← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 270 OF 306

Sashe 270

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ajin da muke nema wajen miji din. Dakinsa ya shiga ya fito ina kallo bai taba abin karyawan dana aje mashi ba alama ya nuna shima ya hau dani lokacin ban kumayi dabaran yi mashi magana daya karya ba . Har ya fito saida yakai kofa ya juyo yana fadin shi zai shiga kaduna wani abu wani zafinsa na kara ji a zuciyana a yan kwanakin nan ya matsawa kaduna din nan sosai yana shiga lokaci lokaci ashe bikon matarshi yake zuwa yi na raya hakan a zuciyana bance dashi komai ba dai har ya fita. Ashe hakan yaci masa rai bai bar zaria ba saida yakai karana wajen maman tudu akan tayi min fada kan halin dana dauko mashi tunda abin bai shafeni ba a cewarshi. Matsalansuce shi da matanshi baiga abin da ya shafoni ciki ba tun nan mama tace dashi ya shafota takan malami tunda in haukan Nusaiba ya tashi kowa hadewa takeyi tayi dashi. Ita dai ta bari tunda bata da matsala da haka sin tana gidanta daban meye nata a ciki sun jima da mama kafin ya fito ya bar gidan zuwa inda zashin . Da rana tsaka saiga mama a gidan nayi mamakin zuwanta don in zasuzo aida safe suke zuwa yaya Auwal daya kawota tace dashi ya tafi idan ta gama zata hawo motan kasuwa ta dawo gida. Tun nan na gane akwai magana kuma gashi ita kadai tazo ba Nafisa dake rakota idan zatazo din na dai tareta yadda na saba na aje mata komai na koma kasa gefe muna gaisawa. A lokacin ta fara yi min maganan daya kawo ta din wajena wai yace baiso ya fadawa iyayyena tunda haka bai taba shiga tsakanin mu ba dashi. Mama ya fada mana sai me ko cikin nan da nake jira in haife yace ba zan haifa a gidan nan ba ina da wajen haihuwanshi ai. Ni dai ba zan shaganta abina ba tunda Allah ya sheda shi yayi min cikin wallahi ban taba zina ba balle kishiya ta kira min zina da aurena. Shiyasan abunda yake tsunta a wajenta har yake ganin a yanzu ya dace ya dawo da ita dakinta tazo taci gaba da aibanta min abinda zan haifa a gidan. Kukane yazo min da nake fadan hakan a lokacin da sauri mama tace tana farashi yadda ta kodu din nan bata farawa ai inane bataje kamun kafa ba don ya maidota dakinta. Anyi na malamai da bokaye baici ba yanzu ta koma na lalama ga yan uwa da abokan arziki har sukaciwo karfinsa ta yarinya yanzu ya yarda. Mama shi ya shafa cikin nan kawai ya tsayar dani gidan nan wallahi da ba zata sameni a gidan nan bama to a nan na sameshi nan zan haifeshi in wuce. Ke yar nan kada ki soma wanan gangancin da kike kokarinyi a yanzu don Allah ki wuce ki bar dan ko yar dawa hannunta ta kama maki ko me ita bagata ta dawo don yarta ba ? Sai kece da baki da mafadi zaki bar naki ki tafi a yadda na amsa kuma nakeyi tasan zan aika don sanin halin mu fulani da karfin hali da tayi. A,a Rahamatu kada ki hakan don Allah kina aon mijin ki yana sonki kada ki yarda fushin zuciya ya rudeki ga banza kan wata can da bata shiryawa aure ba. Sau nawa zan fada maki hakan ne ita fa abinda take nema taga ya samune a tsakanin yau ko wani shirin tayo a kanku nuna mata kinfi karfinta ke. Sai Allah ba boka ba malam kike lamarinki barsu badai dubu ta kafe sai ya dawo da ita a yanzu sukace ba to zai fita a tsakaninsu. Kusa ido kuyi kallo kawai indai dubu ce ita kuma itace kwana nawane za a fara jin tsakaninsu ? Nayi kuka sosai haka na nunawa mama din na hakkura amma itama ta fahinci da sauran zance a zuciyana saida tayi sallah la,asar na rakota zuwa titi nidasu Aminu muka daukar mata drop har gida na biya . Koda ya dawo gidanta ya fara zuwa take mayar mashi da yadda mukayi tace kasan halin fulani malam to kada kace zakaja zancen nan a bangareka don Allah ? Don yarinyar nan ta nuna min cewa haihuwan cikin nan na jikinta ya tsayar da ita tafiyanta zatayi ta barku . Har ya soma fadin ta tafi mana mama halan tare aka haifemu da ba zan iya rabuwa da ita ba ko an fada mata idan ta tafi rayuwana zai bar,,,,,,, Karka soma wallahi don ka yarda yarinyar nan ta subuce maka malam saika dawo ka raina kanka wallahi ana zama da mace don wasu abubuwa nata daga ciki da zan iya fada na farko ga yarinyar nan shine hakarci ko iya wanan kadai ya isheka shiga wani hali idan ta barka a yau din nan. To mama me nayiwa Rahama da zata dauki fushi dani haka in ma fadana da Asmaune takewa ai,bada ita nayi ba don me zata saka kanta a zancen mu ita. Yanzu dai na fadama yarinyar nan kasansu fulani da riko don haka kabi sannu idan ka yarda ta subucema kuma sai kayi nadama wallahi. Duk mutumin da zai zauna dakai tsakani da Allah shine abokin zama ba mutumin dake son ka a fatar baki ba kaidai kasan wanan yarinyar kaduna din komewa halinku zakuyi da ita ko yanzu. Ya dago ya dube mama din tace kwarai kaika yarda da tuban mazurun da tayine a yanzu ai hali zanen dutsene amma mama tayi alkawarin daina duk wani hali nata na baya za a zauna lafiya sosai da ita yanzu . Aifa ni yanzu bance kada ka dawo da matarka ba malam amma kada kayi saki reshe kama ganye a gidan ka tunda uwarka tace ka mayar da ita meye nawa yanzu a cikin hana hakan da zanyi. Da tun farkone wallahi malam zan hanaka ka dawo da yarinyar nan gidanka duk da nasan harkan aurene idan bai mutu ba ba mahalukin daya isa ya raba tsakanin ku yanzu ko mahaufiyarku ta riga da ta ciwo kanka ka yarda da hakan kaga idan na hana a yanzu Allah ba zai barni ba nima tunda uwa nake nima ga wasu yayan. Wa yan nan maganganu na mama tudu sun tsaya mai a zuciya don har sun sakashi wasi wasin a lokacin. Nayi abincin kamar yadda na saba amma a ranan ban aje a falo ba kamar kullum kitchen na barshi na koma daki na kwanta bai shigo gida ba sai bayan isha,i ya biya can gidan yayi masu saida safe. Ina jin shigowanshi amma ban fito ba har ya shiga daki ya dan jima a ciki ya watsa ruwa kafin ya fito ba zance maki yaya ya warke garau ba a yanzu. Har yanzu akwai sauran jin jiki a tare dashi idan ka sanshi a baya ka kalleshi yanzu kasan da sauran ciwo a jikinshi karfin hali yakeyi irin na dan adam mai tafiya da buri a tare dashi. Dakina ya nufo direct ya shigo sai kamshi yakeyi cikin dakewa da sanyin jiki yake fadin kwance ake ne kingani sai yanzu na dawo na biya can gidan nayi masu saida safene. A raina nace ai dole ka kai dare a can tunda an mannaka da bokaya ance mai kishiya bata mutuwar Allah haka zancen gizo bai wuce na koki ba ai. Jin bance komai ba yasa shi fadin banga abincina a falo ba mana ko yau baki iya girkawa bane kuma sai lokacin nayi magana nace. Naga ka daina cine yasa ban aje falo ba amma nayi girki tun dazun ai dan murmushi yayi cikin tsigan neman shiri a tsakanin mu yace kai Rahama kina dai son zance ni banga abin fushi a cikin zancen nan ba ? Nusaiba ce fa ba wata mace zan dauko wace baki sani ba kin riga da kinsan halinta saidai ban san abinda dan gulman naki yazo ya fada maki ba kika hau fushi haka. Wani dan gulma aini ba wawiya bace da wani zaizo ya zugani ni mutuncina da darajan abinda zan haifa na jawa tunda ita dabbama ya fita hankali. Taso kiban abinci don Allah tun safe dana fita ban karya ba har yanzu har ji nake kamar banda lafiya yau a jikina tunda an saba cika min ciki kwana biyu kuma anki kulani ?
Chapter 270 · 0% Book details