Sashe 31
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ratsa a gareta sai dai kuma anan saiba gaskiya a dan shigan da nakeyi ita saiba tasha bamban da Asmau din. Don saiba ko bakaga abu ba zata iya cewa dake idan zakici abu kaza akwaishi a kitchen ko kuma idan kun zauna kuna hira ta dauka abin ta mikama shi a gadarance ta juya bambamcin su ke nan. Sakin fuska sai Asmau kyauta kuma Nusaiba amma wajen kazanta gaskiya a ganina kamar suna kwatawa duk da ance wai Nusaiba tafita dama a wanan fammanin. Nasan matan hausa sun camfa mu matan fulani da iya yi da kisisina da makirci wanan kirarine da akewa matan fulani dake auren kado wani lokaci. Wanda a wurin mu abin ba hakana bane na dauka iya kamun kaine da sanin darajan aure wanda ake ganin hakan kamar wani kisisinane nasu sukeyin hakan. Ko a yanzu gidan nan haka suka fara radawa yar uwata don tsananin bin dokan mijinta da kiyayyewa da takeyi. Don duk umurnin da mijinta ya bata bata taba ketareshi tana kuma kafa,kafa da duk abinda ya gargadeta dayi wanan yasa suka saka mata suna zundenta. Don yana da wuyane ka shigo ka sameta a waje ko kaga gilmawanta a haraban gidan idan har ba wajen iya zata shiga ba. Duk shigan da nakeyi wajen su anty Asmau bata hanani saidai ita ta kama kanta kamar yadda mijinta yace kada yaga tana shiga wani rikici yazo ya faru sunanta ya fito a cikon case dinsu. Hakan yasa nima takan ja min kunne a duk lokacin da taga kamar nayi zurfi a cikin sha,aninsi zata taka min burki da jan kunne kada in yarda wani abu ya fito ace nice na fada. Hakan kesa in kara kama kaina dasu saidai a danyi hiran yaransu ko hiran film iyakata dasu ke nan suma din kuma sun fahinci haka a gareni. Hutu muka samu na dogon zango haka yasa muka samu wanan irin zaman da ko yaushe kana gida da sunan hutu saidai a wajena abin ba haka yake ba. Ranan tunda na tashi nayi irin aiyukan dana saba yi a gidan gyaro ko ina na cikin gidan da waje bangaren yayata da kuma bamgaren iya kamar yadda na saba a kullum. Duk da su Anty Sare suna gida a lokacin ban damu da sai sun tashi sunyi ba Allah baisa min kallon irin hakan ba a rayuwata kace baka abu don wani baiyi ba . Wajen yayata na koma don yanzu dasu anty Sare suka dawo hutu tare da ita nake kwana idan mijinta baya gari. Don cikin jikinta dake bata matsala tana yawan zazzabi da amai da sauran laluran masu shigan cikin . Haka kayana har wanan lokacin a wajenta suke sai na amfanina na yau da kullum ne a wajan iya. Kwance na sameta falonta na zauna a wajenta gaidani tayi da aikin yasa na zauna ina dariya nake fadin ina aikin a yanzu Yanda ? Ramaah kinsan abinda ke damuna yanzu ta fada hakan yasa na sake kallonta ina girgiza kaina alaman a,a a gareta. Nisawa tayi tana fadin wallahi baffan mu nake yawan mafalkinshi sosai Ramaah a kwanakin nan yana yawan zo min a cikin mafalkina kamar yana kokarin aikata min wani mugun abune nake gani kinsan baffa mugun mutum ne Ramaah. Baki addu,ane idan zaki kwanta anty tace inayi kuwa sosai Ramaah ai duk dare ya habu sai ya tunana min da addua idan zan kwanta kina jinsa ai wani lokaci. Tunane na shiga yi don sanin da nayiwa baffa mutum ne mai kyashi da hassada kashe mutum a wajensa ba wani abu bane shi da bakinsa zaki yana ikirarin sai yaga bayan mutum idan dan wani abu ya hadashi da wani. Balle mu da akai rabuwan tashin hankali dashi zai iya cewa zai dauki fansa yanzu akan yar uwata din dan abinda ya faru kafin aurenta. Hakan yasa na dago ina fadin anty yanda mu kira hardo mu fada mai yafi abar zancen nan don kinsan hardone kawai maganinsa shi kadai naga baffa yana tsoro a cikin yan uwa. Dan murmushi ta sauke a fuskanta tana fadin Ramaah ban son saka kowa a cikin lamarin nan ni nasan baffa yana wani shiri a kanmu Ramaah ko ince a kaina don ni kadai nasan yadda nake ji tun zuwana gidan nan a wahalce nake kai safe idan na kwanta. Dan dama idan habu yana garin nan nakanji saukin lamarin amma duk da hakan wani lokaci kuma sai nayi wanan mugun mafalkin nasa. Nasan ba zata taba fadawa wani halinda take ciki ba koni din a yanzu data fadawa Allah ne ya matsi bakinta har ta sanar dani din tunda duk dadewan nan bata taba sanar dani komai ba. Saidai na fahinci tana cikin damuwane sosai a lokacin danafi saka ran akan zaman gidan nan ne ko kuma rashin sabo ke damunta tunda nasan bata da matsala acikin lamarin aurenta. Don haka nasan ba zata fadaba ba kuma zatayi komai ba saboda alkunya irin na fulani data gado. Shiru nayi ina nazari kafin na mike na shiga wanka ba tare dana kara mata maganan komai ba abin mamaki kodana fito daga bayin na samu ta dawo cikin dakin ta kwanta da alaman tsoro ko wani abu yana damunta. Bandai yi mata magana ba balle ta fahinci hankalina yayi mugun tashi a lokacin da abinda take ciki din tana kwance har na gama shirina kafin ta mike ta shiga ban daki don kewayawa. Hakan ya bani daman samun abinda nake so na dauki wayanta na dannawa mijinta kira na fice daga dakin yana ganin kiran ya daga wayan yana fadin . Maria ya akayine na amsa daba ita bace yaya nice Ramaah sai naji yace Ramaah lafiya ina yayan taki kuma meya sameta ? Ba komai yaya saidai yana gab da faruwa amma zurfin ciki irin nata ba zata fada ba balle a dauki mataki nan na kora masa abinda ta fada min bai ko bari nakai karshe ba naji yace ina zuwa zan koma kira . Ashe hjynsu mama Dubu ya kira hankali tashe ya fada mata abinda ke faruwa nan itama mahaifiyar nasa hankalinta ya tashi sosai dajin hakan. Bansan ya sukayi ba dai sai ganin hjy din mukayi gidan lokacin da na gama wayan na mayar mata bina tayi da kallo na mika mata wayan take tambaya wana kira nace kawata bata damu ba ta karba kawai ta koma ta kwanta. Nima ganin hakan sai ban fita ba zauna da ita ina janta da hira inda naga ta dan sake muna zaune mukaji sallaman mama tare da iya a part din. Hakan yasa muka fito muna masu sannu da zuwa idon mama dubu yana kan sarakuwar nata cikin tausayi take tambaya da fadin . Maria meke damun kine yaya kike ganin shi a mafalkin naki ido takai gareni na dukar dakaina kasa hakan yasa mama dubu fadin . Aimu ta kyauta muna data kira Habu ta sanar dashi yau wa take dashi garin nan daya kaiki maria yar uwarki kar kiga laifinta irin wanan abin ba a wasa dashi tunda kunsan halin mutumin nan . Bari kawun ku ya karaso yanzu ki shirya kuje da Iya kafin ya iso ki tashi ki shiga ki shirya idan ya karaso sai ku tafi ba magana takeyi ba ita. Saidai ta mike don bin umurnin sarakuwar nata nan iya ta soma magana tana fadin yanzu yar nan duk sabon dake tsakanin mu irin haka ya faru dake gamu a gida daya ki kasa fada min ? Wancan cikin na farko ya zube kin samu wani kuma lalura ya shigeki irin hakan ba zaki fada ba yar nan asan abin yi akai ? Kawu yai sallama suka shigo da anty Sare data rakoshi ina jin suna gaisawa nima na gaidashi na shiga daki wajenta na sameta ta saka hijab saidai ta kasa fitowa falon ta samesu. Juyowa tayi ta kalleni tana fadin yanzu abin nan da kikayi Ramaah kin kyauta ke nan don Allah zaki tayarwa mutanen nan da hankali haka Ramaah wanan yasa ban fadawa kowa halin da nake ciki nake bari a zuciyana. Hawayene ya zubo min lokaci guda na soma fadin Yanda idan ban fada ba ki halaka ina kallo kuma na sani baffa mugune komai zai iya aikatawa akan kuma don ya fadi hakan kuma mun sani. Muryan mamace dake fadin idan kun shirya ku fito mana kuje maria hakan yasamu fitowa falom muka samesu take fadin sai sun dawo iya zancen nan kada ya fita a cikin gidan nan don Allah. Bana son azo a wuya zancen ta wani tsiga kin dai san halin yaran nan matan shiyancan yanzu ne da sunji zancen zai juye zuwa wani daban.