Sashe 269
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zan iya cewa cikina a yanzu yakai wata takwas a jikina a lokacin kuma zancen services din mu ya fito haka na shiga na fita na samu result dina yayi kyau. Wanan daman na ciki akai amfani dashi banje ko ina ba ga sha,anin bukin saratu wanda ya taso a yanzu don mijin data samu kamar a shirye yake da zancen auren . Don bai tsaya jan wani lokaci ba duk abinda ya dace ayi na al,adan aure yana gabatarwa ba bata lokaci wanan yasa hjyn rawan kai don ganin tayi sa,sn mijin aure. Don ita salima mijin bai karasa ginan shi ba don shine ba za a hada bukinsu ba a cewan mama wanda ya shirya ayi kawai kowa da sa,anshi yake zuwa duniya dama. Wanan yasa suka tsayar da ranan aurenta ita kadai ba tare da yar uwarta salima ba tunda mijinta bai shirya mai karatu dama na fada maki yarone kusan sa,an juna suke dashi a cewarsu alhalin kuma ya girmeta da shekara biyar shi din. Don dai basu sone suke fadin hakan akanshi wai yan sa,a guda suke da saurayin nata ai bata damu ba tunda tana son abinta har ankai ga zancen aure yanzu tsakaninsu. Ni fargaban haihuwa da yadda nake jin labarinsa ya dameni a yanzu ba wani zancen auren saratu ba can donko na sa kaina ba ama yi dani din don me zan matsa kaina da zancen abinda bai shafeni ba. Saidai duk da hakan ban tsira ba a wajen matar yazid nake ji wai nice ke zuga yaya kada yayi mata abin arziki na hanashi kashe kudi ga yar uwarshi kiji alhaki fa don Allah yar uwa ? Ni dako zancen bamu tabayi da yaya ba wai amma mama ta dauki laifin komai ta dora akaina kuma yanzu koda naji zancen ban damu ba saboda nasan karan tsanar da mama ta dora min a kai tun shigowana a cikinsu. Yanzu nagane taso tayi amfani dani kawai inyi ta bautawa rayuwansune kawai a baya bata so zancen aure ya shiga tsakanin muba da danta shi kuma sai ya shamci kowa yayi abin ta baibai ba tare da sanin kowa ba. Zancen kayan electronic sukazo nai dashi yake fada masu har kudinsu ya bada don haka shi ba zai kara komai ba su barshi da abindake gabanshi na haihuwan matanshi kuma. Daga wanan zancen ina ruwan zafi su sakani daga uwar har yar nasha zagi a bakin su ko ina sai batani sukeyi wai na hana yayiwa yar uwarshi komai a yanzu. Wai kuma ashe ya bada kudin saitace gadon da za a sai mata bai mata ba shine mama ta biye mata suka sai gadon da takeso kudin ya kare gaba daya yanzu suka koma suna kame kame . An lalubo Habu yabada dubu dari uku sukara shi kuma yazid yace ai sun san baida kudi tunda da mama aka hada kai kawu ya cinye mashi kudi ta kuma hana yayi magana. Haushin hakan yasa suka shiga wani rayuwa na tashin hankali a lokacin su a zatonsu komai yaya J zai mata sai gashi ya make hannu yace iya abinda zai bayar ke nan ya kuma basu don yanzu ta kanshi yakeyi shi. Ga buki sai karatowa yakeyi kamar yadda ko wani aure kan kankama har dangin ango sunzo sun kawo lefe a family house dinsu wanda mama ta koma can a lokacin aka tari lefen da ita . Tun wajen kawo lefen tsegumi ya fara ana fadin da gani yan kauyene don ba wata wayayya a cikin matan da sukazo din . Mijin kan na nunawa a cikin tsara saidai haline ba mai cewa ga halinsa tunda ganinsa akayi garin yanzo aiki kuma baifi shekara a garin ba suka hadu. A cewarshi itace ta biyu don haka ake fadawa kowa a ta biyu zata shiga gidanshi din ni dai ina gefe ban sa kaina ba kamar yadda ba a sani ba. Na dai sayi zanin gado masu kyau manya guda biyu a wajen anty salma wanda zan bada gudun mawana ga bukin har kuma sun iso a hannuna na aje. A wajen mama nake jin wai yaya j yaje kaduna don yar wajen Saiba da bata da lafiya yarinyar ta koma kamar sikila yanzu . Shine mama tace wai ya dawo da uwarta su dubata a gabanshi maman tudu ta dora da cewa kinga ke nan tana son ayi bukin yarta tana gidan ke nan ? Duk da naji wani iri a raina ban yarda na bar abin a zuciyana yadda zai dameni ba yima nayi kamar ban san wanan shirin da akeyi ba na sharesu muna dai zaune kamar yadda muke dasu duka har shi. Asmau cema suka kwasa dashi sosai da zancen ya fito cewa Saiba zata dawo gidan har sukai fada yace idan yayi niya ita bata isa ta hanashi ba . Wanan zancen kuma yazo min shima na nuna kamar banji ba saidai a wanan karon na kasa daure hakan tunda nima mutym ce mai jini a jika ai. Na danyi fushin hakan kuma ya fahinceni saidai tunda banyi mai magana ba shima ya shareni akan zancen ya nuna ba komai. Ranan daya dawo gidan muma ban bashi wani kulawa sosai ba kamar yadda na saba bashi abinci kafin ya dawo daga sallah na aje mai komai na koma dakina na kwanta. Ina jin motsinshi daya dawo ya zauna falo yana waya amma ban fito falon ba yanayi yana kallon kofana har ya gama yake tambayan Biba ke ina antyn ki take ? Tana daki uncle naji muryanta tana bashi amsa lafiya take kuwa ya tambaya yana mikewa naji tace in dai ba yanzu ba lafiya kalau take. Mikewa yayi ya shigo dakin ina kwance kasa da tasbaha a hannuna da nake ja ya tsaya daga kofa yana fadin yaya dai lafiya kike kuwa ? Na dago na bashi amsa a takaice kamar yadda Biba ta fada mai don ba halin karya gareni yanzu nace lafiya sai yabini da wani irin kallo na shareshi tunda na bashi amsan. To yaya abinci fa ya fada a inda yake din nace yana falo na aje ma yayi shiru kafin yace ba za a bani ba yau ke nan ko ? Nayi shiru can naji yace bakiji me nace bane kin kyaleni yana falo na ajema ai na fada kamar a hasale hakan yasa ya karaso yana fadin wai lafiya kike kuwa Rahama ? Lafiyata kalau nace maka ban dai jin tashine yau Allah ko yau ban samun gata ke nan nan ma ban bashi amsa ba na kyaleshi. Ya dan jima tsaye a kaina yana kare min kallo kafin ya gama nazarina ya tabbatar da lafiya din nake sai naji ya juya yana murmushi ya fita. Har yakai kofa yake fadin idan kin gama saiki taso ki ban abincin ban amsa mashi ba ya fice ina jinshi ya jima a wajen zaune naki tasowa in sameshi din. Saida na tabbatar daya gama ya shige na fito don kawar da kayan na kwashe zuwa kitchen a lokacin na farga da kamar bai taba kayan abincin ba kenan haka na nufin baici ba ko ? Na bude warmer din abincin naga bai taba ba nima na shareshi shiya sani tunda duk kyautatawan da nake mai bai gani yafi bukatan ya dawo da yar cin mutuncin matarshi azo a dora inda aka tsaya tunda ba barin halinta zatayi ba. Na juye abincin nasa a fridge don kada ya lalace na koma dakina na kwanta ban ko tayar da Biba tazo dakina mu kwanta ba yadda muka saba da ita idan baya gidan. Barci ko a ranan rabi da rabi nayisa don haka bai taba faruwa a tsakanin mu ba inba lokacin da baida lafiya din nan ba sai wanan karon. Washegarima ban lekashi ba bai fito ba har na kare abin karyawa na aje mai na koma daki nayi wanka na gyara jikina na kwanta ina jin biba ta gama gyaran gida har ta saka kamshi yana tashi na lumshe idona tagama shirinta zuwa school lokacin ta shigo dakina tana fadin anty nagama zan tafi. Hakan yasa na bude idona da sukai ja a lokacin don bacin rai dana sakawa kaina ina fadin ga kudin motarki nan dana kashi saman mirrow ta nufi wajen ta dauka. Da yake tayi wayau a yanzu harta dan juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin anty lafiya kike kuwa ko jiya uncle yana tambayana da bai ganki ba nace ban jin dadin jikinane Biba tayi min sannu ta fita. Ina jinshi ya shirya ya fito ya leko dakina ina kwace saman lafiyayyen gadona daya sha gyara na harde kafa nayi makari da hannuna na rufe fuskana. Ya dan juma a tsaye kafin ya juya ya fita can naji karan motarshi ya tayar ya bar gidan na sauke ajiyan zuciya ina jan tsuki. A lokacin yadda nake jin haushinsa a zuciyana komai zai faru ya faru din tsakanun mu tunda ba kwanciyan hankali yake kauna bashi. In mama bata damu da kwanciyan hankalinshi ba aishi yasan abinda ke nan da zai biye mata don kawai taga farin cikin mu ya ragu a gidan. Tunda yanzu tana zaton rashin Saibane duk ya jawo mata wani matsalan da take ciki na rashin samun hankalin danta yadda take son ta mulkeshi. Sunce da Saiba tana nan wani abin dole yayi don dole ko yaushe yana gidan ai amma ita Asmau da ita da babu duk dayane a wajenshi tunda bata maida kanta abun kwarai ba a wajen kowa. Shigowan Aminu da yayine yazo ya tsaya daga kofa yana fadin mummy ina kwana yasa na fito falon na zauna a tare dashi yana karyawa yana ban labarin zirga zirgan da yakeyi don cika takardunshi a school din . Bayan Aminu ya gamane nan ma ban shiga daki ba nayi zaune a falon lokacin ya shigo Aminu ya gaidashi ya mike ya fita ni kuma nayi zaune ban dago kaina bama balle in gaida shi. Abinda yasa nake baki wanan labarin shine wani lokacin mu mata idan haka ya faru bamu tsayawa mu duba mu,amulan mu da namiji akan ai zancen bai shafemu ba shiya shafa makin mu kara kyautata hakan sai mu barar da daman mu daga wajen jan