Sashe 237
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
latsashi na dan lokaci zai shiga hankalinsa kasa muna ido kawai kaga yadda zanyi dashi don Allah ? Yana fadan hakan bai tsaya ba ya fice daga falon da saurin binsa yayi da kallo yana sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanunsa na dan lokaci. Muryan maman tudu ya dawo dashi hayacinsa tana tsaye take fadin yazid ne ko ina daki nake jin muryanshi ai shine ya fita ya bata amsa. Can ya dora da fadin yazone yana fada dani kan tafiyan Rahama wai laifina bani daukan mataki idan an mata cin fuska koda a ganane ? Fissabillahi mama wani irin mataki take so in dauka bayan wanda nake kokarin yi mata a yanzu na rabata da zama nan gidan duk da mama da sauran yan uwanta sun nuna min rashin yardansu da hakan amma na cije naki dawowa da ita gidan nan . Abinda take nufin anyi mata ai in Nusaiba tayi mata ita da bata gajiya da lorafin anyi mata ba daidai ba koda yaushe nakan tsaya kuma nayi abinda ya dace amma duk bata ga hakan ba mama ? Watau abinne naku yake son natsuwa da fahinta jafar duk wanan laifin na Dubuce data ba dakariyar yarinyar nan saratu dama da yawa haka a cikin matanka. Har yaushe zan zauna in sakarwa yarinyar da batayi aure ba dama zama da matan yayyun ta haka zaman daba na Allah da Annabiba kuma ta sani ta kyalesu suna aikata abinda ba daidai ba. Har ace kamar Saratu tana kokarin aibanta jinin dan uwanta tun a ciki da nice yarinya tayi min wanan aikin a dakina ranan danasa yan uwanta sunyiwa ja,ira dukan kawo ruwa da gobe bata komawa . Amma dubu ina taji fa amma sai kokarin kare yarta takeyi daga karshe wai aiba da ita sukeyi ba tsarguwane kawai irin nata data sabayi tana kokarin daukan laifi ta dora akan yar mutane. Irin maganan sherin dake fitowa a bakin saratu kan yarinyar nan ko waye dole ya dauki matakin hakan tunda ba a gidan nan aka kare rayuwa ba. Gaba dayan ku kuna da laifi gaskiya yanzu baga habu ba ko ince yazid tayiwa dayan su irin abinda takeyi tsakanin matanka mana idan gaskiyane ? Dole har in kana son yarinyar nan ka dage ka kwatar mata ince ga kowa a gidan nan shine mafita amma baka zura ido haka abubuwa suna faruwa ba ? Sun dauki karan tsana sun dorawa yar mutane da za a tsayar dasu a tambayesu babu mai kawo wani dalili mai karfi a wanan zance kishine kawai irin na mata don sunga ta fisu da komai sai kuma samun wajen iya shege din. Shiru yayi yana sauraren zancen da mama din take kwararo mashi a lokacin shi dai a iya sanin sa ai yana kyautatawa zamantakewan mu dashi ba zaci zance abindake faruwa tsakanina da mama ko saratu da matanshi zai zama laifi a wajenshi ba. Wanan yasama bai yarda ina yawan zuwa gidan ko shiga wani harkansu da bai zama dole ba amma kuma duk bai tsira daga hakan ba a wajena. Da mama ke zancen idan har yana sonta ai itama tasan yana kaunar yarinyar nan saidai ba zai iya cewa yana fito na fito da magaifiyarshi ba kan abubuwan da suke mata din. Yasani ba a kyauta mata amma yasota da yin hakkuri da kullum yake bata kan wata rana sai labari tunda har mama ta kasa hango alherin yarinyar a yanzu yasan ba zata taba hangowabane kuma. Yau duk wanda ya tsaya yayi maka haka akan naka aiko komai yayi ma zaka iya masa ragowa don hakan amma sam sunki su fahinci hakan ita mama tana ganin komai takeyi tanayinsane don ta mallakeshi da abinsa. Har ta ina Rahama tayi wayau haka duk ance kabar mace indaka ganta amma yasan halin matanshi yarinyar da komai kankanta abu ya batashi zaiga farin ciki a wajenta bata taba raina hakan. Nan ko zai basu kuma a raina a kumazo a wullakanta abin daga karshe yana kallonsa an nakasashi baida bakin magana kan hakan har ya gaji ya saba don ba zai sayo abu ayi amfani dashi yagani yaji dadi ba. Shawara sosai masu amfani mama ta bashi wanda yaji dadin hakan sosai har cikin ransa ya kuma godewa mama din don yaji dadin wanan shawaran data bashi a lokacin. Shigowan mama dubu yasa suka canza zancen take tambaya bayan sun gaisa ta tambayi karfin jikinsa da Yazid ya fitane ta shiga part dinsa bai nan ta dauka yana nan wajensune ai ? Anya kuwa Yazid bai fita ba don yace min daga nan idan ya fita gidan kawu dauda yake son zuwa ya gansa ina ganin ya tafi can din ne ? Gidan yaya kuma da safen nan baiko fada min can zai tafi ba yau ya tuna dashi ke nan shima yaya din yanata korafin tunda ya dawo baije gidansa ba. Yaran nan zumunci yanzu bai damesu ba akan zumunci sai Allah ya hana maka alheri suna yawan wasa da zumunci a yanzu wanda basu sani ba yana cikin abindake habka rayuwan dan adam sosai. Yanzu sai kika ko kana da zumuntan sai a sarema gwiwa a zaci saboda wani abin hannun mutum kaje gidan don a baka akama daurema fuska don gobe karka dawo. Haka kuma zakiji mutun yace ko naje banda abin bayarwa don haka ba zani ba duk wanan halaiyan su suka kawo koma bayan zumutun a yanzu. Kedai bari yaya irin fa hakan ke bata zumunci a yanzu ko baka mutum komaiba yaje wurinka ai ya kyautama haka kuma kai da zaka ai ba ace sai ka rike komai ba da zaka dashi. Har iya ta shigo ta samesu a dakin aka zauna ana hira a nan wanda hirane akan lamarin ciwon shi jafar din da mama dubu take fadin yanzu kan jiki yayi dama daba zancen yarinyar nan daya saka a ransa ba aida sauki ya kara samuwa mashi sosai ? Dole ya saka keko Dubu ance ka samu da wanda ya damu dake kodana munafuncine kuwa yarinya data san yakamata yau ta tafi ta barshi ace ba zai damu ba ? Ki duba da gari ya waye din nan yanzu karfe nawa don Allah amna ba a kawo mashi abin karyawa ba har yanzu fa aiko wanan ya isa mutum ramewa haka ba sai ciwo ba ? Halin Asmaune baki sani ba kuma iya yanzu haka tana can tana barcinta na safe sai tayi mai isanta tace zata tashi ta dora abinci ko kuma an dora din an koma an kwanta ana jira. Dukkansu haka suke har wacan data tafi indai kinga an karya da safe gidan nan to yarinyar nan ce ta tashi tayi muna dabara lokacin da take nan din tana kwana samu . Shine zata dan samo mana abu mai sauki da zamu karya dashi suna zancen Asmau ta shigo da kayan abincin da missalin tara da rabi na safe . Mama din ke fadan cewa wai meyasa suke haka suna da mara lafiya amma ba za a daina wanan barcin safen na lalaci ba sai lokacin da akaga dama a dora girkin abin karyawa ? Wayanta ya shiga kara tana fada tana dauka tana jin muryoyi na tashi a cikin wayan wanda yasa hankalinta tashi har ta furta Yazid da yaya kuma me yayi zafi haka kuma ?