Sashe 290
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
a Abuja mama ta hada min shayi mai zafi taban ina sha. Lokacin anty barakha tashigo take labartawa iya abinda sukayi da uwar da fadan Jafar da nusaiba din a dare har take fadin ta fahinci saiba bata bar uwar a banza ba. Maman tudu ta tsoma baki da fadin Dubu ko banza bata bincke abinda aka fada mata dashi take amfani haka take tun farko Alh yayi mata fadan hakan bata daina ba. Saukina a yanzu ke Amina da yake dubu tana shakkunki har yanzu iya ta fada nagode wa Allah daya barku tare da bansan iya inda abin nan na dubu zai tsaya ba. Yarinya karama tana amfani da ita don ciwa manufarta akan yayanta amma dubu bata gane ba tana ganin hakan sone bata san tana dafa kanta bane da kanta yarinyar nan tana cikin silar tabarbarewan komai na gidan nan a yanzu. Shi yayi sallama ya shigo yadda ya samesu ya bashi mamaki yaya barakha bata boye mashi ba ta labarta mashi komai yace ta barshi kawai da ita yasan komai ai. Ya shigo mun gaisa dashi ya tambayi jiki ya dan jima ya fita yana fita kai tsaye ya nufi wajen masu aiki girki ana gaisawa yake tambayan ina naman da aka kawo aka fito mai da dan nama kadan da aka soya. Ina naman kafa biyu da baya barakha tace matanka suka karba aiba mu suka bawa ba Asmau ya nema yake tambaya akan me suka rike komai a hannunsu ga yaya barakha a gari ? Ni nikan ban san komai ba na daiga ana yankan nama a gidan nan amma ba wanda tace dani komai ta fada a cikin sanyi murya. Ina Nusaiba ta fito tana fadin gata yace don me kika karbi komai da yaya ya aiko dashi ga yaya barakha gari ? Don me na karba fa kace don na karba shine abin magana kuma eeh ya fada a gadarance sai tace to ita yaya barakhan ta kawo karana kome ? Ke ina kayan suke nake tambaya ba dogon magana ba ta kawo karanki har kin kai wanan matsayin da zakiwa yayata abinda zata kawo karanki a wajena ? Ban aje wanan matar datafi karfina har ta wullakanta min yan uwaba tukun nazo ina tambayan nama aka nuna min dan wani abu can a kasan kwano ? Shina bayar ta fada a cikin gadara ki fito da sauran yanzun nan to idan na fito dashi mufa ta fada baki sake cikin namaki yace kufa ? Kufa name donki na yanka naman nan ko don sadaka ke koke kika haihu a gidan nan ba zaki min iko da abina ba tunda ina da yan uwa fito dashi nace . Tayi tsaye ya juya ya nufi part dinsu din tare da kiran Asmau tabi bayanshi ita Saiban ta bisu a can fada ya turnike yayu mata dukan tsiya a gaban mutane aka fito da naman a cikin wani jan kula data shake da nama har bai rufuwa. Ga iyayyen suna magana sai zagi take aika mashi da cin mutunci ya kyale har ya juya take fadan ba dole kayi min cin mutunci ba tunda matarka ta zugoka ? Dama wani dane ba dan ,,,,,,,, ya juyo gareta kamar wani tsohon zaki yasa bata karasa ba yace karasa mana tayi shiru yace ke Nusaiba kije gidan ku don Allah na dai sakeki wallahi. Dama nasan shirinkine kika takura sai ayi suna a nan don kiyi muna tozarcin da kika saba saboda mama dake kama maki kiyi min iya shegen da kike so tana sakeki wallahi. Salati aka dauka muna tsaye bakin window daga dakin da muna kallon duk abinda ke faruwa a gidan nida biba a hankali na juya zuwa bakin gado na zauna. Ba zance ga yanayin da nake ciki ba a lokacin shigowan mama yasa na dago take fadin sun sami abinda suke nema dama masu iya magana sunci idan zaka gina ramin mugunta ginashi ya zam gajere. Sunyi hakan don su bakantawa mutane rai yanzu gashi abin ya juye a kansu ba komai bane na sani wanan abin shirine dama don kawai su bakanta baki su bata shirin ga nasu ya baci a yanzu. Ina dadi danka ya tsawata maka a gaban mutane dubu bata da hankali da har take kokarin batawa danta ta goyi bayan wata gashi a gaban kowa ya bata kunya yau. Fadan hakan yasa na fahinci bayan barin inda nake kallonsu wani abu ya faru kuma wai ashe mama cewa tayi ba inda Saiba zata udan yace ta bar masa gida saidai shiya bar gidan baki daya yaje inda aka tsafeshi ta sheda an tsafeshi din . Mama matukar kika hana saiba fita wanan karon zanko nuna an tsafeni din ya fada ya shige cikin part dinsu har ya shiga dakinshi ya fito ya kira Asmau tana zuwa yace ta fara tattara kayanta ta kalloshi yace zamu bar gidan nan ya juya ya shigaciki. Da wanan zance dai suka bata min plan fin sunan da sukeson raina ya baci sai gashi nasu ya bacisu yan garin mu da sukazo suna suka sauka wajen mama kaduba sun iso zuwa rana. Tare da tawagan mama har na debe rai da zuwan anty Salma sai gasu sun iso bayansu kadan naji dadin hakan sosai a lokacin. Muna tsaka da shagalin suna yan uwan saiba suka iso da tashin hankali yaya barakha ta tare zancen ita da yan uwansu suka fara fada a tsakaninsu ko leke yan uwana basu leko ba har sukaci suka sude saiga mama ta koma kuka don yadda yan uwanta ke zaginta da danta a gabanta sukace inma munafuncine mamace ta hada ai. Yanda da anty Nafisa suka shigo da girkin da akayi don yan uwana na kudi muka bayar don abincin yayi dadi sabodasu don haka ba wanda yasan da hakan sai lokacin da suka shigo da manyan kulolin abincin. A nan kuma sai hakan yaso zama laifi yaso zama don saiga sakon mama wai naki debo abincin inbawa mutanen cikin gida. Anyi ba dadi da hakan ya dagawa yan uwana hankali har suke fadin zasu daukeni zuwa gida shan ruwan zafi tunda nan din ba kwanciyan hankali. Tun basu fitar da zancen ba maman tudu da suka fara fadawa ta hanasu yin maganan acewanta irin hakan a yanzu tsegumi yake kawowa su barni a dakina dana haihu ai haiwan tiyatane ba wani wankan jego zanyi da ruwa masu mugun zafi ba. Magananta yasa suka kyale zancen da wai kona koma kaduna ko can gidan camerro zan koma basu kwana ba a ranan suka koma kaduna anty salma kuma ta nufi Abuja. Munso brin gidan tun a ranan amma wai dare yayi mu bari sai washegari hakan yasa muka kara kwana amma tun cikin daren mama ta tattara komai da muka samu aka kai wancan gidan da muke. Nidai ban san don me tayi hakan ba don haka ido na zuba mata don ta fini sanin waye mama haka kuma kayan suna irin wanda akance daga miji ko yan uwansa bai fitar ba a nan bayani kawai yayi min cewa kayan suna gida ya aje min idan yan uwana suna son gani suje can gidan wanan yasa kafin su tafi Yanda ta kaisu suga kayan daga can suka tafi sam ba a shigo da kayan gidan ba. Koda daren sun kara fitina mu dai mun kwanta don ko mama bata fita ba har iya don mun rufe part din mu don gajiya. Washe gari kuma sallah sukayi mama tace azo a kaini gida don kada kayan da iyayyena sukazo dashi ya lalace ban nan gida duk da su anty Nafisa sun koma da biba da Aminu. Ko a lokacin duk da safen na suna kan rigima dai an taru a part din mama ana faman shari,a muka bar 'masu gidan muka dawo ba kuma zance mama ta shigo ta duba moh,d ba har muka bar gidan.