← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 306

Sashe 7

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

can gidan suke da zaran sun dawo hutu zasu tare a wajen kakansu suna tayata zama wanda shi jafarne ya tilasta masu yin hakan. Haka kuma idan suna gidan wajensa yana da wuya ka samu gida kaca kaca a cikin kazanta don suna tsayawa su gyara tsakani da Allah. Tsab mama Dubu ta gama shiryawa don zuwa ta dubo mahaifiyarta da iyalan danta don tana hasashen Asmau ta samu karuwa a jikinta yadda hjy Iya ta fada mata . Idan zata zakice ba a gari daya suke zaune ba don shiri takeyi sosai sayi wanan sayi wancan taje masu dashi sai kice tazo daga kauyene ganin su. Saida ta gama shirin da komai ta fito tana fadawa mutanen gidan nasu zataje ta duba su iya ta dan kwana biyu wanan ba bakon abu bane sunsan data saba yin hakan . A zaton suma basu dauka zata zauna kamar take zaune din nan ba a cikinsu da Allah ya albarkaci yayan nata sosai fiye dakowa a gidan kusan ace dai sune sukaci moriyan gadonsu da aka raba na marigayin. Tunda wasun su har sunka ga saida kadaran da suka gada din sun koma rabe rabe duk da mahaifin nasu bai wani dade da kwantawa dama ba sosai. Dama ance mai zari a wajen rabon gado shine nasa bai faye albarka ba kusan haka dinne ya faru don kuwa su yan dakin hjy babba da aka tsaya masu suka samu kaso mai tsoka sune suka fara wullakanta dukiyan nasu. Wanan ya jawo tsaiko da iyayyen mata suka hana yayan nasu raba wanan baban gidan da suke zaune ciki a yanzu inda sukai rayuwa da mijin nasu. Tunda gidan mata hudune ras irin ginan malam bahaushe duk da ko wace bangarenta a kewaye yake sai babban falon marigayin inda turakasa yake a nan yayi rayuwa har Allah ya karbi ransa. Don haka har gobe idan ka shigo kaga yadda suke rayuwansu zakice ko maigidan nasu yana rayene amma kuma kowa a yanzu yana cin gashin kansa sai dan abinda ke shigo masu da akan kasa kamar yadda dai aka sabayi tun baya Allah yasa mu dace ya jikan iyayyen mu da rahama Allahuma Amin. Daki daki tabi tana masu sallama da sai ta dawo yadda kowansu keyi idan zai dan fita sukai mata Allah ya kiyayye zakice ba wani abu na rashin jittuwa a yadda sukeyi din. Saidai hakkurin wani ya dara na wanine a zaman don anyi ba daidai ba an nuna hadama da zalama daga bayane suka sulhunta kansu kan hakan. Yan jikokin gidan da almajirai suka dauko mata kaya suka nufi bakin titi inda zata hau keke zuwa unguwar su iya din. Fitanta soma zancen ta ukkunsu dake fadin yau kuma ta haka aka fito muna ba Habu yayi tafiya ba kada ya dawo ya sauke abinda ya dawo dashi mugani a bamu tabon mu . Sai ita amaryansu tace aiko yaya bata da haka kowa ya sani nan gaskiya ko bamu gani ba sai an bamu in rabon mu ya ratsa. Ni bance bata bamu ba ai maganace kawai nakeyi ta fada a hasale don ba a kama mata yadda taso aja zancen da nisa ba ta katseta. Yaran da suka rakata zuwa titi ta sayawa rake sai dari dari data basu suka dawo gida da murna hakan yasa data dau kaya zata fita suke taso durrrr subi bayanta da sunan rakiya don dan wanan ihisanin da take masu. Itama hakan yana mata dadi tana jin dadin rakiyan yaran wani lokaci takan daukosu suzo su wuni su koma in Jafar na gari mota tana a wadace . Daidai kofan shiga gidan mota ya ajeta da kayanta sanin da mai adaidaita din yai mata yasa ya taimaka har cikin get ya shigar mata da kayan kuma bai tsaya karban kudi ba duk da tsawan da take mashi akan ya tsaya ya karbi hakkinsa amma yaki saboda mutunci. Kauyen Zakuwande ya samu halartan baki daga sassa na duniya mu sanman a yan nahiyar africa manoma da masu kiyo da suka cika wanan gari dam ko ina bakine dake halartan taron mafi girma da akeyi bayan shekaru. Engineer Abubakar daya gama hada duk wani na,ura da zai hasko masu tauraron dan adam dinsu ya sauko daga saman motan yana kara duba saitin dayayi da kyau kafin ya nufi bayan mota ya bude yana dauko goran ruwa ya balle yana kokarin zuba don dauraye hannunsa. Hankalinsa sam bai kaiga dandazon mutanen da suka kewayesu suna kallon aikin nasu ba sai lokacin daya gama wanke hannun ya kwankwade sauran ruwan ya cillan da goran gefe . A lokaci ya kula da jama,an dake waje ashe akwai inda yafi Nageria kauyanci don goran daya cillan suka taru suna wasoson dauka . Har da manya wani dattijo daga cikin masu rige rigen daukan gora da aka tureshi tare da kekensa yasa Habu din fadin subbahanallahi yaje da sauri ya kama tsohon yana tayar dashi tare da kekensa yana mashi sannu. Tare da tambayan baba bakaji ciwo ba ko yace banji ba dana naso dai in samu wanan jallon nasaka ruwa a ciki yara kuma sun hana. Ina zuwa yace ya koma ya dago gora biyu cike da ruwa ya kawowa dattijun ya bashi cikin girmamawa godiya tsohon ya fara mashi sau ba adadi yaja kekensa ya tafi. Juyawa yayi yaje gun yan uwansa da suka zubo mai idanu saida ya karaso ibrahim ke fadin wanan yasa danasha ruwa saina jefa gora a bayan mota. Tausayi tsohon yabani yana bukatan gorance da ganin haka yafada ibrahim yace tun dazun yake tsaye ai yana kallonka . Watau wanan gari gashi dai babbane cike da jama,a kuma amma kullum basu wayewa su kasan abinda ya kawo hakan yace ina zansan hakan ni dana fari shigota yau din . Yace gargajiya donsu har yanzu gargajiyansu yana nan basu yarda sun dauki akidar nasara sunsawa kansu ba aikinsu ke nan noma da kiyo komai arzikin mutum ata wanan hanyar zai nuna halinsa. Gaga kuwa ba zasu taba cigaba ba matukar basu yarda da nasara ba a rayuwansu gargajiyace tsantsanta a garin nan ka duba ko tsarin shigarsu mafa dabanne kuma kowa da irin al,adansa wajen nan. Hakan yafi masu sauki kallo daya zakai masu kagane basuyi sakaci da addinin su ba har yanzu yawan kabilu kuma ai duk zubin fulanine garesu ko larabawa. Haka sukai ta hira tsakaninsu suna jiran lokacin da zasu fara gabatar da shirin nasu don komai a yanzu hada lokaci kadai suke jira.
Chapter 7 · 0% Book details