Sashe 266
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajajen shadayan rana muka iso gidan nida Biba da Aminu dana jawo yazo yaga gidan don ya sani irinsu Yanda sune marasa marmari irinsune masu batawa fulani suna. Sam bata da sabo ita bata da sakewa da kowa abu daine idan ance so to shi hana ganin laifine a wajen wanda aka jefa da wanan kalman. Don ko son da habu kewa yanda yasa shi bai ganin wanan halaiyan nata na daban da mutane ke fadi kamar ace komawansu gidansu su kadai a yanzu din nan . Ya kara nisanta ta da kowa yara kawai muka samu a falo suna waaansu ita kuma tana dakin kwananta muka tsaya nan muna sallama yaron ya ruga daki ya kirata shi mai wayau din kaeamin kuma ya tsaya yana kallon mu. Haka ta fito sinkinkin da ita tana ganina ta dan yi murmushi tana fadin ashe kune tafe sannunku da zuwa nima kwana biyun nan kina cikin raina wallahi. Ban kulata ba na juya harshe da yare inawa danta Abba yaron baima san inayi dashi ba don bai san abinda nake fadi da yaren ba na juya ina fadin amma kinyi sakaci da baki koyawa yaran nan yare ba nan gaba zasuji haushin hakan. Take fadin babansune bai so a koya masu yana fada idan yaji ana masu yare nace filatancine bai so kome ? Bata tanka min ba take fadin bari ta kawo muna ruwa ki barshi saidai su nikan a koshe nake ta dai mike zuwa kitchen dinta wajen fridge dinta sai gata da gora biyu na ruwa ta aje muna . Nan suka fara gaisawa da yaran kamar mintuna goma na mike da gaiya ina fadin zamu tafi dama munzo kawai mu duba sune. Haba Rahama tun yanzu ko zama bakuyi ba ina ce a nan zaku wuni ai a,a nazo duba yaran nan ne kwana biyu bangansu ba. Suma suna kewanki baba yace in ya dawo zai kaisu which means bada ita ba take fada min hakan kai tsaye to ni zan tafi zamu biya gidan yaya Ai mu gaida ita. Sai lokacin take tambayana waya kawoni nace Nape muka hau take fadin kuma yaya ya yarda to yaya zaiyi tunda ba zai hanani zuwa in dubaki ba matukar ina da lafiya ? Idan kinga ya hanani fitowa ya fahinci banjin dadin jikina shi kadai zaisa ya hani zuwa gidanki ko kuma yana jin jalin maza a lokacin. Dan kame kame ta farayi don itace ko yaushe take fadin mijintane yake hanata zuwa dubana ko tayi mashi magana. Daga gidanta gidan yaya Ai muka tafi saida mukai azahar muka fito zuwa family house dinsu mugaidasu maman tudu. Takuwa ji dadin zuwan mu din sosai don sabo a yanzu ya shiga tsakanina da ita duk da munci wani abu gidan yaya Ai amma saida mama tasa mukaci dambun shimkafa a wajenta. Ta sayo muna sobo mai sanyi mu kora sai hira take jana dashi bandai yarda na fadi wani abu mai muni game da mijina ba ko mahaifiyarsa. Mun jima na bata alherin dana rilko mata koda muka dawo gida mun samu ya rigamu dawowa halin mazane don ko yayi fadan dadewan mu sosai. Har in kaga yayi fada akan abu ransa ya baci da abin donshi nayi shiru na shige daki na sauya kayana zuwa kitchen don yamma da yayi muna lokacin. Har dare bai sauka ba yana fushi dani nidai ya dawo daga sallah na hada mai abincinsa na aje mai daki na koma nayi sallah dana idar kuma na kwanta abina. Daga falo ya kwala min kira nasan abinci zan zuba mai lokacin na fito na sameshi nima fuska a dare nazo gareshi ya dago ya dubi fuskan nawa yana fadin abinci zaki zuba min ? Nan ma banyi magana ba na duka na soma zuba mai abincin har lokacin ban cikin sakewa sai naji yana fadin kin san bake kadai bane zaki fita tun safe har yamma haka ? Idan jigila yaja maki wani matsala fa tunda jikinki ba karfine dashi ba har yanzu gashi ance ba,a son mai ciki fitan yamma ? Gidansu mama muka fito fa mun jima a gidan yaya Ai har kusan la,asar muna can gidan ta ya tare da fadin bandai sin hakan na fada maki nayi shiru. Munyi hakan da kamar kwana biyu ya sameni da zancen a gobe in sha Allah yake son ya koma can gidan ban nuna komai ba duk da naji abin a bazata. Kinsan mu mata ko yayane sai mun dan nuna halin kishin nan gashi kuma sati biyar cur yayi a gida dole ko kome naji in taushe a lokacin don yayi min ba zance ga kara ga ittace ba irin namu na mata. Donshi nace Allah ya kaimu gobe lafiya shiko gogan ya tsureni da idanunsa yana kallona ko zai fahinci wani abin daga gareni. Yaron nan iyayyensa basu ce komai akansa ba har yanzu donshi nake son a nema mashi makaranta ya fara zuwa a nan in kuma uban bai yarda ba ya koma gida gabansu. Me zai hana ya yarda tunda yaran ba damuwansa sukayi ba yanzu inda ya damu aida ya bugo waya yaji ya fada nayi magana a sama mashi gurbi a nan saiki fada mai ya aika su turo mai da takardunshi daga can gida. Naga ke kina son zaman yaron a nan iba haka ba niba zan barshi nan wajena ba saidai ya koma can gida wajen mama su zauna abinci daine Allah ya hore min in basu. Ai yiwa kaine dan yar uwarka ai dankane ba a san moriyan da za a samu ga hakan ba yace badai a wajen barakha ba kuwa a daiyi din kawai don zumunci Allah yace wanda ya yanke zumunci zai azabatar dashi . Donshi nake duba ina dan rage wani abu amma su suna ganin hadani da boka da malam din da sukeyine yake tasiri a kaina. Ita saratu yanzu naji ance ta turawasu yaya mai nemanta wani mutumin sokoto ta samu yana aikin banki a nan garin . Masha Allah nace ashe aure yazo ke nan tunda har yaje gida sai naji yace ita dai ta sani niba ruwana da zancen yar iska yanzu tunda bata son farin cikina. Bance ban mata komai ba amma ba dai irin na salima ba kan da sauri nace hakama ba zai yuyu ba tunda su biyune kadaiyi din a fitar da hakkinsu akanka. Wani haki take dashi a wajena yarinyar data hada min banga a tona min asiri ai duk naji komai shiyasa kikaga ban saka kaina a rikin kawu da yazid ba dukko yadda mama taso naki hakan dole sun kyaleni yanzu. Shi kawune bai kyauta ba ai tunda yasan amana aka bashi don me zaisa kudinsu gaba ya cinye har da aure da dukiyan marayu don Allah ? Murmushi yayi ya mike tsaye yana fadin ke aurema da yayi shiya dameki ai auren amman da matarshi tacine ya fita mata tanan . Da kinji abunda yayi da gudin aida baki kara kallonshi da daraja nace to Allah ya sauwaka ya fita yana fadin zaije family house dinsu a can zaiyi magariba. Nayi mashi Allah ya tsare ya dawo lafiya da haka ya mantar dani takaicin kishin daya fara min tukuburin a zuciyana . Don kodaya fita ban koma takan maganan tafiyansa ba sai zancen kawu da yayi min ne ya tsaya min a zuciyana. Ni dama mutumin yana da zubin munafukai inkin gashi haka kuma tunda ya fara sukan Yanda akan kwanciya asibitin ta na farko yasa na fara kinsa a raina. Lamarin yaya kuma nasan dole dai ya koma wajen matarshi dama tunda yanzu alama ya nuna ya samu lafiya sosai tunda na dukufa da mashi addu,oi da bashi makarun dana amsa a gida tun wancan lokacin da gardama yayi yawa na kwashe abina na boye sai yanzu nayi mai amfani dasu yadda akace. Don kiri kiri mama ta nuna a daina mashi amfani dasu tafi amincewa da wanda suke karbowa da kawu ko kawu din ya kawo shi kadai ayi amfani dashi. Kamar yadda yace din kuwa washe gari karfe biyar yayi muna sallama ya nufi can sai naji gidan ya koma min shiru a lokacin. Na dawo falo na zauna har akai magariba kafin na shiga dakina nacewa Biba idan ta idar ta sameni daki sallah magariba nayi na jira isha nayi kafin na shiga wanka na fito na gyara jiki ranan banjin cin abinci bread da gesha gwagwani nake so shi muka zuba a plate na dan kara garin yaji mukaci. Saidai su sun kara da abincin ranan dana aje masu don Aminu bai wasa da cikinsa abinci yake kwasa sosai abinshi. Tunda na gane haka kuma nake shake mashi abinci a kulansa sai yaci ya koshi tas yake share abincin sai kula. Ashe dayaje can gidan ya shiga gaida mama take fadin yau ko ya bace hanyane yazo da yamma gidasu tunda matarshi ta hanashi kula kowa nasa yanzu sai ita kadai da yan uwanta ? Yan uwanta kuma wasu yan uwansu ke zuwa wajensu kuma mama tace nasani malam kaban mamaki kwarai wallahi da wanan yarinyar har zaka iya zama ta juya ka ? Nasan zaka dawo ai tunda nima ban zauna ba don ba zan saka ido ina kallo na haifawa yan daji kai ba su suka iya balleni ? Iyawan me kuma mama dama kwanakin dana diba ke nan zanyi a wajenta don irin hakkurin da tayi dani da banda lafiya na kuma ba Asmau hakkurin hakan kafin naje kuma ta yarda da hakan itama. Inma kinje wani wajene akan hakan mama sunci kudinki a banza wallahi kafin yacigaba ta katseshi da fadin . As,maun me can don Allah ana batun mutanen arziki Asmau wayau da ita ko wauta koma meye saina nunaqa yarinyar nan tayi kadan wallahi. Dama tafi yar uwarta rawan kai ko a yanayinsu ba daya bane da yar uwarta don yar uwarta na boye halinta zaki dai bata kudinki ga banza mama. Kawu dai ya sauya maki halin ki a yanzu da karfi da yaji wallahi irin abin nan baida kyau mama komai mutum yace bai barwa Allah sai wanin Allah yafi masa wanan hanyar halakace babba wallahi. Au ashe kai malaminefa mai da,awa ai ban sani ba