← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 267 OF 306

Sashe 267

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

saika kafa munbari kofan gidan nan kace ina wanan aikin mama ai gaskiya yaya fada salima dake zaube ta fada. Ta mika mata hannu tana mata dakuwa tace Allah mama har an soma gulman ki yanzu a gida kan hakan don Allah mama ki bari hakan baida kyau. Gashi yace Asmau tasan zaiyi hakan ashe kullum mama ke kika tashi shine anci amanan Asmau da yake munafukace ba ? Waya sani ko sayar mashi da kwanan tayi don jakkanci haka kawai zan sake namiji zuwa gidan kishiya tsawon wata da dan kai doluwa kawai na banza. Yarinyar nan badon mutuncin iyayyenta ba da tuni nayi gaba da wagarar banza kawai mara aji mace chusu kamar an shuka dusa tunma data kara kiban nan sai duk ta koma wani iri da ita wallahi. Haka kuma danki ke son taba saratu ta fito tana fada jin ya dade da fita dakin tunda salima ta soma magana ya fice abinshi. Ni banga abinda yaya ya gani gun Asmau ba tun tana da kurciyarta ita ba kyau ba ba tsarin macen shiga gaban mota ba ita dai gata nan wace iri da ita ba kuma gyara. Ummh mai kyau da gyaran kuma ance karuwa yar kauye kowa dai yaji da nasa ku barshi da matansa son Allah salima ta fada tana mikewa tsaye. Ni mama salima tana ban mamaki wai sai taita nunawa kamar tafi kowa son yaya j a gidan ni abin yana ban mamaki wallahi. Salima din dai bata juyo ba ta shige daki sai saratun ke fadin wai ya dawo nan ke nan kome naji yana fadin wai sun shirya hakan da Asmau ne dama ? Munafuka amma bata fadi ba idan taji kina fada sai dai tace ba komai ai mama ashe da saninta yake can duk dadewan nan ? Allah ba din mugun fata baida kyau ba danace yadda tayi makircin Saiba ta fita itama Allah yasa wacan bafulatanan banza ta futar da ita gidan nan don bata da amfani sai zuba wasu yaya masu gajerta dasu. Iya ruwa dai fidda kai abinda ke hada ki da yan uwanki kenan kuke fada zaki soma kuma aibanta mashi yayanshi ke meyasa kike hakane wai ? Shiru tayi don tasan tunda mama ta kwabeta zancen yaci mata rai da gaskene da ake cewa mama din tana da son jinin ta ita tasan hakan ba karya bane da ake fadi. Don indai yaro dantane ko jikinta tana son abinta ta gano hakane tun akan diyan habu duk yadda taki maria tana son yayanta data haifa da danta wanan yasa ta kame bakinta tayi shiru. Tun a lokacin ba wanda ya kara wani zance a kai game da daaowanshi gida din kamar yadda suka dauko zancen da farko da ace mama ta kama zancen saratu ta fitone tayi maganan aminiyarta lokacin. Sai gashi uwar ta katseta da zancen yasa tayi shiru can kuma bangaren itama Asmau daya shiga wajensu ta nuna bacin ranta a irin sallon nata kishin don cewa tayi dashi aida ya zauna can din ya kara kwanaki. Ba abinda ya dameta sai takura masu da zaiyi a yanzu da gyara wancan kinyi kaza kinyi ba daidai ba ke kazamace hakan kuma baisa ta gyara halinta. Aiko yana shiga daki ya fito ya fara fada yana fadin tunda ya kwanta jinya baijin an taba share mashi dakin nan ma ? Ta yaya mace zata zauna bata da aiki sai kazanta da lalaci ya nufi tsintsiya ya dauko ba abinda yafi bashi haushi kamar bandakin dayaje alwala har wani renewa yayi saboda kazanta. Ganin hakan yasa ta karbi tsintsiyan a hannusa yasan ba gyaran kwarai zatayi ba amma ta fara kore wanan kazantan dake daga mashi hankalinsa. Koda ya dawo bayan sallah isha,i ya samu tana girki wai dama basu da niyar dafa abincin dare sai kuma gashi shine ta dora girkin dafa dukan shimkafa tayi. Ya shiga daki tagama ta kirashi take fadin ga abinci nan an gama ya dan jima ya fito ya dubi yaran dake kwance har sunyi barci cikin tausayi yasan basuci abinci ba sukai barci. Yake fadin sunci abincu tace kafin tagama sunyi barci nan ya soma fada da ita waike Asmau wata irin mace ce ke don Allah ? Wanan hali naki dole mutum yayi aure ko bai shirya hakan a rayuwansa ba ai ki duba yaran nan kefa kika haifesu Rahama dana fito gidanta yaran dake tare da ita irin dadin da sukeji a wajenta. Ke yaushe zaki hankaline wai Asmau kefa kika haifi yaran nan zaki barsu su kwana da yunwa shiyasa a kullum suke fige kamar kar Saiba tabar gidan nan komai naki a yanzu ya kara tabarbarewa ga baki daya wallahi. Dama ai ka saba fadan tafini don kafadi haka matanka sunfini aiba yau ka saba fada min hakan ba ? Ni wanan bai taba damuna tunda nasan ina kokarina kaine baka ganin hakan yaja tsuki ya bude plate din abincin data kifa wani saman wani da niyar yaci. Abinda ya gani shiya tunzurashi ya mike kawai yabar falon zuwa dakinshi dama tsamin falon ya isheshi a cikin daurewa yake karfin hali. Haka a yadda yaken ya dan kara gyara dakin ya feshe da kamshi har zuwa ban daki ya samu waje yana maida numfashi. Haka ya kwana da yunwarsa cikin dare kodaya falko ya ganta a bayansa tana nasari da safe ya fice sallah daya dawo wajen iya ya nufa. Ya kai karan Asmau din iya dai hakkuri ta bashi tace idan ya matsa ni zai shafawa laifin yanzu don kowa zaice ban barshi a banza tunda ance so nake in kore su in mamaye gida ni kadai yadda yar uwana take zaune ita kadai. Iya din dai ta kira Asmaun tayi mata fada sosai ta kuma gaya mata ta kama kanta in har ta bari ta tunzurashi ya kara aure ita tasani. In kuma so takeyi Saiba ta dawo ta hanata kwaciyan hankali to ta matsa tasan komai yana iya faruwa don da ya auro wata gara ya dawo da saiba din dakinta. Wanan zance shiya daga mata hankali sosai in akwai abinda ta tsana taji anyi zancen dawowan saiba gidan gashi iya ta fara fadin hakan kuma . Taji fadam iyam don kuwa a ranan ta wuni gyaran gidane tun safe ga girki data daukeshi wani jar duniya a wajenta runda yace bata iya girka abin kwarai ba shine ta zage tayi masu tuwo da miyan shuwaka. Yazo gidan mu ya dubmu lokacin sha dayan rana har ta gwauta koda ya shigo ina daki ina barci naji ana ja min kafa hakan yasa na falka. Yana tsaye cikin fararen kayan daya saka a jikinshi annurunsa daya fara dawowa lokacin sai naga ya dan gushe min ga gani. Kun tashi lafiya ya fada na tareshi da fasin ina kwana ya amsa min yana fadin kun bar gida bude kun shige daki kowa na barci. Nayi mika ina fadin mun karyane naji kasala ya kamani nazo na kwanta bansan nayi barcin bama wallahi na fada ina kokarin tashi zaune. Falin muka fito tare mun dan taba hira ga kuma girkin dana dora muna na rana yana gidan saida akai sallah azahar ya fita.
Chapter 267 · 0% Book details