← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 306

Sashe 192

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka kan kallo daya zakiyi min kisan nasha kuka a wanan wunin don yadda idanuwana sukai hulu hulu saboda kukan da nake kebewa inyi, Tare da tunanen duniya kala kala dake sauka min a zuciyana game da halin da yaya Jafar din yake ciki. Ina zaune nayi shiru a gefe tabarman dasu mama ke zaune sama bayan mun idar da sallah la,asar nagama maman tudun wada ta miko min kofi cike da fura har da kankara a sama . Kaina girgiza alaman a,a don banson komai a lokacin take fadin maza karbi kisha ina kule dake tun karyawan safe baki kara saka komai a cikinki ba yar nan. Masu fadin suke dashi don suke da diya dashi aun zage nan suna ciye ciyensu a gaba kowa balle ke din da sukewa arashun baki aje ko kwai a tare dashi ba balle ki fisu nuna damuwa sun zage suna kai abu ga bakin salatinsu. Maza ki karba kisha ki danji nauyi a cikinki kinji Allah ya kareki da takaban kuriciya da suke maku fata hakan don yafi komai daci da muni ga ya,mace . Hawayene suka sulalo a idona take fadin ki daure ki daina wanan kukan haka Allah ya tada kafadan mijinku yasa hakan zakan jikine a garesa. Karbi maza ki shanye ba a jinya da yunwa don saika fadi mai ciwo yazo ya mike Allah ya tsare dole na karba nasha din datace min saidai ban iya shanyewa ba na rike sauran a hannuna take fadin maza na shanye na miko mata kofin . Dole na kara kurbe sauran ban kaiga idawa ba Asmau ta kwala min kira da nazo daga kofan dakin hakan yasa na aje kofin da sauri na mike tsaye na nufi dakin . Don na fito saboda karmu saida hali a waje don yadda take nunawa lokacin dana shiga dakin ko abu zanyiwa yaya din zata taso da sauri tace dani na bari kawai ai zasuyi mai ko idan na dauki abu zatace na miko mata abin. Ganin hakan yasa na fito daga dakin don zuciya bata da kashi zan iya kasa hakkuri na biye mata muyi abinda ba daidai ba har mutane suji a tafi damu a baki. Koda na shiga dakin na zata wani abune sai take cemin wai na duba ko ya sake bata jikinshi wani kallo nayi mata mai nuna baki isa ba. Kin fimu karfin hali yasa muka kiraki Asmau ke fadin hakan gareni nace na zata ba saini ba zaku iya hakan ga mijin ku ai. Ke don mun kiraki kada ki fadawa mutane maganan banza don Allah idan ba zaki iya ba kice ba zakiyi ba kada ki kawowa mutane wani zancen banza a nan ? Banda lokacin ki don haka kiyi haushin ki ke kadai dama kin saba ciwon nasa aida alaman ba damuwanki yayi ba don da baki zauna kina damunsa da waya haka ba akai. Ashe kinji zafin wayan da nakeyi din inkin isa kizo ki karbe wayan insan kincika yar jin haushi kaji min yarinya da zancen banza har wakike inbashi dayaga abin banza ya nace akanki ba ? Subbahanallahi dama nayi tunanen hakan ai yasa na biyo ku, yanzu yarinyar nan har bawan Allah nan yana kwance haka cikin wanan halin ? Amma baki saduda da wanan halin naki ba sai kin dagawa mutane harshe a nan kuma ? Muryan mamace data biyoni bayan shigowana take fadan hakan tana tafa hannu don bata jini ba saiba din ta sama tana fada min maganganu a bakinta lokacin. Wani daga harshe nayi yanzu kuma mama ita har waye da zata tsaya tana fada min magana akan abinda zanyi yaushe ta samu wanan power din take ganin takai ? Amma kin kai sakarai ashe ? har yaushe wanan taga lokacin fadan wani magana gareki a nan yarinyar dake ta faman darzan kuka tun dazun a waje . Gadon da yake kwancene ya fara jijiga gaba dayan mu hankalin mu ya koma kanshi hakoransane ya datse a waje daya yayin da idanuwansa suka firfito waje ma,ana dai ya kara shiga wani sabon hali lokaci guda kuma. Ko salatin mama ya isa ya rudamu a lokacin inda Asmau ta fita waje da gudu tana neman taimako ga mutanen dake zaune waje cikin rudewa da tashin hankali. Ba maza a kusa iya mu matane da muka cika asibitin a lokacin sai salima data hari dakin likitocin hankali tashe don kiransu. Rasa me zanyi nayi saina tuna da dan anty salma ya samu attack irin hakan yadda mukai masa a abuja da sauri na juya na dauko spoon na nufeshi ina kokarin bude bakinsa na tura spoon din ya datse tsakanin harshensa da hakoransa. Kanshi yana saman jikina muryata a cikin tashin hankali na soma fadin don Allah ku rike min kafansa daga mama din har ita saiban sun kasa hakan shigowan Maria da Anty Barakha ya taimaka min suka rike kafafuwan nasa dake halbawa. Innalillahi nake maimaitawa saiga likitocin sun shigo a rude nurse suna fadin a rage daga dakin a fita don koke koke da yai yawa a lokacin dakin duk kowa na tsaye cirko cirko a cikin tashin hankali. Ruwan sanyi ko kankara nake fada ina nuna hanyar waje likitan ya kamo hannayesa yana dubawa har lokacin yana kwance shambal a jikina. Ruwan da nake fada din suka miko min a daidai kanshi na manna ruwan sanyin lokaci guda ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi ya daina wanan gurnanin da yakeyi da farko. Dukkan mu matansa mu ukku muna tsaye a dakin a cikin tashin hankali har likitocin sukai mashi abinda zasuyi din ganin ya lafa suka soma magana a cikin fada. Ba mun fada maku a daina shigowa ba haka da yawa dakin muna son ganin farfadowansane a ko wani lokaci zai iya yuyuwa yana jin komai saidai nisan fita hayacinsa da yayine ba zai bari a fahinci hakan ba zai iya jin wani magana da zai iya daga mashi hankali kuma har hakan ya faru kunga ciwon yana son canza sabon sallo kuma ke nan. Na yarda da maganan ka likita don matar nan tasace ke sa insa a dakin lokacin da abin ya faru kaga ke nan zancen ka gaskiyane ke nan a nan mace ke fadan hakan. Kuka saiba ta saka mai karfi tana fadin don kawai ba a kaunata za ace nice nayi sanadin hakan ya faru ya zata fada min magana inki ramawa don ina tsoronta ko me ? A nan kowa ya raina mata wayau don fahintar itace silan faruwan hakan ashe a lokacin da mama ta fada. Anty barakha ke fadin indai hakane aisai duk su fita wallahi tunda ba zaman Allah da annabi sukeyi a nan ba zasu kashe muna dan uwa da bakin kishinsu kawai ? Ya zama dole duk su fita likitan ya kalleta yace ita wanan na zaune bida gadon data bashi taimakon gagawa ina matarshi ce ? Yana da kyau a barta a kusa dashi na fadawa brother nasa dazun don tana taimakawa sosai wajen abubuwa da dama ko yanzu badon tana wajen ba da zaiji ciwo sosai wallahi. Don zai iya fadowa daga gadon haka kuma harshensa zai datse din ya ja masa wani matsala babba kuma sabo amma taimakon data bashi din ya taimaka muna sosai a yanzu wajen magance matsalan don haka abarta a tare dashi please . Amma kowa ya fita daga dakin nan a yanzu sai mutum biyu kawai za a bari a ciki tare dashi da zasu zauna su duba halin da yake ciki. A daidai lokacin kuma su yaya Auwal suka shigo a rude don an kirasu a waya ana sheda masu halin daya shiga din a lokacin suna wajen karbo maganin da ya habu yai magana a kai. Ankara masu bayani ya isah bai tsaya likitan yakai karshe ba ya soma magana yana fadin amma na fada ai kada wanda ya shiga bayan amarya saike mama din me za a barsu su shigo har haka ya faru ? To ya zanyi inyi magana yarinya tana batun zagina don kawai na fada mata gaskiya ku yanzu ai ku tsawata mata ta daina kila amma halin yarinyar nan ai baiyi ba wallahi. Kishi har mutum yana kwance gadon asibiti ba zaki saduda ba yanzu da likita daku kuka fada ai zata fahinta ko ? To kuji don Allah duk wanda yazo ya gaidashi ya fita don ba zamu hanaku shigowa duban mijin ku ba amma a shigo a tsanake a fice daga yau don ba zamu lamuci rashin hankali ba a nan lafiyan dan uwan mu muke duba a yanzu ba kishin banza ba a nan. Wanan abinda ya faru yasa jikin kowa sanyi har saiban da take jin take gani mamata lauya mata laifin komai a kai duk da tasan ba gaskiya bane nice dai na fara gasa mata magana gashi kuma Asmau taki magana har lokacin sai kukan da take faman yi akan laluran mijinta din. Basu jima ba ganin ya samu barci ya koma normal sukayi sallama suka koma gida nikan ina asibitin tunda naga maman tudun wada ta kama min na samu shiga a idanuwansu kishi ke nan dama. Da kwatance kawu dauda suka tsaya a wani gidan zana dake can dan gefen garin wajen dake dauke da wasu manyan itatuwa dake karawa mazauna wajen ni,ima. A gaban gidan ya tsayar da motarshi yayin da mutanen dake zaune a innuwar suka zubo masu idanu suga masu fitowa daga motan. Kawu ya fara fita har hulansa na faduwa kasa kafin ya bude bayan motan iya ta sako kafa ta fito tare da mama shi yaya habu shine ya fito karshe suka nufi wajen mutanen bayan ya rufe motar tashi da key. Kawu ya fara gaidasu suka amsa tare da masu sannu da zuwa da yaya hanya bayan gama gaishe gaishensune yake fadin don Allah Tuni fa da cewa matar kamar yadda ake kiranta dashi a wajen. Wani daga cikin mutanen ne yace wai Tuni kan ai ta dade da barin mu saidai yarta kudidi ke aikin a yanzu tana ciki in wurinta kuka zo? Innalillahi iya ta ambata tare da fadin shike nan dauda son kanka ya halakamu ga baki daya yanzu kuma ya habu yacewa mutumin kana nufin bata raye yanzu ita
Chapter 192 · 0% Book details