Sashe 34
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
safe a daidai lokacin daya dace mace ta mike ta dorawa mijinta da yara girki safe. Idan baku koya a yanzu ba sai yaushe zaku iya hakan don Allah, irin wanan lalacin shike wahal da matan shiyan can da yayanku yatara. Idan baka koya a gida sai bayan kayi aure kace zaka koyi abu yanzu don basu koya a lokacin daya dace ace sun koyi hakan ba yaushe zasu iyashi yanzu. Dankalin turawane da kwai shake a cikin kulan da Sare ta bude din take fadin nasan dai wanan har damune aka zuboshi. Nasan baza a rasa ruwan zafin da za a hada shayi a nan ba ai shiyasa ban dauko ba maria din ta fada tana kallon Sare. Hakan yasa na fahinci ta zubawa kowane harni mu karya a nan din mikewa nayi na dauko plates s kitchen na fito dashi na zama nayi na fara dibarwa iya dana fahinci tsohuwar tana jin yunwa a lokacin don fadan da takeyi. Na zuzuba masu a cikin plate na mikawa kowa nasa lokacin naji ya Habu ya soma magana yana fadin Iya zankai Maria asibiti a dubata ? Wani abin kuma ya samu maria din iya ta fada tana duban yar uwar tawa yace a,a iya zandai kaita a dubatane ko da abinda zasu iya bata asibitin ? Wani kallo tayi mai tana hade dankalin data tura bakinta dakyat tace Habu kana haukane da zaka dauki matarka dake fama da laluran jinnu zuwa asibiti ? Jinnu kuma iya ya fada yana kallon tsohuwar yayinda yar,uwata ta dukar da kanta kasa cikin sanyi jiki nabita da kallo cikin mamaki jin abinda tsohuwar ta fada. Kaga mubar zancen nan yanzu ka bari uwarku nasan tana nan tafe gidan nan taje ta shirya wajentane ta dawo yau din nan don ta fito jiya bada shiri ba yasa ta koma gidan. Sun dan jima a part din kafin su fita nabi yar uwata da kallon tausayi don na fahinci me iya ke nufi da zancen ta saboda matar baffa dake fama da matsalan jinnu idan tafara lalura saita ba mutum tausayi. A yadda naji yan rugga suna fadi lokacin wai saboda matsalanta baffa ya aurota don ta rasa manemi baffa yace shi zai iya yanzu har ta haifi yaya uku da baffa lokacin da muke rugga din tare dasu. Tuna hakan yasa hankalina ya daga sosai a lokacin gashi mijinta yana gari bamu samu kebewa da ita ba tun safe saboda mijinta dake gari. Misalin shabiyu saura mama ta iso da alama zata kwana biyu a gidan don bata saba zuwa da kaya haka masu yawa ba idan zatazo. Balle a yanzu din da taga inawa mahaifiyarta komai mama din ta rage zuwa sosai kamar yadda takeyi a baya zatazo tayi sati biyu ko wata kafin ta kwasa ta koma gida kuma a yanzu saidai tayi kwana biyu ko ukku ta koma. Munyi mata sannu da zuwa nice na dauko ruwa na kawo mata tana zaune iya tana bata labarin yayan matan mama din yadda suka kwasa dasu da safe. Daki na koma tunda na fahinci kamar suna boye muna halinda ake ciki yasa na nuna ban damu da insani ba nima saidai a zuciyana zancen jinnun da iya ta ambata yana daga min hankali. Yar uwata da take kamar uwa a wajena tun tasowan mu da ita na bude ido yau naga tana son shiga halin rayuwa duk da ta girme min nisa ba kusa ba amma tare muke komai da ita ko yaushe muna tare muna gudanar da rayuwan mu. A bakin iya nake jin cewa wai ashe sun fita asibiti a ranan duk data gargadesu da zuwa asibitin fadan da takeyi da yaya Habu din a lokacin ya tayar dani daga dan barcin dana samu a lokacin. Kiran sunana da ya habu din yayi yasani fitowa ina amsawa yake fadin naje Yanda din tana nemana a part dinsu. A kwance na sameta falo da alama sosai tana jin jiki don yanayinta daya nuna hakan sosai a lokacin gaida ita nayi take fadin in gyara part din in dora masu abinci . Cikin dan lokaci kankani nayi duk wani abinda ta umurceni da yi a lokacin na jera masu abincin dana samu taci sosai saida mijin ya shigo wanda kallo daya zakai mashi kasan yana cikin wani yanayi na bacin rai.