← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 306

Sashe 75

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu dai bamuje kaduna ba saisu mama dubune sukai mana kara ita da kishiyanta inna da yanzu itace kamar uwar dakimu gidan saboda tana nuna muna kulawa sosai kodon muna tare da yartane oho ? Koma meye damunzone gidan zata karbe Abbati tana angonta tana ba,a kasancewa itace amarya acikinsu. Wanan yasa muma muke zama a dakinta har dai shakuwa ya shiga tsakaninmu sosai da ita bamu gane ko mama dubu tana son hakan da mukeyi ko bata so ? Har dai yakai ya habu da kansa yakan dauki yaron yakaiwa inna shi don yawan tambayansa da takeyi lokaci lokaci kota niko gari tazo gida tace tazo duba maigidantane ita da iya. A kullum kuma inna tana kan muna nasiha game da zama tare zakice ita din yar uwamuce ta jini donshi shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu da ita harma yayanta. Don haka ta takawa mama wajen rakiyan ummah gidan sabon mijinta akaduna sai gashi sunje sunga abinda basu zata ba a can din. Yanzu tsakanin mu da ummah wayane mu duka kowa na kiranta yaji lafiyanta tana ce muna lafiya kalau wanan ke kwantar muna da hankali. Gaskiyane da wasu mata idan mazansu sun mutu sun barsu da yaya koda iyayyensu suna raye suke fadin gatansu ya fadi gatansu ya tafi wanan zancen ba karya bane don mun gani a kanmu a rayuwan mu. A yadda hardo ke fada muna a yanzu duk shanayen mune wajen baffa shanayen da idan da zamu mallakane zasu taimaka muna harmu taimakawa wanin mu a rayuwa. Sai gashi badon ubangiji ya rufa muna asiri sanadin ya Habu ya auro yar uwata ba da rayuwan mu a bautan baffa da iyalansa zai kare muna. Sannu sannu yau nakai UG 3 da dadi da wuya haka karatun ke zuwa min a daidai yayin da Anty Salima take shirin zuwa bautan kasa a lokacin kuma muka shiga wani tashin hankali sabo dayafi na baya a gidan rikona inda yar uwata take aure. Don ko an samu sakon ya Jafar wanan ciwon kan nasa a yanzu ya dawo inda abin har yafi na farko ga fadan masu fada labari yazowa mama kamar hauka yayi a lokacin. Innalillahi wa inna alaihin raji,un tashin hakan da muka kwana dashi muka tashi dashi kr nan a gidan wanda yasa su kawu dasu yaya habu kwasan jiki zuwa garin da yake. Da alama ba dadi don duk lokacin da wani zai kira a gida aji halinda yake ciki amsa dayane shine jikin dai da saukin musulunci za ace kawai amma ba sauki sai a wajen Allah. Rana daya naga damuwa karara ga iyalinsa ranan da ya Habu ya kira yana fadawa mama cewa da wahalan da Jafar yake ciki mama gara a roka masa Allah kawai saukin mutuwa. Sai mama ta fashe da kuka kuka mai tsanani dole kowa a gidan kukane na tashin hankali ba maiba wani hakkuri a gidan lokacin. Duk muna falon iya gaba dayan mu in banda iyatu dake faman aiyukanta a wajen gidan nan saiba ke fadin mama ko zamu shirya mujene ? Ai yanzu ba zancen zuwa bane tunda gida zasu dawo dashi a gwada a gani abin na asibiti yaki suncesu basu ga ciwon komai a jikinsa ba komai nasa yana lafiya don haka bana asibiti bane abin iya take fadan hakan ga matar nasa. Dawowa dashi din garama da suke can labari kawai mukaji bamu gani ba don ganinsa a irin halin da yake ciki shine babban tashin hankali ga yan uwa da abokan arzikinsu. Kai innalillahi tashin hankali baida kyau don ciwon maimakon aga sauki sai kara sabon sallo na ciwo da yakeyi yau ya taba nan gobe ya canza waje duk a jikin nasa. Idan ya taso yana kugi duk inda mutum yake a gidan yana iya jinsa saboda zafin ciwo a yadda naji har salinta jikinsa ya farayi yana saba irin na macizai. Haka na shirya na bar gidan a cikin damuwa ganin mama yadda take kuka a gaban kawu da iya tana fadin wanan wahalan yai yawa in tafiyane Jafar gara katafi ka huta da wanan wahalan haka. Duk da nake yarinya banji wanan adduan ta mama yai min dadi ba musulumi sauki aka sanshi dashi da nema a wajen ubangiji ba zancen baki ba. Masu fadan hakan bawa yasan abinda zai tar a gurin Allah ne shidai bawa ya nemi sauki koma meye a wajen ubangiji shine mafita. Har nakai school da wanan zancen nake a zuciyana a karo na farko da kusan shekara biyu ke nan da zuwan mu gida ban taba gwada kiran layin Dage ba sai a ranan naji ina son kiran Dage in sanar dashi halinda dan uwar mijin yayata yake ciki don mutumin arzikine sosai ya J komai mutum zai iya masa don ya cetoshi daga wanan uku ban da yake ciki na bautan ubangiji . Gashi ashe sakacin su yasa basu koma can wajen wancan malamin daya taimaka masu ba da farko tunda sukaga sauki suka fita batun koda kawu ya koma yace ba abinda zai iyayi yanzu da ace tun wancan lokacin sun dawo sun karbi abinda yace din da sun bashi goron sa da wata kila hakan bai faru ba a yanzu don an riga da ancin masa ko ciwo yayi nisa wanan zancen tunda kawu ya dawo ya shedawa mama ta fita hankalinta ga baki daya. Cikin ikon Allah ina danna kiran layin ya shiga bai dauka ba har kiran ya katse a kasa nake tafe hakan yasa na kara danna mashi kira a karo na biyu. Sai gashi naji an daga ana faman fadin Alo alo alo murmushin karfin hali nayi ina fadin who is speaking au kafirata ka kirana ashe ? Naji Dage din na fadan hakan na sake sallama don na fahinci zai iya kashe wayan a lokacin ya amsa sallama yana fadin wake magana ? Nace budurwankace ta birni da kaba layin wanka koba dage bane yace kwarai kuwa nine Dage nace to ni aljannace na kirakane muyi soyayya shiru yayi da har yasa na daga wayan na duba koya kashene a lokacin. Sai naji yana fadin Aradu Ramatuce oho yar nema ja,ira sai yau kikaga daman kirata watau ? Ina gwada layinka Dage baya shigane nayi mai karya yace kai kinshan me Ramatu kudin da kika ban ardu kudin albarkane ai watau da wanda kika bani da wanda kika ba inneje na hada suk na sawo muna dan karo mace dana miji Ramatu bakiga yadda suka haifa muna diya ba wallahi kowa sai magana yakeyi nashe wa tsayahu wanan karon zumuncine tsakanina da Ramatu. Dariya na kwashe dashi na katseshi da tambayan mutanen gida har baffa yace kul ardu kun kuru da baku samu baffan nan a gida ba lokashin . Yayi cizon yatsa yashe ai zaku dawo shi za a kawowa shegan taka ita maria harda haihuwa da kado ko ? Gabana ya fadi nasan za a rina dama indai baffa ne da suke kira da magajin tauri duk wani maison maganin tauri yazo yaga baffa ya warke. Dage akwai wani bawan Allah dan uwan mijin maria da akaiwa makaru nan dai na tsaya nayi mai dan bayanin abinda nasani game da ciwon yaya din. Kai amma ke Ramatu a kwaiki da shirme wallahi ina wanan garin dana fara baki shi zaki dinga mashi hayakinsa haka kuma. Ki samo magarya kunne gomasha bakwai kada ki dada daga hakan a samu dutsen tama kinshanshi ko nace a,a amma zan nema yace kwara ukku kacal a saka kasan tukuyan a tafasa a tare saiya dahu sosai a sauke ya huce a diba hannu uku asha sai ayi wanka da sauran . In Allah ya yarda da zakuga sauki zan binciki baffa nayi mai karyan wani nason taimako a waje na bashi dan kudi sai ya fada min wanin. Bari na turo ma kudi a wayan ka ka sayar ka bashi ba sai ka taba naka ba Dage ayi haka kuma Ramatu haba dai ka barshi kawai nayi niyane ai. Wurin mai shago na tafi na bashi kudi ya turawa layinsa lokacin haka ake tura sakon kudi sai gashi ya kirani yana fadin arradu Ramatu kinyi lafiya kun ketare kaidin baffa shima baffa yana fada gaba dayan ku kunfi karfinsa ai. Ya gwada sa,ansa akanku ya kasa cin maku tunma ke yace ke iblishiyace da zaki kai wani lokaci a wajensa da kin kwance masa karfinsa. Haka dai muka rabu dashi yana ta shirmensa na tare abin hawa zuwa gida saidai kuma me a gidan dai badadi don wani tashin hankali na dawo na riska inda mama tayiwa matan jafar kaca kaca a ranan . Wai suna gudunshi suna kyamarshi don haka mama tace sai subar gidan ita zatayi jinyar danta in da rabo in yaji sauki su dawo mashi amma yanzu kan sai sun bar mata gidanta. Tunda babu wace keda hankalin da zata kula dashi iyakarsu su dan shigo suyi shaaaa su fice babu mai zama ta kula dashi a cikinsu. Hakan ya farune da Asmau ta shigo dakin da yarta yana dan cikin hankalinsa ya mikawa yar hannu da tazo wajensa sai uwar taki bari yar taje. Shi jafar din ya dubi matar nasa yana fadin inku kuna kyamana a haka har da yayana zaku hana su rabeni Asmau ? Kawu da mama na zaune lokacin da hakan ya faru mama tace sun ma isa sunce suna kyamar ka jafar ? Yace aigata nan idan akwai wace ke yarda ko gadon nan ta taba haka nake fama idan baku kusa kona kirasu basu zuwa su taimaka min komai zasuyi min a wullakace suke min shi suna gudun su dauki cuta a jikina. Wanan ya harzuka mama ta soma bala,i da tashin hankali har haka ya faru ita saiba sai ta fake da tayi yaji ta kwasa ta nufi kaduna wai mama na yawan takura mata . Ita Asmau bata tafi ba shine mama tace har ita din ta tafi duk mai zaginta ya zageta amma basu zama a gidan. Nima na kula da hakan a lokacin saidai sanin halinsu yasa ban dauki hakan wani abuba tunda haka yake zaune da abinsa. Na rasa yadda zanyi in aiwatar da maganin nan ga yaya j ina zance dasu na samu wanan abin ina part
Chapter 75 · 0% Book details