← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 306

Sashe 64

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da zanyi amfani dasu da zan iya ba wani taimako akan hakan saidai ba wanan a gabana don na dauki hakan da tsubu shirka sukeyi a wajena. Tashi nayi na kasa komawa barcin ina faman tunanen wa kuma wani bala,in zai sama inda nakai raina shine yanda don itace a asibiti don haka hankalina ya kara tashi sosai da mafalkin. Bayan nayi sallah la,asar na fito falo anty salma na dakinta barci tayi tun bayan dawowanta sauke daddyn Imran ta kwanta. Sai wajajen biyar ta fito daga daki har lokacin ina zaune a falonsu ni daya da wayata a hannu ina game. Muryan ta naji a kaina tana fadin tsiyan abuja ke nan fa ranan sallah ba wani gurin da mutum zai fita yawo saidai kaje park da sauran wajajen yara saiko gidan yan uwa da abokai. Na dago ina gaida ita da fitowa wanan dabi,an gidansune muka gada ko wanka mutum ya fito sai angaidashi da fitowa . Zama tayi tana fadin wai Ramaah kinsan wanan rigar taki mai bala,in tsadane kuwa kwanaki nayi ta neman irinsa in saya ban samu ba sai gashi na gani a jikin ki. Murmushi nayi ina fadin yaya J ya saya min da zamu zo saboda ban samu dinkin sallah naba aiko wallahi yayi maki kokari sosai rigan nan yakai seventy fa Ramah gaskiya guy din yayi kokari. Anan muke dan hiransu jefi jefi har nake bata labarin yadda zaman mu yake gidan da yadda matansa suka tasamu a gaba da nuna kiyayya har yadda sukai mun kafin inzo Abuja da dalilin dayasa mijin nasu ya saya min kayan. Mesuke nufi dayin hakan nace sunce kamar ni zai sayawa lace mai tsada hakana matsayina baikai hakan ba. Don ya saya masu abu su da kannesa zai saya min ai rikona akeyi a gidan in gaskiyane Habu ya saya min mana ai dalilishi nazo gidan. Kaji jahilai zasu batawa mata tsarin diyanta idan mijin maria ya saya maki ai zaiga kamar ya shiga gaban dan uwansane tunda kansu a hade yake yadda na fahinta. Kin mun daidai wallahi laifin uwarsu bagani a nan don itace ya kamata ta fara magana ba wanan salima din ba gashi ai yanzu ya saya maki wanda kila yafi wanda suke fada a kanshi din. Kishine fa kada ki dada kishine irin namu na mata kawai suka dora akanku ku fita zancen su kawai yan iskane. Ni dai abu daya zan fada shine kada ki yarda ai maki aure bakije gaba kin kara karatu ba idan maria batayi ba ke zaki kara gaba din insha Allahu tunda kun fito wajen wanab mugun mutumin. Ai wasu yan yankin kune suka fadawa daddy lokacin yafita zancen ku don mutumin nan na iya halakshi da asiri wana yasa daddu ya bar zancen ya barku can zube a hannunsa amma idan bashi ba daddy yaso dawo daku hannunsa nan. To an fada mashi shine ya kama kurwan baba fillo shiya kasheshi don haka daddy ya barku ko ba mutuwa wahala ai baida dadi Ramaah. Mun dauko hiran baffa sosai a wajen har nake tunane kodai wanan hiran nasa da zamuyine yasa nayi mafalkinsa a ranan. A Zaria kuma abu ya koma tashin hankali sosai don ya J yana cikin wani hali ba barci ba zama sai kugi da yakeyi anyi mai allura amma a banza. Dole kawu yaje wani waje dama yan zaria badaga nan ba shirya suke da unguwa na malamai don akwai kasuwa a irin hakan . A wanan wajen ya karbo wani hayaki akai mashi shine har ya samu ya dan ci abinci da barci yayi ya kafin hankali ya kwanta amma a asibitin suka kwana dashi. Washe garima jikin da sauki saidai wajajen rana kuma lamarin ya kara dawowa sosai sai kugi yake yana kiran wai shi kansa zai mutu babban mutum yana raki yana kiran sunan Allah. Hankalin mutane ya kara tashi sosai kawu dauda ya shiga nan ya fada can kowa da kalan nasa aka samu ya samu dan sauki kawu yace a basu sallama tunda ba abin asibiti bane. Lokacin hankalin mama Dubu ya tashi sosai a wanan dawowan gidan dole Nusaiba ta dawo dakin ta ba shiri saidai basu ga maciji da Salima da take ganin itace ta sanar da dan uwanta fadan su har ya dauki mataki haka akanta. Salima bata damu ba itama shere Saiban tayi tunda ta fahinci me take nufi a kanta nan gida sukai ta magani har ya dan samu sauki ya daina buga kan nasa da yakeyi yana fadin ciwo kamar a cire mashi kan ya huta yake ji. Sai daga baya bayan munyi waya da salima data kirani take ban labarin irin halin da suke ciki na tashin hankali kan jafar din inda ta kare zancen da fadin amma yanzu abinda sauki yauma ya fita sallah jumma,a ya dawo. Sai banji dadin hakan ba ko banza ance ka damu da wanda ya damu dakai akace sai naji na damu da jin hakan hankalina ya koma Zaria din tunda a karkashinsu nake kuma ni banganin laifinsu akaina.
Chapter 64 · 0% Book details