Sashe 78
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wai habune aka fada a bayanshi jin hakan yasa ya tsaya cak yana dube dube ko zaiga wani fuskan sani ya kirashi. Saidai ba alaman wanda ya sanshi a wajen hakan yasa ya dauka bashi ake nufi ba ya kara yunkurawa zai shiga motan. A daidai lokacin ta karaso tana fadin Garba sadauki garaba gagare Abu bakari mazan fama baka shedani ba ko ? Yanzu kan yasan dashi take magana a lokacin don haka ya dakata tare da juyowa gareta duk da baudaden halinsa dabiansune gaida nagaba dasu. Ina wuni yayi mata cikin ladabi ta amsa tare da fadin kwana biyu shekaru da yawa Habu ba zaka shedani ba duk ku din kuna a raina don abinda na hango a zurian ku. Uwarku tana da yawan sakaci ga mantuwa habu tun a lokacin naso tazo na fada mata abinda ke faruwa bata zoba har nabar garin ku. Banfa ganeki ba boyar Allah ya fada yana kara kallonta sai tayi dan dariyan manya tace kagani na ganeka kuwa ni mutum ce da bani raina alheri komai kankantarsa idan anyi min. Balle alherin ka dakai da uwarka yasa naji ina dai son in taimake ku duk da nasan abin ya faru ko dan uwaka yanzu. Don yanzu haka yana kwance a gida rai a hannun Allah kuna shiga kuna fita kuna bata kudin ku a banza. Duk da kamar warkansa yana hannunka a yanzu amma baku san da hakan ba don mantuwa irin naku. Haka kuma cutarshi na jikin ku habu yana biye daku sauda kafa ako yaushe matukar ba wanan sadakan aka bada ba. Duk da akwai hannun maki don abune da yayi yawa a tare dashi shiya nasa ya kaishi kwance amma ko ku baku tsira ba gaba dayan ku matukar ba wanan sadakan aka biya ba. Ba na fada maka a ranan tafiyan ka a kofar gidanku ba na fadama alherin ka da nasara yana inda ka dosa a lokacin tabbas nasan zaka hadu da wani abin alheri a can da zai iya fin karfin abinda ke bibiyan ku. Wanan kawun naku yasan komai kuskuren daga gareshine shiyasa yake jin nauyi a yanzu yadda zai gyara kuskuren nasa. Haka kuma ku din kuna da kariya daga Allah don kuna da alheri sosai kaida dan uwanka harma ince shiya fika. Cikin yardan ubangiji kuma kayi nasara a nan Habu don baka bar alherin naka ya salwanta maka, ba a lokacin don a yanzu haka kana tare dasu a hannu . Matsalan saidai kada ka yarda kai sakaci irin na dan adam kamar yadda iyayyen ku sukayi a baya11q. Kallonta yayi kafin ya katseta da fadin Mama kece matar nan mai maciji da tazo gidan mu a baya ko ya tambayi matar cikin mamaki ? Sai yaga tayi murmushi tana fadin nice naso fada maku komai a lokacin tun hakan ba faru ba amma mahaifiyar ka bata maida hankalinta ba. Zanso kubar yarinyar nan ta bashi maganin hannunta don mai gaba daya akai mashi itace zata iya kwatoshi ba tare da komai ya sameta ba koya sameshi. Amma bayan ita duk wanda zaice zai taimaka maku akan matsalarsa karyane hakan saidai maishi yaci kudin ku kawai. Nata dai din shine maganinsa don shi wanda ya bata makarin bai san iya amfanin shiba dabai bata ba itama tayi arziki dauko wanan abin daga wata kasa zuwa wajen ku. Ka tambayi dan uwanka dake kwance zai fada maka komai don yasani a yanzu babu maganin da yake sha da yake mai amfani kamar wanan da take bashi a boye. Mahaifiyar ku kuma ka fada mata nace inda ta nemo haihuwata tayi gagawan zuwa ta biyansu sadakansu idan ba haka ba an dinga bibiyan ku a cikin sauki sauki ana halaka ku. Su kuma wa,yan nan yaran dake cikin ku a yanzu sune saukinku dob kamar kariyane a wajenku. Saboda abinda ke bibiyan naku basu iya masu komai akwai alkawari a tsakanin su dasu tun na asali amma suma basu sani ba akwai dafa,i a jikinsu dashi kuma ake haifansu . Ko wani mahaluki daka gani a duniyan nan akwai wani sirin rayuwa a baya a tare dashi tun na kakaninsa saidai yai ta mafalkin abin ya dauka mafalkine kawai. Saidai mutanen yanzu basu sanshi ba kamar na da saboda wayewan kai da suke amfani dashi a yanzu sun watsar da komai na baya. Wanan yasa kaga ciwo yayi yawa ga dan adam naba gaira ba dalili da asibiti saidai su camfa kawai don su lalaba mutum. Don haka kuma muddin suna tare daku a gida daya wani mugun abu ba zai taba cin maku ba sai alheri saiko idan aka samu akasin hakan kamar yadda ya samu dan uwaka din. Falkawa yayi yana zufa duk da sanyin AC dake dakin amma zufa yakejin yana tsiyayya mashi abinda ya gani a mafalkin nasane ke dawo masa wace yarinya ke nan wai ake nufi ? Amma zai gwada tambayan J din kamar yadda ta fada yaji idan da wata yarinya dake bashi magani basu sani ba ? Idan har hakan gaskiyane dole ya fadawa mama dubu wanan magana asan abinyi shi wanan maimagini na Niger abinda ya fada masu ke nan duk yadda akayi wanan abin yana da salsala daga mama din ke nan. Allah Allah yake gari ya waye ya nufo gida don yana katsina yai wanan mafalki duk da ya dauka karyan mafalkine hakan don dadin barci amma zai gwada tambayan J din kamar yadda matar mafalkinsa ta fada. Abinda ya faru tun haduwansu da matar ya kama dawo mashi sabo gashi kuma shi J wani lokaci saiya kama salinta jikinshi na saba irin na macizai. Abinda da daure kai a cikinsa duk yadda mutum yai tunane abin ya wuce hakan gareshi Allah dai ya bada lafiya kawai za ace. Watau akidar nan ta mutanen baya kakannin kakannin mu da sukai ta shirka wa yan nan abubuwa suke bibiya wani lokaci don suna biye da zuri,a har karshen duniya don alkawarin da aka dauka a kansu. Shine zakiji ana fadan wani nada iska ko wance iskansu na gadone ai ko wani ciwo ya kamashi ba a san takamaimain ciwon ba Allah dai ya kyauta kawai za ace. Mafi A,a lah shine bawa ya koma ga Allah a kula da addua da sadaka da taimakawa bukata nakasa dakai komai kankantan alheri wata rana sai hakan yai maka rana. Da irin wanan tunanen a zuciyarshi ya shigo garin zaria kai tsaye gidansu yaiwa tsunke inda maigadi ya bude mashi get yai arba da kawu dake tsaye yana waya. Suma ido suka zubo mashi suna mamakin dawowanshi a ranan don ya fada masu sati daya zaiyi a can saiya tsaya yaga komai ya kankama ga aikin gidan man nasu da akeyi. Sai gashi kwana guda sunga ya dawo garin kuma koda ya fito mota wajensu ya nufa suna mai barka da hanya ya runsuna ya gaishesu. Lafiya dai ka juyo yau kawu ke tambayansa yace lafiya kawu wasu takarda zan dauka kuma sai an bincika yasa na dawo da kaina. To aida sauki hakan sannu da hanya na dai dauka don jikin dan uwan naka kajuyo kuma ince Jafar kan jikinshi Alhamdullahi jiki a na samun sauki sosai ai. Mikewa yayi zuwa part din ya J din inda ya samu Nafisa na shara ni kuma ina mopping a bayanta ya shigo muna gaidashi da hanya. Ya amsa muna tare da shigewa dakin da dan uwan nasa yake kwance da sallama dan juyowa yayi yana kallonshi yace Habu ka dawone ? Na dawo J ya fada yakai zaune saman kujeran dake gaban kadon yana fuskantarshi yayi mai ya jiki shi kuma yana tambayanshi hanya ? Jiki da sauki ya fada a hankali cikin yanayin ciwo ya dan kura mashi ido na dan lokaci kafin yace J akwai wata yarinya dake baka maganine bayan su mama ? A hankali ya juyo kanshi ya kurawa dan uwansa ido yana nazarin fuskansa da tambayan daya jefa mashi kafin ya mirgina kai gefe daya yana fadin . Meyasa kake tambayana hakan ina son in tabbatar ne kawai don wanan zancen na dawo garin nan amsa kawai nake son ka bani ? Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin ya furu iska daga bakinshi bayan dogon nazarin daya gama a kasan zuciyar shi don bai san dalilin tambayan da dan uwan nasa ke mashi ba ? Akwai ya fada a takaice yana kawar da kansa gefe daya don sauraren abinda zai fada din game da zance. Wacece ita J ya kara jefa mai tambayan shiru na dan lokaci kafin J din ya juyo gareshi cikin tsare gida yana fadin kai inda aka fadama basu sanar dakai ko wacece ba. A,a sun daice in tambayeka kasan hakan zaka fada min ina son sanine don a tsaya ga magani daya ba tare da dora wani ba akan hakan. Ok to Rahama ce ta wajen ka tace daga gida aka bata makarune amma sirine bata son wani yasan da tana min amfani dashi kada a fahinceta ta bai bai amma gaban Nafisa ta fada min don kafa hujja koda wani abu ka iya tasowa. Rahama dai Rahama kanwar maria Rahaman nan dai dake waje na itace kuma naji sauki sosai don tunda na fara shanshi gabban jikina suka daina ciwo hakama kaina . Da wanan abin dake rike min makogorona duk yanzu na daina jinshi sosai a jikina karfin jikin ne dai da banda. Rahama ikon Allah Rahama dai dama abinda ake yawan nuna min ke nan akansune shine alherin da ake nufi tabbas hakan ne kuwa don a wanan tafiyan na hadu da maria. Kana yawan mafalkin ke nan kai ma ban taba dauka ita bace amma ina yawan ganin rabin fuskan maishi tana neman taimako a waje. Idan nazo in taimaka mata sai kuma inga nita taimaka saidai ban dauki wanan mafalkin da ma,ana ba sai yanzu da kake wanan maganan . Amma idan Rahama ce kuwa ,,,,,,, Me Rahaman tayi muryan mama dake shigowa ya baiyana a dakin da sauri ya habu ya dago yana fasin zancen aikin da yaran nan keyi mukeyi mama . Ki duba yadda cikin yan kwanakin nan yaran nan biyu kacal sun gyara wajen nan haka gwani ban sha,awa dashi wallahi. Ai kaidai bari kawin kuma saida