Sashe 196
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
mu kowa ya rude. Nan tashiga rabtabo masu labarin yadda abin ya faru zaune habu yakai a gefen dan uwan nasa ya zuba mashi idanu yana kare masa kallo a cikin tausayi. Can ya juyo yace ko dan kokon daya dan karba yanzu ya daina sha ke nan ko mama tace ina ai tunda sukai mai alluran nan ya samu barci hakan nan daka ganshi yake tun dazun din. Saida kyat suka samu suka bar asibitin don mama data matsa masu suje gida su huta tunda muna nan asibitin mu hakan yasa suka tafi. Har iya dake son hutu a lokaci tabisu zuwa gidan yaya habu duk a nan suka kwana ranan sai kawu da suka sauke gidanshi har lokacin ya kasa furta komai a garesu. Tun da asuba na jona ruwa na gyarawa yaya jikinsa da taimakon mama na samu na tsabtace masa jikinsa muka saka mashi wasu kananan kaya sai ya fito dan few dashi don rama da yanayin jikinsa yayi. Nabi dakin na gyara na fesa kamshi da yaya Auwal ya sayo ayi amfani dashi na gyaro har ban dakin koda suka dawo daga sallah sun samu har nagama komai a lokacin. Lokacin kuma yaya habu yayi sammakon zuwa asibitin shima don duba dan uwan nasa daya kwana dashi a rai. Ásmau ce data kira layina tana tambayan ya mai jikin nake fada mata idan zasuzo suzo da koko don Allah ban jira me zatace ba na kashe wayan. Sai wajajen takwas suka shigo asibitin da yaransu mun gaisa lafiya suna muna ya mai jiki mama ta amsa da sauki nan rake fadin . Tunda kunzo sai ku kamawa yar uwarku taje ta huta ke Asmau saiki zauna dashi zuwa karfe biyu sai ita nusaiba ta karbe ki zuwa yamma don ita yar nan ta huta don batayi barci ba a jiyan. In yaso zuwa dare saita karbe ki atakaice dai mama ta raba muna wanan taggadaman a tsakanin mu ke nan kuma hakan ya zaunu saidai ina jin hakan na fara haraman zuwa gida don ina son dama gyara jikina robona da wanka tun da zan fito gida zuwa wajensu a jiyan . Ina saka hijjab nake jin suna zancen bashi kokon dasu da mama dubu na gama kimtsawa na dauko jakata ina fadin zan tafi sai anjima bisa ga umurnin mama duk suka juyo suna kallona zaki gidane naji mama dubu ta fada . Ehb zanje na dan watsa ruwane mama na bata amsa take fadin ibrahim yana kusane ya kaiki zan fita ko zan samu wanda zai saukeni na bata amsa sai naji tace min to indai babu kowa saiki dawo habu ya saukeki ko ? Nayi masu sai anjima na fita daga dakin cikin sanyin jiki cike da mamakin sanyi mama a kaina lokacin ina fita na hadu dasu anty Barakha da yan uwanta nan muka tsaya muka gaisa suna tambayan jikin dan uwan nasu. Muryan Asmau naji tana kirana hakan yasa muka isa tare dasu take fadin mama ke magana dani nashiga take fadin kada ki tafi ai ki tsaya abashi kunun nan don kece kikafi sanin yadda yake kamawa idan anbashi. Hakan yasa dole na kwabe hijjab dina na muka soma kamashi don mu dagoshi dole saida na dan hau gadon na rungumeshi duk sun zuba min ido na soma da kiran sunanshi a hankali ina mashi sannu. A lokacin su yaya habu suka karaso dakin suma sai yayi kamar ya bude idonsa ya kalleni nace ka daure ka dansha koko koda kadan ne don Allah yaya ? Wani irin ajiyan zuciya ya sauke lokaci guda duk hankalin kowa ya dawo kanshi da sauri ya habu ya karaso yana tambaya hankali tashe da yaya dai ? Murya a kare nake fadin ajiyan zuciya ya sauke na kallo Asmau da jikinta ke rawa nake fadin ta bani kunun ta miko min na kara fadin ka karba yaya don Allah kashe kada ka zauna da yunwa haka tunda bai shiga ta roban da ake baka din. Bskin nasa naga yana bukatan a kara wankewa hakan yasa na nuna mata ruwa ta miko min na diba a hannu ina dan wanke bakin nasa . Ya kara sauke ajiyan zuciya a hankali nake fadin ya taune halshesa ashe jiya har yaji ciwo a bakin muka gama na bashi kunun ya karba sosai kamar cibi biyar aka samu yasha ya habu yace in barshi hakana zan saukeshi a jikina yayi alaman a,a . Ita Asmau ke fadin kamar ya girgiza kai fa nace hakane ya habune yace ki zauna dashi haka yake nufi. Nan anty barakha ke fadin Allah sarki yasan itace ta rikeshi ke nan ya habu yace ya sani sosai idan tayi mai magana ai yana nuna ya ganeta. Ikon Allah ai dole inda zuciyarsa take ke nan dole ya shedata ai mama dubu ke fada hakan ta matso tana fadin sannu jafar ya jikin kai ya kara dagawa a cijin karfin hali. Suka shiga gaidashi daya baya duk daba amsawa yakeyi ba sun dai gaidashi din ne kawai irin na al,ada da akeyiwa mara lafiya. Yaron Asmaune aka shigo dashi yana rikici suyi lalshi yaki shiru mama ke fadin ta fita waje dashi. Hakan yasa na karbeshi daga inda nake zaune daidai fuskan uban na nuna mashi shi ina fadin ga baba yana gaida kai yaya sai kawai ya bude idanunsan tarr akan yaron . Da karfi saare ke fadin wallahi yaya ya bude idonsa hakan yasa duk suka matso garesa a cikin farin ciki sai kuma ya mayar da idonsa ya lumshe a hankali. A hankali ya habu ya leko yana fadin J ya jikin sai ya kara bude idon ya sauke ga dan uwan nasa ya sake sake lumshesu ya bude ya kafawa Habu din ido na wani dan lokaci. Likitocine suka shigo dakin suka sameshi a hakan sunji dadi sosai a yadda suka sameshi hakan yasa aka rage a dakin harni a lokacin na samu na fice na nufi gida. Ban dawo asibitin ba har yamma don saida nayi barci bayan nayi wanka na kwanta na samu barci sosai sam na manta da zancena da dan uwana Dage saida kira ya shigo min a wayata yana fada min gashi ya shigo zaria hakan yasa na tashi da sauri ina salati. Kwatace yayi min inda yake maigadi na tura yazo dashi tsamo tsamo don da ganinsa a tsorace yake saida ya hangoni tsaye kofan gidan mu ina dakon dawowansu hankalinsa ya kwanta. Nan falona muka zube na bashi abinci yaci yayi wanka saida akai sallah muka samu kebewa dashi ya soma yi min bayanin abinda yazo dashi din . Haka kuma ya sanar dani cewa sammako zaiyi ya koma washe gari don gida ba a san nan ya nufo ba yazo min da abubuwa masu amfani sosai. Nayi godiya nayi mai alheri iya abinda zan iya wanda yake ganin kamar na tsomashi a aljanna ne tare mukaje asibitin dashi da yaya habu dana kira nayi mai bayanin komai . A saibitin ma ya habu bai boye ba don yace hardon mune ya toroshi ya kawo muna maganin da za ayi amfani dashi ya fadawa yan uwansa haka tare suka koma zai kwana a wajensu dasafe ya sakashi motar farko ya koma gida suma sun mashi alheri ya tafi.