Sashe 106
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
3️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kwance nake har lokacin cikin gajiyan da ba zance ga dalilinsa ba ina dai dangata hakan da fitan da mukayi da anty salma yasa jikina weak a lokacin.
Nayi mamaki yadda wanan ya narka kudi aka hada mashi wanan lefen a cikin kwana biyu rak kayane dai aka zuba wanda zaki dauka cewa macen ba zata taba neman wani abu mai suna sutura ba ko kayan kwaliya.
Gaskiya maishi ba karamin kokari yayi ba hakan ko banjitane ko kuma so an dai narka nairori a wajen nan gaskiya irin tunanen da nakeyi ke nan a zuciyana naji an turo kofan dakina.
Muryan anty salma danafi zaton itace don ba kasafai yan aikinta ke shiga dakunan kwanan mu ba saida wani dalili mai karfi.
Wai kwance kike har yanzu na yunkura ina mika nake fadin haka kawai naji duk jikina ya mutu nasan gajiyace na mike ina gaida ita.
Mama ta bugo waya muje yanzun nan tana neman mu dani dake jin abinda ta fada yasa na kallota da sauri ina fasin mama kuma ?
Lafiya dai ko anty Salma tace ai kinsan halin mama kilama ba wani zance bane tana dai son ta gamune kawai tace mu taso.
Murmushi nayi don ko yana yuyuwa haka din ne sai muje tace ayya yaran nan ban ganku ba kwana biyu kuna cikin gaein nan kun shareni ko ku nemeni ?
Hakan yasa na tashi na shirya da sauri don na fahinci a shirye anty Salman ita take a lokacin ba wani dogon shiri nayi ba wasu dogon riga da ya tsaya iya gwiwa tare da wandonshi sai gyalen dana rufa iya wuyana tunda daga mota sai mu shige cikin gidan mama din don haka ba saina tsaya wani bata lokaci ba.
Karshema zata iya sakani wani aiki a hakan yasa ban tsaya wani dogon gyara ba kodana fito anty na zaune tana waya tana ganina ta mike tana fadin muje ko tana mike yaranta.
Na dan marairai ina fafin kin rufo dakinkine anty wayata naso dauka a nan na barta tun jiya sai naji tace gashi na saka maki a jakata muje saina baki a can din.
Ba wani dogon tafiya bane don basu da nisa sosai da juna sai gamu gidan daddy din tun a waje na fahinci daddy yana gidan a lokacin.
Yan aiki keta kara kaina a tsakar gudan duk da yanzu gidan ba yawa sosai ko masu aikin su ukune yanzu ba kamar lokacin da mukai tamu rayuwan dasu ba da muka cika masu gida.
Mama fa ta tambaya tsohuwar tace tana gun Alh suna nan falonsa zaune hakan yasa muka nufi can naso togewa iya ita ta shiga sai ta juyo tana fadin muje mana kin tsaya kuma kai wanan bakar bafulatanan dai ?
Murmushi nayi don sanin sun rike wanan wasan ta fulani da barebari a tsakanin mu ko yaushe kuma har daddy suna tsokalan mu dashi.
Daga mama har daddy din suna waya a lokacin muka shigo abinda kunnena yaji mama na fadi shine ai gasu mun kirasu daddy zaiyi magana dasu daga baya sai inkirani kiji meke nan.
Ta kashe wayan ta dago kai muka fara gaisawa ranan fuskansu ba wasa a cikinsa don ko dan zolayan nan babu sai daddy daya mikawa dan salma hannu da yazo yaron ya leke a jikina.
Mama ke fadin karka kama gaye ka sake reshe kwana biyu ba zaka ganta gidan kuba dan nema kawai salma ta shafo kan yaron tana fadin ai tare zasu tafi zaria da anty salma ko ?
Akayi dariya muka zauna dai a cikin harshensu suke magana wanda duk zaman mu banda gaisuwa da dan wasu abu da muka rike har yanzu bamu jin yaren nasu sosai amma muna fahintar me suke fada da kanuri din.
Don naji mama na fadin ban sani ba tace a,a har yanzu dai bansan komai ba amma sai ban kawo a kaina suke magana ba.
Daddy ne ya ambaci sunana da Rahama hutu ya kare ko sai shirin komawa makaranta na dan dukar da kai ina murmushi yace to Allah ya taimaka na amsa da amin kawai .
To Rahama nace yar uwarki tazo dakene nan don muyi maki magana irin ta iyayye yau a duniya dai kin sani ko Abdullahi mahaifinku yana raye ni Adamu ina iya yanke hukunci a kan ku ?
Zama na gyara don nasan maganar kila a kainane zancen komawata gidan su Yanda da anty salma tace ba zan koma ba ke nan ta kawo gaban daddu din hakan yasa na amsa da baki da kai da alaman hakane.
Yace madallah ina son kiyi amfani da tarbiyanki da natsuwanki da iliminki haka kuma ki zamo musulma mai ruguman kaddaran da duk ta samu bawa ta rayuwa walau mai kyau ko akasin hakan ?
Na sake jin kaina ya kulle min lokaci guda har na fara tunanen ko nayi rashin wanine a lokacin falon yai shiru babu mai magana na dan lokaci.
Mama ta zuba min idanu daga inda take zaune hakama anty salma ke kallona cikin wani yanayi na tausayi sai duk na kara tsunkewa lokaci guda.
Yayin da suka fahinci tun bansan meke faruwa ba yanayina ya sauya tun soma maganan daddy a kaina.
Yadda duk na fara fita hayyacina tunma basu fada min kome yake faruwa ba kaina dago cikin yanayi na damuwa da alaman tambayan ku fada min kome yake faruwa mana.
Sai naji daddy yace kiyi hakkuri Rahama a matsayinki na musulma ya kamata ace kin yarda da kaddara mai kyau ko akasinta.
Don haka ki kaddara hakan da zan fada maki kaddaran kine haka muma iyayyenki bamu isa mu sauya maki kaddaran kiba Rahama ?
Kai na gyada a hankali haka kuma indai har kin yarda da mu iyayyenkine kinsan ba zamu cuta maki ba to ina son ki kara daukan hakan da gatan iyayye akai maki aka daura maki aure ba tare da sanin ki ba.
Zubur nayi na mike dakyau zaune ina binsu da kallo ga anty salma kallona ya tsaya sai naga tana min murmushi da a lokacin na fassarashi dana kiyayya a gareni.
Mama ta karba da fadin kakanku hardo ya daura maki aure kwana ukku da suka wuce da dan uwan mijin Maria yar uwarki.
Ina fatan zaki dauki hakan a kaddaranki kin dai san ba za a hada kai damu a cuta maki ba Rahama ?
Don haka kamar yadda daddynku ya bukata ki zamo mai biyaya ga mijinki haka kawai da zakiyi shine zaki nuna matsayin mu na iyayye a wajen ki yanzu.
Haka muma zamu san Abdullahi ya bar muna marayun Allah mun kuma runguma a bayansa .
A iya binken daddynku wanan yaron baida matsala asalima taimaka muna yayi a namu ganin da wani yazo wanda ba a sanshi ba ba asan halinsa ba ya aureki daga baya azo ana samun matsala kuma?
Hakan yafi muna kwanciyar hankali dake har mu don ansanshi ansan koshi waye haka kuma ki zauna gashin kanki yafi zamanki a haka hankalin mu kullum a tashe kanki.
Shi aure rahamane ga bawa alherisa yawa garesa don ba akanka kadai kaida kayi auren abin ke tsayawa ba yakan shafi har wanda baka taba sani ba.
Allah ya taimaka hawaye sun zubo min don sune saukina a lokacin da ace ban samu sunzo min ba a lokacin komai yana iya faruwa dani wajen.
Kinsan mu fulani da busashen zuciya toni a wajena wanan hawayen da suka zubo min sune saukina a lokacin saidai duk da hakan saida faduwan gabana yakaini ga sulalewa kasa cikin kaduwa.
Salma da mama sukayo kaina da sauri suna kiran sunana da Rahama Rahama haba dai wanan abin ai bakai har na daga hankali haka ba ke nan baki yarda da hukuncin mu da kakanki hardo akanki ba ke nan Rahama ?
Mamace ke fadin hakan cikin kaduwa da halin data gani a ciki shiko daddy namijine yana zaune ya harde kafa yana zuba murmushi kawai daga inda yake zaune yana magana a cikin yaren kanuri yake fadin.
Su kamani zuwa daki ba komai bane kaduwane zan sake idan zuciyana ya samu nasuwa amma a kira doctor zainab ta dubata.
Haka suka kamani zuwa dakin mama saman katafaren gadon mama din suka kwantar dani tare da kunna min AC dakin daya kara sakarwa jikina yanayin zazzabi sai gashi na fara rawan dari a hakan doctor din tashigo ta sameni kwance.
Allurai tayi min dama shine nasu tare da maganin da zansha indan watsake tace a barni in samu barci idan na tashi komai zai tafi in sha Allahu.