan wanan halin banzan naki. Na rasa yadda akayi yarinyar nan ta koma haka jafar yake fada cikin takaici sai iya ta amsa mashi da fadin dama hakan take ai halintane a hakan . Wanan yasa mama tayi shiru har suka kai zaria bata kara magana ba mota na tsayawa suka shiga ciki nan tahau fada da yar nata tana fadin . Da wanan halin kike tunanen zakije aure Saratu na dauka abinda zaki barine ashe abin naki bana bari bane ke a gurinki. Bansan baki da wayau ba sai yau din nan ki rasa wanda zakiwa tsiya sai Jafar duk irin kokarin da yaron nan yakeyi daku sakaiyar da zaki mashi ke nan ? Kallon mamaki saratu ke mata tace kwarai indai kinayi don Nusaibace tun wuri ki daina don bani kaunar yarinyar nan mai bakin wayau tsiya ta dawo gidan nan . Taje abinda sukaci a gareshi ya isa hakana naji da wanan dake son tsaya min a makoshi don na kula Jafar baisan ciwon kanshi ba. A zatonsu naje bikone saboda Allah na daije kawai don kada ya halaka a yanzu tunda ya kwallafa ransa ga yarinyar nan don shi kawai naje kadunan nan . Dukkansu biyu kallon mamaki sukewa uwar har dai Salima dake kallon ikon Allah yanzune fa suka bar kaduna tare da alkawari akan dawowan Rahama dakinta amma mama take fadin wanan magana kuma ? Tsam ta mike zuwa daki cike da tsoron halin mahaifiyarsu din tabbas wanan hali na mana yasa bata shiri da saurab kishiyoyinta ashe ? Da wanan tunanen ta wuni ta kwana sai washegari data je gaida yayan nasu da kwana take basu labari shida iya. Iyace ma ta hau fada yana zaune baice komai yayi shiru yana tunane a zuciyarshi kafin ya umurci ita salima din data gyara masu part din don yasan idan ba ita ya saka aikin ba Asmau ba zata taba tunanen zuwa ta gyara masu ba dama kuma yana jin haushin halin ko in kula da take nunawa a kanshi. Shidai abinda ya dauka hakan wani jerabawa a rayuwansa Allah ya kawo mai dan ya kara imani da hukuncin ubangiji ga bawa. A yanzu yasan masoyanshi da kuma masu nuna hassada akanshi dan zaman jinyar nan da yayi gida bai fita ko ina.