← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 302 OF 306

Sashe 302

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kame tana fasin ta zubo mashine tace wani ai tun jiya na dawo garin ina gidan Rahama can na sauka. Tayiwa bakina abin kari sun karya har sun kama hanya sunce sun wuce kaduna tun dazun nasan kona kasu nan takaici kawai zaki barni dashi ace yara kananu sai wajajen sha dayan rana suke karyawa kina kwance kina barci don baki damu dasu ba ? Yaya ban damu dasu bafa kace ko nayi abin karyawa tun dazun karshenta baci zasuyi ba cikin tsawa ya hauta da fada yana fadin nasan maganin ki yaya Auwal zan fadawa shi zai dauki mataki a kanki. Da sauri tace yanzu dai ai na dinga tashi da safe ina hada masu bashike nan ba ka kaini kara wajen yaya Auwal kasa yazo har gida taci min mutunci ga banza. Fita yayi ya kama hanyar gidansu mama da ita ya fara cin karo zata unguwa ganinshi yasa ta dakata tana tambayan yaushe ya dawo yace jiya da dare. Tare suka shiga wajen iya suka gaisa da ita Salima ta fito suka gaisa har tabada baya zata koma daki tayi brush ya dakatar da ita yana fadin yaron nan kabir yana gari ko yayi tafiya ? Yana nan yaya kice yazo karfe hudu ina nemanshi yakira layina yaji inda nake lokacin ta amsa da to yaya tashige don kimtsawa ya dubi iya yace zaman salima da Nafisa a gida yana damuna iya ? Ina son ayi aurensu a huta aji da wa yanda ke tasowa yanzu kuma ita Nafisan tana da mijine yarinyar da uwarta ta koya mata kitihi iri iri wa zai aureta ? Haba dubu kikan fara maganan ki ke nan nafisa dince da kitihi har kala kala haka ita wace ba a koyawa ba tayi auren ne ina mamaki gaka da abin zagi a gindinka kaje zagin nawani ? Irin abubuwan nan tambayan bawa sukeyi a rayuwa ke da girmanki meye na fadan hakan akan dan wani don Allah kinsan nufin yaron nan akan auren nan akan yaran nan daya fada ? To iya nidai bada wata manufa ba fada ba din Allah dukkansu aure zasuyi kwanan nan ita saratu bagata can gidan mijinta ba yanzu an huta da ita. Wace saratu saratu saratu kan na dakin uwarta yanzu ka ganta tashigo gidan nan tace zata gidan kawarta a kwashe mata kai. Saratu fa iya garin yaya ta dawo gida kuma iyan tace ka tambayi uwarta ita tasab dalili nayi magana tunda mijinta ya bugo ta koma ance ina nafito. Ya kuma turo abokinshi uwarta tace bata komawa sai yazo ya juya wajen mama din yana fadin mama yaya akai haka kuma ban sani ba ? Ta yaya zaka sani tunda baka nan yau kwananta goma sha daya da zuwa miji ya dauketa ya kaita kauye ya aje cikin matanshi ina saratu zata iya aikin yawa da sukeyi ? Mama ba aure taje yi ba su wa yanda ta sama ba haka suke zaune dashi ba tunda suna son mijinsu ta tareshi da fadin sai ta zauna wahala ya kasheta ke nan ko ? Mama dakata don Allah kin taba jin inda wuya ya kashe mutum don Allah ita mace fa da hakkuri akasanta ita dabance a cikinsu daba zata iya hakkuri da mijinta ba ta zauna yadda kowa ya zauna yana hakkuri ko tafi sauran matan nashune da suka zauna su ? Ina an fada mata tace tana iyawa karya ake mashi saida na zauna daku kafin duk su yaya su saka baki cikin maganan tana iyawa tace min tana son shi san nan yanzu zata dawowa mutane gida don tana yar iska uba me tadawo yanzu ayi mata to nan ? Kana magana kamar baka fahinci mutane ba ina saratu zata iya girkin mutum kusan dari don Allah ? Amma mama ita tace tana sonshi ai yau din nan zata koma ai tasan yana da iyayye yana da mata da yara tace ta amince ta aureshi mu zata dawo ta rainawa wayau yanzu ? Irin rainin wayau da na guda ke nan gun Asmau don nasan sakarauce ta mayar da kanta sha,shasha saboda son jiki nazo da baki dole gidan Rahama naje na sauka jiyan. Ina zakazo da boka a barshi da yunwa yanzu dana biya gidan sai yanzu na samu wai tayiwa yara abin kari zasu karya yaro za a bari da yunw har wanan lokacin saboda sha,shancin banza da suka dorawa kansu. Dama nasan za a rina wanan daban tsiyan da suke taruwa sunayi a wuni ba mai iya yiwa kansa abin kwarai yanzu gashi duk ta dauka in anyi magana mama kice an matsa mata ba a kaunarta ina tsiya ina girki ga mace girkifa za ace ya koro mace gidan miji idan ba tsiya da samun waje ba. Naki bai hadaki da mijinki ba sai zancen girki din Allah mama ta amsa da fadin ai shima ya shafi mijin tunda yasan inda ya dauketa da zai kaita kauye yace sai tayi kalan aiyukansu. A ina ya dauketa gidan attajirai ko gidan sarakuna naga dai har gobe gidanku suna aiyukan hannu na hausawa iya ta fada yanzu inane yar nan Nafisan da kike zagi ba zata iya shiga ba ?. To taje kauyen ita amma saratu bata komawa kauyen nan sai dai asan abin yi gaskiya kauye kan ta fito ke nan cikinsa in sha Allahu. To shike nan mama tunda haka kikace saidai ku sani duk wani zance na saratu daga yau bani ba ita wallahi ta zauna gida tunda kunga hakan yafi maku. Ya mike iya ke fadin kai Alh dawo mana ya juyo yayi dan murmushi yake yana fadin ke kuma matar Alh ba don bana in sha Allahu ga kujeranki ga tawa iya muna gaban jirgi da yardan Allah ni dake. Kai kai kai kar kasa in fara shiri don Allah wanan ai ba karamun fata bane kayi min Allah dai ya nufa yasa hakan abakin yan amin. In sha Allahu iya haka nake da niyan dake da uwayena dukansu hudu in Allah ya yarda zamu keta hazo muje dakin Allah mu ziyarci kabadin Annabi mu sauke nauyin da baba yayi niya Allah bai nufa ba. Kace in fara shiri ke nan dai Jafaru yace iya fara insha Allahu makkan bana dake ciki da yardan ubangiji kuwa iya in ranmu yakai. Ranmu yakai jafaru ranmu yakai Allah yasa muna da rabon ganin hakan da rayuwan kai naji dadun wanan fatan ko ince albishir din Albishir dai iya. Su kishiyoyinki na sayowa ko wacensu mota ita Asmau daya ita kuma Rahama daya na tausan gaba uwargida zata makka a taushi kirjinsu ta kwashe da dariya tana fadin aiko uwargida ta kosa tunda motace tausan gaban kishiyoyin ta. Mama na gefe sai dan murmushin take takeyi saida raga alaman fita zaiyi daga falon race wai da gaakiya kakeyi ne yace insha Allahu mama haka nake fata ku sauke farali a banan nan kedasu mama da su yaya Auwal inda hali zan hadaku da barakha din iya kuje. Allahu Akbar lalai dan nan arzikine iliya dan mai karfi ke nan yaro ya zo da arzikinsa da kardin Allah ,,,, ji iya kuma ana zance wani dan kike magana tace mai babban suna mana wani dan ai haihuwansa alherine a waje dubama ga yadda aka samu yaron nan koshi ya isa yasa mutum ya fahinci hakan . Fita yayi ya barsu bai kara zancen saratu ba fitan da mama batayi ba ke nan a ranan ta kira yaya barakha tana sheda mata abunda ya faru barakha din tace kai amma jafar ba abunda za ace mashi. A yanzu jafar din ya juye mata kamar bashi ba tana jin shakkunsa da nauyi ba kamar jafar dun baya data sani ba da rake iya tankwasawa kota umurceshi yabi. Tasan yasan abunda ke nan akan kawu amma ya share ya nuna bai san da hakan ba ko zancen bai dauko mata ba amma zata kyaleshi taga gudunsa. Tasan ba zai taba kyale kawu di yazid ya wullakantashi ba ai tunda daga yazid har habu sam basu jin zamcenta yanzu jafar din ne mai dan dama dama a cikinsu. Yanzu kuma shima ya juye har yana son ya fisu gashi ta kasa gane matsalan daga wajenrta yake balle ta gyara Allah yasa mu dace amin. Sai washe gari yabawa kowa motarta ya fadi kalan tace Asmau ta zaba tace baka take so tabar min farar munyi mai godiya dani da ummah har da mariya ta kirashi tayi mai godiya ya kuma ji dadin hakan sosai nagane hakane da yake cewa ke kina ta wahal da mutane da kira halal zaki saya masu credit ne ? Zancen makkasu ya tabbata wurin mutum goma ya biyawa makkah da zasu tafi har labarin irin tarin dukiyan dayasamu a yanzu yakaiwa saiba sai gashi ta fara bugo mashi waya tana ban hakkuri. Kashedi yayi mata yace kada ta sake kiranshi idan ba haka ba zai kaita ga hukuma ayi masu tsakani da ita amma hakan baisa ta daddara ba. Don sai ta fito da sallon kiran wayan taba yarta idan ya dauka tace daddy yaushe zakazo ka daukemu bata san tsiya ta kullawa kanta ba a wanan sallon . Haka yasa ya tura su yaya Auwal su karbo yarinyar a hannunta nan kuma tace bata isa ba shima yaya Auwal yace bata kai mashi can ba dole tabada da yarinya don bai yarda da tarbiyanta ba. Dole mahaifita yasata gaba ta mika masu yarsu suka dawo da ita kaduna can gidan Asmau aka aje yar don yaso yace a wajena zata zauna mama tudu tace dashi ko kusa zaman yar nan yana iya kawo matsala tsakaninka da yarinyar nan kaga ba shiri take da uwarta ba. Ka barta can ta zauna tare da yan uwanta tunda dasu ta saba dama ita yar hakan zaifi mata dadi yace mama niba ra,ayinta naso ba don ta samu tarbiyan da nakesone ai tace barta dai can tukun na hakan yasa dole da akazo da ita ya barta gidan Asmau din.
Chapter 302 · 0% Book details