Sashe 82
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
komai. Na amsa da to ina karban maganin da yafito a wajena gashi kuma a yanzu ya sake dawo min mikewa nayi jiki na rawa sai lokacin naji yaya habu na fadin ita Nafisa don dan magana ya hadata da Saratu shine zatayi fushin zuciya tace gida zata tafi ? Ke Rahama kira min Nafisa na amsa da to na fita da sauri don a tsarge nake dama a falon ganin daga kawu har ita mama basuyi magana akan maganin da yaya din ya miko min ba. A zaune na samesu dasu iya ga jakkar kayanta a gefe daya tana duban wayanta nake fada mata sakon yaya din. Na fita don ban tsayawa saboda Saare dake falon kwance da waya a hannunta tana charting part din mu nakoma yayata tana zaune tayi tagumi cikin damuwa. Yaya kukayi dasu take tambayana maganin na fara nuna mata kafin na zauna ina fadin Allah ni da zuci daya na bashi wanan maganin kuma Nafisa tana wajen itama. In Nafisa na wajen fa Ramaah kiyi tunanen Nafisa aiba uwarsu daya ba dasu baki gudun ace an hada baki dake a cuta mashi. Shiru nayi ina wiki wiki da idanu don sai yanzu nake hango zalla yarintar danayi na daukan wanan risk din don ba karamin magana bane idan ya fita anji . To ya zanyi aikon gama ya gama sai fatan Allah ya kiyayye yanzu kan don mai faruwa ya riga da ya faru magani kusan sati daya ana sha yanzu meya rage kuma. Da yamma saiga su yaya sun dawo da wanan abinda na fada na karya asiri ba a bata lokaci ba mama ta dafa aka kai mashi ya diba yasha yayi wanka. Yana fitowa ina tsaye na kada wanan maganin kamar yadda yay habu ya fadi dokansa ya amsa ya shanye gaba daya ya miko min cup din tare da godiya. Ya tambaya ko magariba yayi mama tace kamar da sauran lokaci nafisa dake shigowa tace an fara kiran sallah a wasu wuraren ai. Saida yayi sallah magariba kafin ya kwanta kamar karamin yaro ya dunkule a waje daya lamo kallo daya zakiyi mai ya baki tausayi. Ina ganin haka na nisa ina fadin Allah ya sauwaka na fita da kayan wajen zuwa kitchen dinsu da yanzu yake samun gyara don anty Nafisa ko yaushe tana tsabraceshi. Tunda na dawo nashige dakina ban fito ba sai washegari nayi shirin school na fita na biya part din na gaidasu mama ke fadin jiya ina ta jira ki dawo baki dawo ba kodana aika akace barci ya daukeki. Nace ko kema kin damu da zancen shashan nan Saratune ai ita tazo muka kwana tare tunda Asuba ta gudu wajen iya wai batayi barci da dadi ba a nan. Nayi murmushi ina fadin mama maganin fa ina son shiga school kada in makara to sai ki hada din ki bashi tunda maganin yana da ka,idan sha ? Nayi mamaki jin furucinta na ka,idan sha watau yaya habu shima ya nunke su mama a baibai ke nan don kada su gano wani abu kome ya fada masu oho ? Da sallama nashiga duk sa safiyane sosai amma na samu har yayi wankan maganinsa yana kwance yayi rigingine jikinsa saye da farar jallabiya mai dogon hannu. Gaidashi nayi da yaya jiki ya amsa da Alhamdullahi nagode na sada kai kasa ina fadin zan shiga school ko za a hada maganin yanzu ? Har na gama kadawa idonshi yana kaina har na gama na miko mashi ina fadin gashi yaya don yanzu ba sai an rike cup din ba yana iya rikewa yasha da kanshi. Ya dan dago daga kwancen ya karba yasha ya miko min cup din yana godiya ya koma ya kwanta a yadda yake bankai ga fita ba naji yayi wani irin gyatsa yana hamdallah. Kodana fito ban tsaya ba nayi masu saina dawo na samu Nafisa zaune da mama suna magana a lokacin bandai san akan meye ba. Daga kwancen da take daki lamo jin ba motsin kowane ta daga waya yana ringing sai can aka daga ta wayan ke fadin ai wallahi Saare nayi fushi. Ta amsa da fushin me tace wai ace tunda nazo kaduna baki kirani ba haba saaratu amana baice hakan ba ai, na zata kece ta farko da zata nemeni sai naji shiru Allah nayi fushi sosai da hakan. Haba dai tawa nifa sai jiya na samu ya kara dawowa sai kuma na samu wai baku nan dukkan ku iya ke fada min shirme wai kuna kyaman yaya yasa mama tace kuje gida har ya samu lafiya. Humm ni bansan me zance ba banda wanan sakariyar Asmau data fitar muna da zance a fili yar iska ko an fada mata inma kanjamaune haka ake kamuwa dashi ? Ba kanjamau bane wallahi don yanzu yaya yaji sauki sosai ba kamar yadda nazo a ranan na sameshi ba yanzu har tafiya yakeyi da kansa. Don Allah ki bari ! Tace wallahi ko saidai abinda banji dadinsa ba shine wai fa Nafisa da yarinyar nan Ramaah suke taya mama jinyarsa. Su kuma wallahi iam telling you don nayi maganan hakan baiyi ba shine munafuka Nafisa waina nuna ba mama ta haifeta ba kar kiso kiga fadan da mamake min fada wallahi akanta. Nafisa fa ita har ta samu wajen hadaki da mama ke nan bari yar iska kanta zamu koma ksi ba ita ba har wanan mai ido kamar glove saita bar gidan nan shiri nakeyi sosai wallahi. Mutumiyar kin min daidai wallahi ina son ki wajen aiki da zafinsa ai dama kin gansune yadda suke rawan kafa su kakansu ta yanke saka yan iska don a yabeau wai ? Tsiyar banza wa zai yabesu din sunyi a banza wallahi zan matsa naga na dawo ko wata yar iska saina koya mata wayau a gidan nan. Ina yinki nawa Saare din ta kara fada har da fadin Allah yasa kin hada da wanan yar iskan duk su tafi su bamu gida wallahi ni gaba daya haushi suke bani Allah na tsani wanan maria din wallahi haushinta yasa bani kaunar kanwarta din itama. Sun dauki lokaci suna sherin su har mama ta shigo ta sameta duk da bataji sosai ba ta fahinci da Saiba take wayan a lokacin. Saida ta fitone tayi mata kaca kaca ta zageta tas tace kuma zata dauki mataki akanta tunda abinda ta daukowa rayuwanta ke nan munafunci. In ba rashin sanin ciwon kai ba dakece za a hada kai ana mugunawa dan uwanki saratu matan nan fa cewa sukayi suna kyamar shi. Watau ya dauko mugun ciwo kada ya saka masu shine nufinsu ko ? Mama ai cewa ake wai wanan ciwon mai karya garkuwan jiki ya kwaso a can wajen kwatakwali shine,,,,,,,,, Mama dubu bata bari wanan matar takai karshe ba ta karbe da fadin Allah ya kare al,umman Annabi baki daya. Duk wanda yaiwa yaron nan wanan sheri yaga abinsa insha Allahu watau su gasu sakatkaru shine suka yarda da hakan ko ? To mama kokece kikaji haka da ake fada ai zaki kama kanki tunda gari haka ake fadi sai lokacin Nafisa data shigo tayi magana take fadin wallahi ba kowa ba kan sai dai yan sheri . Amma kowa yasan ciwon yaya kamar sammu ko jinnu ke damunsa ta ina ciwonsa yayi kama da wanan ciwon don Allah ? Koma an fada banda jahilci ai suma ke nan suna dashi ko tunda mijinsu akace yana dashi har insun yarda. Rana mama tayi kuka sosai saida kawu yazone ake mayar mashi yace shima yaji wanan zancen kuma mutane dama haka suke meye na damuwa haka da zancen duniya. Ni sai da yamma dana dawo anty Nafisa take min hiran abinda ya faru nace Allah ya kyauta mutane akwai daukarwa kansu wahala.