← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 306

Sashe 154

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kinji meta fada ai ashe baki cika yar iska ba tunda baki doketan ba a yanzu get out of side kafin ki kaiga abinda kikeso ki samu a gurina yanzu. Tana tsaye har yaci abincin yayi hamdala a gabanta yasha ruwa ya mike don ya fita a kofa ya tsaya baiji kunyan idon da yan falon suka kafa masu ba a lokacin. Nan ya tsaya tafito ya rufe kofan nasa dakinta ta nufa rai bace ta kira yar uwarta nan ta karfafa mata akan tayi hakkuri duk abinda zai mata don ya kureta kada ta yarda ta kara barin gidan har suzo. Zuciya dai bata da kashi duk maganan da yarta tayi mata haka baisa ta hakkura ba can dai ta sameshi part din mama suna magana kan zancen anty baraka din ta fado falon cikin fitina. Nan ya wanwanka mata mari duk da mama na magana ido rufe yake fadin shi zata kawowa rashin mutunci yana magana da mahaifiyarshi ta zo mai haka. Sai lokacin ta fahinci irin kuskuren da tayi don duk abinda sukeyi bai taba daga hannu ya duketa ba sai wanan ranan kuma a gaban kannesa dani da muke dakinsu muna kallon wani dinki da salima ta jawo mu gani. Abin dai ba dadi a lokacin wanan yasa ba a jima ba yace mu fito mu tafi duk da iya tayi mashi magana akan ya barmu yace yana son muje mu gaidasu mamane can family house din su. Dole iyan tayi shiru ita mama abu yai mata yawa saukinta ma shi J din daya kira anty barakah din ya bata hakkuri akan ta daina zancen ta bari zasuyi magana dashi daga baya . Wanan ya kwantarwa mama din da hankali saidai muna fita daga gidanne kuma Habu ya kirashi yana fadin kada yace zaiyi wani abu ya kyale yar tasu sai ta koyi hankali. Shima bai samu dogon magana a wajenshi ba saboda ranshi dake bace na daiji yace dashi zai kirashi idan ya sauke mu . Nidai nasan badon hudubar dana samu gun anty salma ba dana kade a wajen Saiba don yadda ta sakani gaba dani da mijin. Amma sai Allah ya taimakeni nayi amfani da wanan huduban na anty salma nacire tsoro da fargaba ina bata amsa ba tare da rashin kunya ba ko fitsara daidai da yadda tazo min nake daurewa ib dauki mataki a lokacin. Wanda ni kaina har mamakin irin daurewan da nayi din nake ji ina fuskantanta garan da garan gaba da gaba ba shamaki ko tsoronta. Mun shiga cikin gidan da kedojin da muka riko masu inda ko wani daki muka shiga muke aje masu sabulun wankine da omo sai manshafi dana hado dashi din. Ina dakin inna inda na yadda zangona dama tun kan na auri ya J idan nazo gidan nan muke dasu anty Nafisa kiran Maria ya shigo min. Da harshen fulatanci muke magana don su inna dake dakin zaune inda maria din ke tambayana ashe abunda ya faru ke nan. Yanzu take ji a wajen iya cewa Saiba tayiwa yaya rashin mutunci a kaina ya mareta har idonta daya ya rufe wai sun tafi asibiti da Saratu. Nan na fada mata abinda ya faru don ganin su salima ban samu mata bayanin komai ba har na fito a lokacin. Take fadin dama ta fada ashe duk ranan dana zo gidan saita wullakantani a gaban kowa gashi ni ban wullakanta ba ita ta samu duka haka. Inda take fadin yanzu ta shiga duba jariri ake fada mata abinda ya faru nace a cikin yarenmu na fulatanci ban taba bin kowa da mugun nufi a rayuwana yanda amma idan kace zaka bini da wani nufi akanka abin zai kare ai. Shigowan Nafisa har lokacin ina waya nan ta zube tana fadin ke kunbar gida da jidali Saiba ido ya kumbura saida mama tace a kaita asibiti ashe fada sukayi sosai har yaya na fadin zaman mama takeyi ai a gidan ba zamanshi ba. Kiji min mata wai kuma ashine take zaune bata tafi gidansu ba ko hakan aita wullakanta dai data sani ta bar zancen nan tayi hakkuri har lokacin da aka gama hidiman nan sai tayi abinda zatayi din. Amma yanzu har wanda bai wajen sai yaji zancen nan ta dauka irin bayane da take kada iskancinta yadda taso kuma a zauna lafiya. Wai ita Nusaiban ce ta tayar da fitina inna ke tambaya don ni tunda ta soma magana ban bata amsa ba nan take fadawa mahaifiyarta abinda ya faru zancen bai tsaya a nan ba don duk gidan kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa. Maman fambeguwa uwar gidansu mama Dubu ita ke fadin duk wani shashancin da matan Jafaru keyi laifin dubune. Don bata son a fada bata kuma yarda wani ya tsawata masu idan matsala ya faru haka kiri kiri suka tauye yarinyar nan Asmau a gidan bata da wani power matsayinta uwargidanshi sai abinda yar nan Nusaiba tace shine yanzu suke son ya faru da yarinyar nan. Idan Jafaru ya yarda aka hadashi da yarinyar nan bai kara samun mace irinta a rayuwanshi diba a yan watanin nan yadda shi kanshi ya koma ya samu natsuwa da kwanciyan hankali a tare dashi fiye da baya. Aini ina dauka tana hakane kan son da takewa yayanta din amma sai daga baya na fahinci wani abune na daban ga hakan kamar yarinyar nan ta asirceta za ace. Daga daki nake jiyo zantukansu irin na yan babban gida da idan an samu magana kowa saiya tofa albarkacin bakinsa inda na kula da rikon Biba da yaya ya dauko muna yaiwa kakan yarinyar dadi sosai. Sai haba haba takeyi da jikan nata duk da nasan an sakata daki an mata bincike akan zaman namu da ita duk da nasan ba zata fadi wani mugun abinda rai zaikai ga baci ba saidai wanda ba aka rasa kawai dan dole a samun hakan ga rikon da. Daga gidansu muka wuce gidan anty Rukkaiya taji dadin zuwan namu sosai bamu jima ba muka nufo gidan yaya Ai nan mukai magariba muka koma gida a cikin dadin rai don ya zauna da yar uwarshi sunyi magana ta fahinta kan yaya baraka da matsalanta inda muka bar gidan da shawaran da suka yanke a kanta inda yaya Ai da yaya Rukkaiya zasu can garin wajenta din duk wanan hukuncin mama dubu bata sani ba a lokacin. Saidai na kula da yanzu kamar yaya ya tsame kawu a cikin lamarinsu a hankali yake abubuwa bada sanin kawu din ba wanda a baya ba haka suke dashi ba. Tunda muka dawo gida ban tayarda zancen matarsa ba shima haka baiyi wani zance kan abinda ya faru din tsakanin mu ba. Ranan dai da dare yake fada min su yaya Ai zasu tafi gasau wajen anty barakah dan tarewan amaryanta da za ayi kada ayi babu kowa nata a kusa. Allah ya kaisu lafiya hakan kuma gaskiyane don ba dadi ace ba kowa naka kusa irin haka ya faru don koba komai zasu dan rage mata damuwa da zuwan nasu. Zanje gida in sanarwa mama koda abinda zasuje mata dashi don tunda safe ibrahim zai kaisu gobe in sha Allahu nayi mashi a dawo lafiya ya fita. A zuwa lokacin na sakankance dai kamar aurensu da Saiba yana rawa kamar yadda naji wajensu nafisa da salima shima kuma ya fada ranan a gabana da yace zaman mama takeyi gidansa aiba zamansa don haka tabar saka baki a matsalanshi da matansa. Na dauka a ranan zatayi yunkurin barin gidan don cin fuskan da yayi mata a gaban mutane sai gashi naji Salima da muke waya tana fadin wai Saiba ta samu yaya kan abinda za ayi na suna yace a gidana za ayi komai nasa da jama,anshi don haka zasu shigo su tayani aiki ke nan. Nayi mamakin jin ta saura a gidan ashe batayi fushin zuciya irin na mata masu jan aji ta tafi ba har lokacin wanan ya kara min wani haske game da zamantakewa. Don hakan ya nuna itace mai cutarshi bashine yake cutarta ba don da shine ke cutanta nasan ba abinda zaisa ta zauna tunda har hakan ya faru koma dai maiye tsakaninsune ba zan saka hakan a raina ba don tare nagansu bani kuma fatan a sanadina tabar gidan in sha Allah. Koda ya isa wajen mama yake sanar da ita cewa gobe da safe su yaya Ai da anty Rukkaiya da inna amarya zasuyi sammako zuwa Gusau wajen anty Barakha don suga halinda take ciki. Budan bakin mama cikin mamaki sai cewa tayi da dan nata akan me zasuje duk bai isa mu walwale matsalan ba sai sunje ba Jafar ? Kafin yai magana iya ta bata amsa da fadin keko dubu wani lokaci kikan yi abu kamar mara tunane . Idan su yan uwanta basuje sun nuna mata gata ba kece zakije da kanki kowa wanan shawaran da yaron nan ya yanke ko ita barakha din zataji dadin hakan ai idan ta gansu tare da ita. Hakan kuma zai kwantar mata da hankali don za a san tana da gata idan anyi mata hakan don Allah kadai yasan bakin cikin da take can ita daya take kumsa ? To shike nan idan hakan yafi ni a zatona iya za ai mashi magana akan kudin tane ya bata abinta idan anje ai sai ya dauka ayi na,am da zancen aurensane yasa sukazo din. Kaiya ni kikan bani mamaki wallahi dubu sai in rasa ina hankalinki ya shiga ki barshi da dabaran nan da yayi namijine fa yafi tunane abinda zaije ya dawo akan komai . Tunda kikaga ya shirya hakan dole akwai wani hikima da hakan ke nufi ai ga Barakhan dole idan za ai wata tsiyar ganin idon yan uwanta dole a raga mata ai . Banda abinkima Dubu yau in ba Jafar din da kuka samu kamar ruwan sanyi ba wa zai tsaya har yai hakan yadda kuka rufe ido ke da yayanki kuka so ku tozartashi gidan nan kan kudin nan . Gashi ai shi baici ba wani kato yaci a banza har da tukwaici ya dora maku dashi kuma ba yadda kuka iya dole ku barshi da kudin ko don haihuwan dake tsakanin su. Irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko da
Chapter 154 · 0% Book details