Sashe 4
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a wajen shi kuma lokacin ya shiga masallaci ya yayi sallah ya fito shine ya nemi mahaifiyar tasu . Akwai sabo da shakuwa sosai tsakanin mama Dubu da yaranta ta koyar dasu shakuwa da ita irin ko wani hali suke din nan ko a inane kuma zasu kira mama su sheda mata halinda suke ciki din. Suna gama wayan ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo fuskansa yana bin garin da kallo wanda yake kallonsa tankar a Nageria yake bawai kasan waje ba. Komai nasu rayuwan da komai zaka iya kirasu da yan Nageria don hatta shigan suturunsu iri dayane da mutanen Nageria . Mazan shaddane ko yadi ajikinsu da kalan dinki kuma iri daya dana yan Nageria saidai ya fahinci suma suna da yawan kabilu don yanayin shigar tasu daya sha bambam . Ya fahinci akwai masu siffan larabawa a yanayin shigarsu haka kuma a take wajen ya fahinci bambamcin dake akwai da wa yanda basa sallah a cikinsu. Mota ya bude ya zauna yana dakon abokan tafiyanshi da sukayi tattaki don duba abinda zasu dan iyaci a wajen don suna son su fara haka na,uransu da zai watsowa al,umman duniya shirin kai tsaye. Ido ya dan lumshe a cikin gajiyan dake dibansa don ba abinda yake nema a yanzu sai inda zai dan saka hakarkarinsa ya huta duk da yasan hakan yana da wuya. Inda ka dosa Habu alherin ka yana wajen muryan boyar Allah nance ta safiyan jiya da yabaro kofan gidansu da kwallan maciji yaji ya ziyarceshi a karo na biyu ke nan tun bayan barinsu gida zuwa nan . Don ko acikin mota yayi wanan tunanen inda ya zabura ya daga cikin dan firgita dajin muryanta kamar a gefenshi take zaune. Me wanan matar take nufi da zancen haka din don sai a lokacin ya tsaya yana nazari a kan wanan matar mai yawan murmushi da fara,a a fuskanta. Kana da tarin mahassada da makiya ka kula da addua da sadaka a rayuwanka inda ka dosa alherinka na wajen zancenta ya dawo mai karara a zuciyarshi. Raba kanka da irin mutanen nan masu neman abincine kawai ba wani abuba kadama ka bari zancenta ya zauna a zuciyanka. Wani sashe na zuciyarshi ya gargadeshi da hakan lokaci guda tsuki yaja yana mayar da kanshi saman kujera zubur ya mike zaune don karan gugan motar tasu da yaji anayi ya duba . Wata bakar yarinya daba zata wuce shekara takwas zuwa tara ba haka ya gani tana zoza hannunta jikin motar alaman dai abin ya bata sha,awa har takai hannunta tana wasa da kuran da motar ta kwaso a hanya. Ido ya kurawa yarinyar ya kasa magana data jaye sai binta kawai da yake da kallo gata bakace amma kuma kyakyawan gaske. Han din boniyo ke maria ki jaye wajen nan kada ki daukowa mutane magana ke kadaice yarinya a wajen kowa bai kai hannunsa ba sai ke ? Addah barin taba na koma naba da labari a ruggan mu naga motan tv har na taba da hannuna da sauri yar uwar tazo ta jaye yarinyar tana dangwarar mata kai cikin jin haushi da takaicinta. Yare ta soma cikin fada fada har lokacin tana kai hannu tana dangwaranta kan ta taba mota zata ja masu matsala suna zaune kalau. Baisan lokacin daya bude baki yace da ita barta mana ki daina dukkanta hakana jin hausanshi yasa yar matashiyar budurwan daga kai ta kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta fisgi hannun yarinyar sukai gaba . Binsu yayi da kallo kawai daidai lokacin daya daga cikin abokan tafiyansa ya dawo yana fadin oga akwai matsalan abinci fa a wajen nan. Son mun duba gaskiya abincin nan sai a hankali wallahi saidai fura kan da nono wanan gaskiya ko kamfani za a bude a nan albarka. Baida damuwa ibrahim akwai dan abinda na riko gudun haka ban manta da rafiyan mu zuwa calabar ba ai. Ku karya mu soma aiki kada lokaci ya kure yana fadin haka ya mike zuwa bayan dogon motan nasu da suka loda kaya ya bude ya shiga ciki. Wani jakka da kula ya jawo ya bude bread ne da cake a cikin jakkan sai wani leda dake cike da kayan cima na gwangwani ya debo ya fito daga cikin motar ya nufi dayan motan da yan uwan nasa ke ciki suna hira mikawa kowa yayi suka dauki murna da mashi godiya sai sahabine ke fadin. Kai Habu habu yaushe kayi wanan dabaran haka bamu sani ba murmushi yayi kawai ya nemi waje ya zauna ya bude kifin gwangwanin ya soma ci da bread . Daga kan da zaiyi wanan yarinyar dai ta dazun ya hango daga nesa ta zuba masu ido tana kallonsu cikin shagala tana magana da wata ta kusa da ita. A zatonshi abinda yake ci take kallo sai yaga ba haka ba motar dai tasu take kallo cikin mamaki don yadda take gwada tukin mota da hannunta cikin yanayin wasa da tukin mota. Dago kai yayi suka hada ido yayi mata alaman tazo ta karba ba bata lokaci tazo da saurinta ya mika mata bread din da kifin daya soma ci ta juya da sauri ba alaman tsayawa godiya a gareta ta nufi hanyar da sukabi dazun da yar uwarta. Goran ruwa ya jawo ya soma dauraye hannayesa yana dan yarfarwa kafin ya bude mota yana fito da na,uran daukan rohoto ya soma saitawa yadda zasu samu service a wajen taron