Sashe 159
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
mun hada komai don washegari suna sai dare na samu na kwanta da asuba kuma muka dora abincine don yan zanen suna da za a fita dashi da safe. Na aikawa makwabta dashi duk daba shiga gidajensu nakeyi ba kuma sunji dadin hakan da mota su ibrahim suka jida zuwa family house dinsu. Muka dora wani kuma da za akai part din mama duk da suna abinci suma a gidan sai wajajen two na rana suka kwasa suka tafi nace dasu in ya dawo zan samesu daga baya duk da nasan yana da wuya inje. Koda ya dawo din bai nuna alaman zuwana ba sainice nace dama kai nake jira zancen zuwa can gidan ? No ba sai kinje ba tunda kinyi aiki a nan kowa yasan kin gaji ai ban kara maganan ba sai darene mama takira waya tana tambayan dalilina kin shigowa suna ? Naji yace shine ya hana don munyi aiki mungaji donshi yace in zauna ba sai naje ba din ni dai nasha jinin jikina ina mamakin mama da halinta a kaina yanzu ? Don nice dai bata so da danta har bata iya boye hakan acikin ranta na kula duk abinda zanyi laifi mama zata kirkiroshi a kaina.