← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 286 OF 306

Sashe 286

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu muka samu sallama dama da iya da mamane sai salima muke zama asibitin da inna dake zuwa itama ta wuni damu wace a yanzu na fahinci taga kamar mama ta karbe matani don da farko itace muke tare da ita. Amma zamanmu jiyar yaya dasu maman tudu din sai muka saba sosai da ita fiye da inna duk da dukkansu suna da halin sukan mama dubu da iyalinta a gabana saidai ina nuna masu hakan bai damuna don ba halina bane zama yi da mutum. Wanan kuma nasan cewa halin kishin mu na matane yasa suke hakan tundai mama gaskiya tana yawan magana da korafi kan halin mama amma wanan matsalansuce ta manya ai bai shafeni ba amma kuma tana da fadin gaskiya dasa mutum a hanyar da zai fusheshi. Din haka koda muka dawo gida mama tudu itace ta biyo mu zata zauna dani ke nan yan kaduna sunzo tun washe garin haihuwan sun dubani hakama Yanda a ranan da dare tazo ta dawo kuma washe gari har dare tana wajena kafin ta tafi. Duk da bai fadi ba kana kallonsa kasan akwai damuwa a tare dashi a yanzu ba lokacin da zai iya fada min ko maye don ko yaushe muna tare dasu mama idan zai shigo wurina. Yayi kokari sosai zamana asibiti haka abokainai da yan uwa suma sunyi nasu rawan ganin a lokacin gaskiya gashi wanda duk yazo da alherinsa mama ke karba idan yazo ta mika mai da farko ya nuna abarmin aimu aka ba. Amma mama ta nuna mai ai damu dashi dayane don haka ya karba ya rage lalura dashi ga asibitin na kudune sai demand suke saka mashi na kawo kudin kaza kawo kawo dai a asibitin har aka sallamo mu muka dawo gida. Ina barci da dare ranan yaya habu yazo dubamu ya jima suna hira dasu mama don lokacin yana gida nabar labari a baya don kuwa mama dubu itama sun shigo a ranan da aikai min aiki ita dasu Asmau da Nusaiba . Ta dauki dan ta kare mai kallo mama ke fadin dubu kinga farin miji kin kasa ba uwayensa su dauka su gani budan bakin mama sai cewa tayi ga faein miji kam amma yazo a yanayi. Baizo lokacin daya dace ace fari yazo ba walwala ba maman tudu tace jam meye na rashin walwala kuma dubu ga yaro da uwar kafiya kalau dasu. Ummm,hummm yaya ke nan nabar zancen don ba zaku fahinta ba Allah dai ya raya muna shi ta amsa da amin tace mikoshi kada ki shaye zakin angonane dai ni kadai ko Ladi tayi ta barni da abina da cewa inna. Da haka aka wasance zancen nata lokacin iya tana waje tana sallah akai hakan suma suka karba sai Asmaucema ke fadin kai lalai mama kinyi ango wanan aiya kosa a ciki sosai tubbarkallah masha Allah ta juyo tana min sannu nayi murmushi ta mikawa Nusaiba ta dan karbi dan a dakile ko minti daya baiyi a hannuta ba ta mayarwa matar yazid dashi ta fice daga dakin wai tana waya. Basu jima ba suka tafi wai yaya na gida yana jiran a kawo mashi mota ya fita don dayan motan tashi da suke fita ta lalace lokacin. Haka zancen mama ya tsaya min a rai don na kasa fassara abinda hakan ke nufi lokacin saina bar zancen a raina. Tare da mama muka kwanta a gado iya kuma falo ta tsaya don lazumin da takeyi da dare washegari tunda safe mama ta tayar dani nayi wanka don anty Nafisa na gidan har lokacin. Ya shigo suka zauna da iya a falo suna gaisawa mama ta fito suka gaisa yake tambayansu dare tace Alhamdullahi maigidan nawa ai bawan Allah neshi baida fitina ko kadan. Kamar dai sak nacewa dubu kai ya biyo amma take fadin wai baku da kama yaron nan kaine ai sak babu inda yaron nan ya rageka gaba daya diyanka ba wanda ya daukoka irinsa duk da uwayensu sukai kama sauran ba dai kamar wanan mai yawan ciwon ita bata rage uwarta ba ko ina ? Ya mike da zuman zuwa daki wajena wayanshi yai kara ya tsaya daukan wayan yana karawa a kunnensa a cijin harshen turanci ya soma magana da maishi har ya shigo dakin ina zaune nayi zufa na gama shan tea ke nan a lokacin. Hannusa yakai yana share min zufan tare da fadin eh nine kwarai kuwa nike magana ya tsaya ya saurra da kyau ga bayanin da mutumin yake mashi na daiji yace Allahu akbar kabiran . Jin hakan yasa na dago na dan dubeshi daga inda nake zaune din ya hannusa yana rike da nawa har lokacin godiya ya somayi kafon ya kashe wayan yana rungumeni ya furta Iam back Rahama in sha Allah kayana da suka salwanta anganosu yanzun aka kirani daga can. Farin cikine ya kasheni ina murmushi na furta Alhamdullahi Allah abin godiya wai Allah mun godema. Ya sakeni ya juya falo zuwa falo wurinsu mama yana shiga ya daga hannu yabawa Allah kirari da godiya ya duka yayi sujadan godiya ya dago yana fadin me zance mama wanan mijin naki lalai arzikine an gano kayana da suka salwanta a can kasan aka kirani ana sanar min. Masha Allah suka dinga furtawa a cikin murna budan bakin mama sai cewa tayi Allah ka rufa wanan asirin dama na fadawa dubu hanya Allah yawa gareshi yanzu me zatace don Allah kuma ? Tace wanan dan bai zo a sa,a ba don yazo ba a cikin walwala don haka ita batayi dashi nace mata hanyan Allah da yawa yake yanzu gashi ? Ita dubun ta fadi hakan yaushe tayi wanan zancen banzan haka banji ba a ranan da sukazo asibiti mama taba iyan amsa tana labarta masu yadda akayi. Yoo kuji zancen bamza don Allah jininka zaka tsaya fadawa wanan zance haka abin kunya abin takaici wai meke damun dubune kamar wace kwaro ya hau kanta don Allah jinin ja zakaiwa wanan furcin ? Wanan kam saidai a kirashi da arziki yaci babban suna mohammad za,a saka mashi insha Allah dama dashi nayi mashi hudu babane ya dawo . Gaskiya kam yaci wanan sunan wanan da arzkine yasha sara da suka da sassaka da kushe tun yana cikin ciki har fitowanshi duniya ba a bari ba kai jama,a Allah na gwadawa mutane isharanshi tun a duniya. Dubu dubu meya samu jan yarinyar nan ne nikan sai ince ko mutanen boye sun shafetane wai ba a sani ba dariya taba kowa datake zancen nan . Kubar dariya don Allah iyan ta kara fada tana fadin nifa abinta ya fara daure min kai jama,a kutayani duban zancen nan na dubu jininka yazo duniya ka nuna bakin ciki a fili kana wanan furcin haka abin dubawane zancen nan ? Ta fada don nima abinda tace min ke nan a lokacin wai Rahama bata da sa,a gashi ta haifo da a cikin rashin sa,a yazo babu komai sai wahala. Duba fa wanan zance haka ina ya fito ki kyaleta iya komeya faru kaddaratace a hakan ai Rahama tayi hakkuri sosai da abubuwan nan don haka ki kyaleta muyi mata addua inma wani abin ne ya hau kanta Allah ya yayye matashi iya. Ina ganim gobe insha Allahu zan tafi lagas zan bar nan zuwa Abuja inshiga jirgi don suna nemana ai ina ganin suna ba satin nan ba ko yake tambayan mama. Ina sai maijego ta kara samun lafiya dole a dage sunan nan don aikin da akai mata saita mayar da karfin jikinta . Haka nayi tunane ban fada bane kada ace wani abu ya fada mama ta bashi amsa da fadin haka abin yake ai sai an mayar da sati daya ko biyu maijego ta murmure ake suna idan aiki akaiwa mace. Sun zauna nan suna hiran yadda abin ya kasance haka lokacin daya kwanta ciwo yana processes din fitan kayan nasa ciwo ya kadashi sai wani abokin hurdanshi kirista ya dauki kayan ya boyr a can da suka isa. Nan kuma ankira a tura kudi habu yabi don kada kayan ya salwance yace ba kudi a hannusa a turo mai daga wajensu sun turu din kuma aka kama amfani dashi wajen magani. Har kudin sukai rauni koda habu ya samu zuwa kuma ba issasun kudin da zasubi kayan shi kuma baiyi dabaran karawa da nasa ba a samu kudin su fito don maganan su saiba a lokacin kan yana tausan dukiyan su kadai shida yazid ba a basu komai. Ke mai karatu kinsan harkan wani zumunta da zama a babban gida gidan yawa yana tara mabanbantan mutane masu banbancin ra,ayi sai a cakude ayi ta zaman tsama a tsakaninsu. Irin wanan halin shiya shafi habu donshi dan no case ne suna wanan maganan ya shafi dan uwashi har kowa nasa ya hau fushi tun a lokacin ya fita batun komai daya shafi J din saboda zuciya. Tunda ya bar gidan yake zirga zirgan neman kudin tafiya don dan kudin wajensa daya tsira dasu lokacin ya saka a wani aikin kuma don dai a samu a karu din kada akai kasa warwas. Saiga Allah yayi ikonsa kayan sun fito ba abinda ya samesu yayi sadaka ya godewa Allah yayi hamdallah har yamma basu da labari don ko mama bai fadawa abinda ke nan ba. Saida Aminu yaje gidan take samun labari da yake fadin wanan haihuwan maman zaria ya jawowa uncle alheri ta juyo tana kallon yaron shekeke don jin furucinsa. Amma kai yarone wani yaro yazo a sa,a yaron da zuwanshi duk ba alheri a cikinsa sai tsiya Jafaru dake cikin walwala auren yarinyar nan da samun cikinta ya zamowa mutane tsiya yanzu a gida. Don baka san yadda muke bane a baya kama sani ai kana zuwa kana gani ko bakazo ba uwarka daku kuna gani a tallen ku yanzu fa wakeci banda ita, ? itama din yanzu ina ma ya gansa balle waninta yaci din ? Amma dai tsohuwar nan uncle da dukiyansa ya fito zaki tsaya kina fadan hakan ya fito gidan ubanka mama ta jefawa yaron zagi. Haba mama wanan abinda kike fadi kan jaririn nan wallahi bai dace ba shi yaro ai Allah kadai yasan arzikinsa sai masu hassashe ke fara fahintar arzikin yaro tun yana
Chapter 286 · 0% Book details