← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 306

Sashe 3

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiyace ta mota da zai dauki dogon zango haka suka fara tafiya tun suna dan hira a tsakaninsu har abin yakai da anyi shiru kowa na tunane a kansan zuciyanshi. Dosan mabila da sukayine yasa su fara bayana mamakinsu a fili kowa na fadan albarkacin bakinsa ga albarkan kasan yankin mabila din. Abin sha,awane da daukan hankali ga bakon zuwa wajen harma wanda ya saba sai yabi dabbobinsu da kallon shawa yadda suke daban da wanda aka saba gani. Lokacin da suka zo wajen wanan hawan kusan kowansu hannushi a gaba yake yana ganin kamar ba zasu iya hawan nan ba don yadda sukaga wajen. Sai gashi cikin yardan ubangiji sun hau lafiya sun gangara kuma lafiya a sannu suka fara barin cikin nahiyar kasan Najeriya zuwa cikin kasan camero dake da iyaka da Nageria. Abin sha,awa don basai ka tambaya ba alakansu da addinin musulunci don har yan wani addinin shigarsu shigen na musulmaine su a kasan sukeyi. Tafiya dai tayi tafiya don shi driver yasan yankin da za ayi wanan taron wanan yasa basu damu da yada zango ba sai tsatsaya ko ina ba. Saidai idan lokacin sallah ya riskesu sai kuma shan man a hanya sukama hanya amma sam basu tsaya kwana a hanya basu kamar yadda wasu da yawa suka yada zango. Hakan yasa sukai wa wanan yankin shigar safiya duk da alokacin wurin sha dayan ranane a lokacin duk wani mai lalura ya fito a lokacin. Sai wanda ke gida baida abinyi sannu a hankali yake bin garin da kallo daga bayan motan yayin da driver ke aikin kutsawa acikin garin zuwa babban filin da za,ayi taron gwajin na gargajiyan shekara. Suna wanan al,adanne bayan ko wani shekara goma idan ya shige in rayuwa ya kewayo ake haduwa wajen wanan shagalin nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya. Abaya kasan Nageria tana irin bukukuwan nan na nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya wanda yake kawo dankon zumunci da habbaka sana,an mutane da cigaban kasuwanci harma da zumunci a tsakanin yan garuruwa na nisa dana kusa. Sai a yanzune da abubuwan kasan suka tabarbare wanan al,adan ya mutu mutus a arewancin Nageriaa sai dan abinda ba,a rasa ba dai kawai da akeyi yanzu. Sai dai al,adan kamun kifi da wasan ruwa da sauran al,adun har yau har gobe mutanen kasan kebbi a garin Argungu kabawan asali basu daina hakan basu a wajensu. Don suna raya garinsu basu bar al,adansu da suka gada tun kakanin farko ba da kakani baya, don manyansu sun rike da wanan abin sosai tare da kawo cigaban nahiyar tasu ta Argungu din har gobe. Wanan kadai za ace an saurayi a yanzu cikin arewancin Najeriya da har wasu kashe duniya suke zuwa kallon irin al,adunmu na hausawa tare da fasahan malam bahaushe dake tafiya da al,adanmu na Nageria. Bayan shishi din a gaskiya yana da wuya ace an saura wanan habbaka al,adan da sauran kasashen africa dake kewayen nageria irin su Niger, ghana, camero kwatano da benin da sauransu su basu yarda sun bar al,adunsu ba kamar mu. Zama ya gyara daga bayan motan yana sauraren Sahabi mai daukan photonsu dake wanan sharfin akan nahiyar ta arewacin Nageria da yanzu abubuwa suke ta kara lalacewa a kasan saboda sanyi da rashin sanin ciwon kan malam bahaushe a yanzu. Ai baka sani ba malam Sahabi zance dakai wanan abin tun lokacin da aka ragewa gidan Redio Kaduna karfi da power abubuwan da dama duk suka shiga tabarbaremuna kai in maka na mahaukaci kamar anyi wanan abin da manuface zance dakai. Don wallahi ba karamin koma baya haka ya mayar da Arewa baya akayi ba da hakan hakan ya taba kima da mutuncin arewa sosai a kasan nan. Dama sune masu haskawa suna yadawa amma tunda wanan ya faru sai sannu a hankali kaga abubuwan sun fara ci baya. Hakane kwarai malam ibrahim maganan ka dutse wallahi wanan abin ya taba arewa sosai don kashe wanan gidan redio da sauran waje irin masakan kaduna su gidan kada da wajen fata wanan abin ya kawo muna cibaya sosai a arewa yanzu don da suna raye matasa zasu samu aikin yi a kasa. Salatin Abubakar ne daga bayan motan ya dawo da hankalin driver ya maida hankalinshi sosai ga a saman dan wani tsukaken haya da suka biyo inda wasu yan mata ke gara amalanken shanu. Wanda saura kiris su gwauro da juna Allah dai ya gyara ya takaita masu wahala dole sukaja burki suka tsaya suna maida numfashi. Malam ibrahim ne ya soma fitowa daga cikin motar yana fadin kaga min almuran yarinya kawai Allah ya kawomu lafiya saida mukaga mun shigo gari muna murna zaki ja muna tsiya. Allah dai ya gyara malam ibrahim barta ta tafi kawai itama kauyancine bata sanda mota a bayanta ba sun dauka sai masu kafa kawai suke tafe a hanyar. A daidai lokacin da hakan ya faru uwa mai kulawa da yawan addu,a ga yayanta takanji wani yanayi na daban aduk lokacin da wani mumunan abu zai samu danta. Irin wanan yanayin ne ya ziyarci mama a lokacin sai ta shiga maimaita innalillahi a kasan zuciyanta da sauran addu,oin da zasu aikawa yayan ta dake cikin duniya dama wa yanda ke kusa da ita kariya. Kasa hankalinta gida biyu tayi tana tunanen Abubakar ko Jafar mai yawan tafiye tafiye don shi ko yaushe a hanya yake dan kasuwane bai tsaya ga aikin gwaunati ba ya aje ya soma kasuwanci da yake ganin yafi mai aikin gwaunati a rayuwansa. Alhamdullahi kuma an samu cigaba sosai a wanan harkan da yanzu har yakai lamarinsa ya fara tsone idon makiya. Su ukkune diyanta maza da Allah ya bata da marigayi din sai mata ukku shidda ke nan matan biyu kananane koda mahaifisu ya kwanta dama autar ta ko yayeta batayi ba a lokacin. Wanan yanayin daya bakunceta yasa ta fita da sauri ta yafa hijjab dinta dauke da kwalin sugar a hannunta wanda ta saya a cikin hijjab dinta. Kofan gida ta nufa akwai tsangaya gaba dasu kadan can takai a rabawa yara sadaka shi kuma malam ta bashi naira dubu sadaka. Tun kan tayi nisa take jin an fara raba sadakan sugar tana tafe da dan saurin don ba fita sukeyi haka ba don wai mijinsu ya rasu suna cikin gida ko yaushe zakice mijin nasu yana rayene. Don komai da akeyi gidan ba a fasa ba don ko wani daki na gidan yayansu suna rike da uwayensu da kannensu da wa yanda basuyi aure ba. Rayuwan gidan marigayi Alh Sanda rayuwace ta ba yabo ba fallasa ga iyalinsa daya bari duniya don ko yabar masu abinda zasu duba kansu ko bayanshi. Daidai wadata gwargwadon hali dai ba cancan ba kowansu ya samu kaso daga abinda marigayin fitacen dan kasuwan tsohon yabari. Wanda bayan rasuwansa duk kokarinsa da yake raye wajen ganin ya tsaya ya hada kan iyalinsa koda bayansa ba wani matsala ko barakan rashin hadin kai da zai biyo bayan hakan . Sai gashi a karshe bayan Allah ya karbi rayuwansa an samu dan matsala a tsakani iyalin nasa saidai ankai zuciya nesa da wasu bangare sukayi don kawai a zauna lafiya. Haka din ne kuwa ya biyo baya a yanzu masu zaman hakkuri sunayi yan bamu damu da gado ba ko dashi ko babu muna tsaye da kafafun mu. Irin bangaren dakin mama ke nan dake da yara kana a cikin gida don ita Allah bai bata haihuwa da wuri ba har mata biyu sukazo a bayan ta sukai ta haifo yayansu sai can kwatsam ubangiji ya azurta da samun ciki. Dama kamar camfi haka zancen yake kuma ga duk matar da bata haihuwa zakiga ubangiji ya azurta hannunta da arziki duk sana,an data dafa zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Saidai da zaran mace ta soma haihuwane zakiga arzika ta ya soma jayewa sannu hankali ya koma ga yaya kuma wanan abin kamar wani camfi haka yake idan mutum ya duba. Haka har in Allah bai azurta ta da haihuwan ba zakiga mace komai ta dafa da sunan neman kudi abin nan zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Anan dai kamar wani baiwane ko hikima na ubangiji daya barwa kansa sani akan hakan saidai kiga mace ba haihuwa tanata wahala da yan uwa bata gajiya da hakan. Irin wanan rayuwan mama Dubu tayi da farko a rayuwan zamanta gidan mijin nasu abaya tana da abin hannunta sosai datake juyawa wanda har yakai ta mallaki wani fili babba a lokacin . Saidai ta boye hakan ga yan uwan zamanta tabar wanan tsakaninta da dan uwanta da yai mata jagora a lokacin har ta mallaki wanan filin a wani sabon unguwa da gwaunati ke yankawa mutane filin. Wanan dan uwan nata shine ya karfafa mata ta soma gina da sunan saita bada haya inda taja daku part part har hudu a gidan saidai Allah bai nufi ta karasa ba Allah ya karbi ran mijin nasu inda ya barta da yara kanana tare da ita. Sai bayan rasuwan mijin nasu da son kai ya shigo cikin rabon gadon sune manya dake da diya masu girma da kuma yan uwa dake fada aji suka shiga suka fita aka tauyewa marasa galihu hakkinsu. Dan abinda ta samu ita da yaranta shine suka sayar ta karasa gina wanan gidan nata data soma gina sai kuma hakan ya dawo ya tsonewa abokan zamanta idanu daga baya. Wanan ya kara ja mata tsana da tsangwama daga ita har yaranta saidai duk da wanan mama Dubu bata yarda ta bargidan mijinsu wanda ba a kai ga rabashi ba har lokacin tana zaune ciki har yanzu a part dinta anan take rayuwanta da yaranta kanana da basuyi aure ba. Bayan ta dawo daga kai sadakan hayaniyan yan cikin gidan ne ya tareta tunda ta doso gidan hakan baisa ta tsaya kula mai sukewa hayaniya ba don indai da sabo ta saba da hakan ai. Wayanta dake makale a caji ne ya ta samu ya kara ta dauka muryan Habu dintane taji yana sheda masu saukansu lafiya tare da mata bayanin irin nisan tafiyan da sukasha a hanya. Murmushi tayi tana fadin a godewa Allah daya kaddara saukanku lafiya Habu tunda ankai lafiya ai Alhamdullahi. Sukai sallama don sahabi ya shiga nema masu abinda zasu dan samu suci
Chapter 3 · 0% Book details