Sashe 79
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yai wanan maganan jiya ni yaran nan na rasa irin haukan kurciyan su yanzuma kawun ku a kansu yake min magana waje. Wai mahaifin ita Asmau ya matsa da zuwa gidansa akan ya ban hakkuri kaga dai rashin su yasa munyi magani a tsanake so nake kowacen su takoyi hankali a gidansu. Duk da ita wanan Nusaiban da alama ba hankalin zata koya ba tunda ta saba zuwa gida ta zauna shiyasa wanan karon nake son su dauki lokaci a gidajen nasu har iyayyensu su fahnci rayuwan da sukeyi a dakunan su. Mata ku zauna baku iya komai ba sai kazantar tsiya da sherin duniya kala kala bayan wanan basu iya komai ba sai daukan kai su wata tsiyace. Aiko yanzu sun horu mama ki barsu su dawo hakana don Allah abinda takaici shi bai gujesu ba don halinsa sai sune suke kyamatarshi habu ? A gaban mu wanan yarinyar ta nuna hakan fa haba dai don kwatoshi cikin bari a horasu tunda ba tsoron su akeji ba mana abin yayi yawa shege da hauka. Idan dai zasu dawone su dawo kawai duniyace ai zata gyarasu gaba ina kawu ya tafine habu ke wanan maganan shi jafar yana kurum baice uffan ba a lokacin tunda aka dauko zancen matan nashi. Ya tafi kaidai wai yana da daurin aure bayan sallah kuma muka tsaya muna magana bai fargaba har lokacin ya dan shige. Ok mama wai nace ba don Allah wani tambaya nake son nayi maki kuma kada ki damu tambayane kawai jin hakan yasa ta zauna tana kallon dan nata. Nace mama ko a baya kin taba yawon neman haihuwa haka ko amsan wani magani kan haihuwa a wajen wani ? Magani kuma gaskiya kona taba ba zan iya tuna hakan ba wani abune akace game da hakan eeh to ance gaskiya. Don yadda aka fada min kamar kin karbo maganin bisa ga sharadin cewa idan bukata ya biya zaki koma ki kai masu wani abu . Sai kuma da bukatan ya biya mama baki koma ba wanan yana daga cikin abubuwan dake damun J a yanzu in ma ba ai hankali gaba dayan mu wanan matsalan zai iya shafan mu. A ina kaji wanan zancen Habu tana tambayan dan nata cikin zuba mata idanuwanta don jin amsan da zai bata don zancen ya taba mata zuciya sosai. A baya kan lokacin da bata haihu ba anyi neman magani duk wanda ya kawo kuma tana gwadawa ita yanzu yaya zata iya tuna hakan. Mama ina son ki tuno kafin kiji yadda zancen nan yake san nan kuma zancen maganin da J yake sha a yanzu duk za a dainasu akwai wani wanda zan ba Rahama ta kawo maki yana a mota shi kadai za,a dinga amfani dashi har kwana biyu a gani. Ko me kikace mama shiru tayi kafin tace a sanyayye a gwada din aiba a ki ta magani ba sai an gwada akansan na kwarai inji ba haushe . Yanzun ai lalube mukeyi a cikin duhu Allah yasa a dace din ya bashi lafiya shida sauran al,umman Annabi baki daya suka amsa da amin. Sai aiwa kawu bayani ya dan tsagaita zuwa wajen karbe karben da yakeyi din yanzu a gwada wanan din sosai a gani ta amsa da insha Allahu. Sun dan jima kafin ya mike zuwa part dinshi a gajiye anan ya sameni dauke da Abbati dakinsa ya shige matarshi ta bishi hakan yasa na fito zuwa part dinsu iya don nasan anty nafisa tana part din. Ina shiga na samu Saare tazo nasan kuma a nan zatayi weekend tunda alhamisce Allah ya gani duk da gidansune banyi maraba da ganinta ba. Haka na gaida ita a darare ina kokarin zama take fadin kai dan fillo miko minshi nan kafin na kaiga mika mata iya ta karbe da fadin dan fillo kuma kun basune ? Ai dole mu basu dan nema baisan kowa ba sai uwayenshi bakin kiuyane dashi iya baya yarda da kowa a gidan nan. Ki daina fadan hakan ran mahaifisa ba zaiyi dadi ba ranan dayajiki da aida gidan ubansa aka san asalinsa ba fannin uwa ba. Ai fulanin basu kadai bane ko ita Asmau asalinta ai fulanine saidai sun zama yan garin nan yanzu don ko yare basu iya ba gidan su. Nafisace ta fito daga daki tana fadin Ramaah mamace kadai a wurin yaya wallahi ban sani ba anty nafisa tunda na fito ban koma part din ba ina shiyan mu. Saida ta mede baki take fadin yanzu kune kuma masu kula da ya j din duniya tai maku dadi matanshi sun tafi kun maye gurbi. Haba dai Saare wanan wani irin maganan banzane zaki fada haka idan munyiwa yaya hidima laifine yaya mukaiwa ko kan mu ? Shike nan don matansa ba zamu kulashi ba ko suna nan ai dole mu kulashi tunda lalura ya kama na hakan kin taba gani mutum ya guji dan uwansa ? Zaki mayar min da zance wani abin kuma niba nufina ke nan ba gani nayi dai bai dace ba inda baku kulawa din ai mama ba zata iya ita kadai ba ? Oky hakan laifine ko to ba don wani abu mukayi ba don Allah da mama dashi ya J din mukayi inma kina zaton wani abune. Ta mike tana fadin nifa Nafisa ba wani abu nake nufi ba ato shiyasa ban damu da zuwa ba son gudun hakan da kayi magana ayi kokarin juya maka zance zuwa wani daban. Kallon mamaki nake mata nasan dai sabodani take wanan zancen a kofa suka hadu da mama dake shigowa tana fadin hayaniyar me nake ji haka wai ? Banda wanan figagiyar mai zubin yan ruwa kinsan ita bata rabo da abin fitina na rasa yadda yar nan ta koyi tsegumi a gidan nan. Meya faru Nafisa tace ba komai mama ba zaki fada ba kina tsoronta ne tace wai cewa tayi munji dadi an sallami matan yaya mun maye gurbinsu da mu barki ke kadai da kika koresu kiyi jinyar yaya din . Allah sarki ke kan kinyi hasara wallahi baki san takaici ba sun maye din sai ki dawo dasu dakunan su insan kin cika yar nema mara hankali. Daga zuwanki kina son ki haddasa min bacin rai abinda yaran nan keyi min ko biyansu nakeyi zan iya basu hakkinsune jinya wasane halan ? Kedai baki san harara ba wallahi ashe kema kyamar dan uwan naki kikeyi yasa kina cikin garin nan kikaki lekowa ki gaidashi ? Haba mama kyamarshi kuma to na sani tunda zancen ku daya dasu baki wanka ki bushe kina wajensu kina koyon iya shege don bandashi banga abinda suka karaki dashi ba. Ke Rahama yayanku Habu ya baki maganin da za a dinga bashi din ? Jin ta ambaci sunana yasa na dago ina fadin a,a mama bai bani ba bari dai in koma in karbo mashi na sakai na fita na barsu zaune.