← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 306

Sashe 208

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

?. Ki bashi kinji naji muryan yazid yana fada hakan yasa na bashi din naku fara shafa mai a duk jikinshi yana nishi muna mashi sannu har na shafe mai ko ina ban damu da wai su mama na wajen ba. Ga jikinshi har wani rawa yakeyi a lokacin hankalin kowa ya gama tashi da kuma tsoracewa lokacin ya habu suka shigo da maria. In fada maki mai karatu maria bata kyauta min ba nake gani a wanan gabar yadda takan share lamarina a wanan lokacin sai shiru shirun ta ya zamo min illa a zuciyana. Son nasan ko batazo don dan uwan mijinta ba ai zatazo don ni akai akai amma saita dauki sati biyu har ukku ba tare data leko mu ba taga yanayin da muke ciki dashi. Har na fara saka hakan a raina daga baya don sanin halinta yasa na share zancen nacigaba da al,amurana. Wanan yasa koda suka shigo ma a lokacin ban kulata ba ina gurfane a gaban yaya din mama da iya sai faman fadi sukeyi Allah ya baka lafiya ya tayar da kafadanka cikin iyalinka jafar. Ko asibiti zamune yaya habu ya fada a firgice ko anje asibitin me zasuyi da wanan lamarin saidai idan za a din daga gefe kuma yazid ne ke faman karanto mashi addu kala kala daga bakinsa. Sai zufan ya kara tsananta can yayi wani irin ajiyan zuciya ya lumshe idanunsa idabuwan mu yana kansa har lokacin acikin tashin hankali dayawa duk sun koma falo anyi zugun an tsurawa sarautn Allah idanu. Don ba wani mai iyawa ko gwaninta sai Allah gabadaya kowa ya tsunke yayi kamar yana barci har yazid din yana fadin ya samu barcine fa. Can baya na koma na zauna nayi tagumi daga inda nake ina iya hangonshi daga inda nake zaune din suna shawaran fita zuwa asibiti dashi . Sai lokacin suka tabbatar da ya soma magana da gaskiya don yadda ya bude ido yana ambatar sunana da karfi hakan yasa har wa yanda ke falon shigowa da sauri. Jiki a sabule na karasa din wajenshi yana fada min amai yake son yayi in daga shi mun kasa fahintar me yake fada a lokacin sai can nagane ina fadin amai kafin ma na rufe baki ya soma zubo amai ba kaikautawa wani irin bakin amai yake zubowa a bakinsa din. Ya Allah yasa dafin wahalan kake amayarwa jafar Allah yasa karshen wahalankace hakan maman tudu ke fadin hakan a gareshi sai yayi kamar ya lafa kuma ya can ya fara kakarin amai din. Oho har muna fadi kafara jin sauki sai kuma ga wanan lalura kuma yanzu nan fa muke zaune da yar nan muna hiran akanshi. Don yanzu akwai alaman sauki sosai a yanayinshi sai gashi munji daga ciki yana kakari ashe kuma zancen ya baci . Allah dai yasa saukin ke nan yazo da hakan mama tudu ta karasa zancen nata dashi tana kara mayar da hankalinta kanshi. Muryan yazid dake fadin amarya ki daga daga wajen wata daga cikinsu ta kwashe aman nan hakana ya fada yana kallon inda Asmau da Saiba suke zaune. Dan jim sukayi sai Asmau data yunkura tana daga danta daga jikinta yace No ke ki zauna ki rike danki wanan ta kwashe ita. Ai zancen ke nan wanan abin kowa ya shafa ba ita kadai ba amma sun mayar da zancen ya koma wani abu na daban a wajensu yanzu iya ke fadin hakan. Yace wace bata iyawa ta koma gidansu mana iya mu lafiyan shi mukajawa ba wani kishi ba can koda sun bar mata din ai wanan zata iya ma tunda gashi tanayi ba tare data kula da abinda suke nufi ba ai. Na lura da hakan sosai tunda na dawo garin nan iya dama ina son gaskanta hakanne da idona gashi ko nagani a yau. Tun safe daya fara aman nan yarinyan nan itace tsaye a kansa suna binta da kallo me hakan ke nufi ke nan maganganun da kukeyi a kanshi damu yan uwansa ya zama gaskiya ke nan jira kuke ya mutu ku wawashe dukiyan nasa yasa har kuke ragen dan uwansa daya kama komai ya rike a hannunsa yana ci da iyalinsa. Dagowa tayi tana fadin mu muka fadi hakan mu akace ma mun fadi hakan a ga habu din wazai fada in baku ba inda kuka fada sako yazo kunnen mu ai ? Kallon Saare tayi da sauri yace kwarai friend din munafuncin ki kenan ai ita ta fada inda za aji cewa mun kama komai mun rike dani da habu koda mun rike din laifine hakan ? Wanan magana ina kuma ya fito magana haka babu dadin ji mu da ke neman rayuwan dan mu ina zancen wani dukiyansa kuma ya fito a yanzu haka ? Ga sakaran nan mara mutuncin yarinya mana mama bada ita suke zama suyi gulman muba tunda ta zama banza a cikin mu banga laifin maza dake gano halinta su gujeta ba don munafuncin saratu yayi yawa mama. Idan anyi magana mama tace an mata kazafi da sheri ba abinda take nufi ke nan ba yanzu tunda ana zaman jiran gado ai sai kowa ya san zafin gadon da zaici din ke nan tunda ba wanan ce kadai zataci gadon nasa ba. Juyawa mama tayi gun saratu din tana fadin amma saratu abin yai maki yawa wai meyasa kike nuna baki damu da dan uwanki bane ke ? Kin taba ganin wanda yaki nasa yaso bare dan uwa marfin jallone fa yau jafar da sauran yannan ki sune zaman mahaifin ku a gareki sabodawa kika san yarinyar nan ma a gidan nan ? Wanan da kuka tasa a gaba da tsina tafiku sanin ciwon kanta don da biyu take kula dashi haka na farko daukan da tayi masa na dan uwa wanda ya kamata ace kune kuke hakan sai na biyu alakar aurataiya daya shiga tsakaninsu kinga riba biyu zuwa ulku ta samu a gareshi . Kun dauka gulmace gulmacen ku da kyashin da kuke nuna mata zai sa ta gaza dashi hakan bai kara komai ba illa karfi da kuzarin da kuka kara mata ga hakan yanzu. Kada ku dauka bai san meke gudana bane a hakan wallahi yana fahintar komai dake faruwa wajen nan ni ba yau ba yaran nan sun jima da zube min a idanuna . Karku dauka gari ba a san me kukeyi bane ansan komai an kuma sakaku a baki tundau ke saratu kaf yan uwa sun tsanaki a yanzu. Ido rufe maman tudu take fada masu magana iya son ranta yazid na kamawa inda yakewa mama bayanin cewa wai har saratu take fadawa salima cewa sunyi shawara cewa zasu kai karan habu kan ya danne komai na jafar ya hana masu gaba ya hanasu baya basu san komai da ake ciki da zancen dukiyan jafar ba ki duba fa mama da saratu za ayi wanan maganan haka idan ba sun saba hakan ba da ita dama ? Shine salima ta samu habu da zancen take fada mashi abinda ke nan wallahi sunki shawaranane da tun jiya ba wace zata zauna a gidan nan gaba dayab su. A,a yazid ka cireni cikin zancen nan ai gasu nan idan suna abin su ban kulasu ina can ina aikina komai aka kitsa nikan bada sanina bane wallahi tunda nice ke girki kullum saboda su mama dukiya yakai min uban diyana da bai da lafiya Asmau take fadan hakan. Dama na kula da hakan tun kwanaki cewa yarinyar nan ita kadai ke girkin nan don ko yaushe ka shiga itace a kitchen tsaye . Yau nasan ke munafukace Asmau dama kina hakane don munafunci ashe me nakeyi don munafunci da kikace ba zaki kara girkawa kowa komai ba tunda mama tudu tace ba za a kwana dashi ba mena fada ki fadi a gaban kowa mana yadda mukayi dake ? Nan dai tonon asiri ya tashi a tsakaninsu inda har sunan saratu din yafi yawa komai da ake kitsawa ita da saiba ce ke kitsawa har zuwa wajen malam da sukeyi duk Asmau ta fallasasu a bainan kowa yanaji harda abinda basu zaci zata iya fada ba game da suratansu na hassada . Ranan dai rayuka ba dadi a gidan ga mai ciwo ga kuma tone tonen maganan da yazid yajawo akayi na fallasa inda mama dubu a karshe tafi kowa bakin cikin hakan jin saratu abinda take kullawa don kawai ta bata tsakaninta da yayanta din kamar yadda Asmau ta fada. Saida yaya jafar yayi kwana biyu a cikin wanan halin aman har yakai dole aka kara mashi ruwa leda biyu manya ko zaiji karfin jikinsa. Don gabadaya a wanan gabar duk yan uwa an debe rai ma a garesa gaskiya ga badama a koma asibiti dashi haka tunda ansan ciwonsa dai sai Allah saukinsa bana asibiti bane don maganan likitoci gudane su basuga abinda ke damunsa ba suke fada. Barci yakeyi yanzu sosai tun bayan shigan wanan ruwan a jikinsa idan na bashi magani da safe zai koma yayi barci mai nauyi na tsawon wani lokaci idan ya falka in bashi abinci yaci . Allah sarki a hakan kuma fa tunda ya fara dan motsi sallah baya wuceshi zai min kwatance da zaiyi sallah a dagashi yayi idan ya idar kuma ya koma kwancensa. Kan zancen nan saida yan gidansu Saiba suka shigo zaria suka nuna bacin ransu ga abinda ya faru suka bada hakkuri yazid yana zaune yace ai su batayi masu laifi ba wanan tsakaninta da wanda ya ajetane da kuma Allah. Tun daya fara jin sauki yake cin abinci sosai a yanzu don ya fara karban abinci da alaman ma kokon dayake sha ya gunduresa a yanzu din. Asmauce a lokacin take bashi abinci don ita ta girka duk wace ta firka zata zauna ta bashi yayin da kuma wace bata girki zata zauna dashi a wunin . Sai tsarin hakan yayi min dadi sosai don jikina ya fara nauyi da laluran gaskiya a yanzu ko ina samun hutu sosai inyi ta barci. Ina zaune a gefensa Asmau tana bashi abinci dan Asmaun na goye yana a hannuna ina mashi wasa a gefe yaron yasa kuka uwar tana tsaye a gaban mijinta tana fadin saita gama ta kamashi. Sam yaron baida yarda da
Chapter 208 · 0% Book details