Sashe 264
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
je gunsu ba a cikin sati biyun da yayi a gidan mu. Duk da dama ba fita yakeyi ba illa iyaka dai idan wasu da baiso shigo mai gida suka zo shine yake fita kofar gida ya samesu. Saida yayi sati ukku cur a gidana ranan kwatsam naga ya kira yazid yana fadin yazo ya kaishi gida ya dubu su daya gama shiri kuma yace min sai ya dawo. Sai bayan fitansu nake ji a bakin Aminu daya shigo gaida mu da kwana yake tambayan uncle fa nace ya fita yaje gida yau. Sai naji yace dama iya tace in fada mashi yayi kokari yazo don rikicin kawu da uncle yazid da sukeyi da sauri na juyo ina fadin rikici kuma akan me ? Yace to ni dai naji kamar ana fadin rikicin kudin gadonsu uncle da mama saratu wai kawu din ya cinye masu kudinsu na gado. Wanan magana babbane ashe naji iya tace uncle yazid yana da gaskiya ita kuma mama tana fadin uncle baida mutunci. Allah ya kyauta nace dashi na karasa da abincin ka yana kitchen ka dauko ya mike zuwa kitchen din ya dauko a nan falo ya zauna yana cin abincin nasa. Yake ban labari akan zaman su yaya barakha da kishiyarta shike fada min yadda tayi da kudinta itama da aka raba ta karba. Yadda mijinta ya cinye kudin kaf babusu babu dalilinsu a yanzu ga kuma ba zaman lafiya a tsakaninsu yanzu ya kare da fadin kowa gari ya sani da kudin ya kara aure ai. Haba dai Aminu haka na yuyuwa kuwa ya dauki kudinta ya kara aure dashi shine ya shiga ban labarin irin rikicin da akayi lokacin auren. Yaya bai dawo gidan ba tun safe har dare nina daukama ya koma canne sai gashi wajajen magariba ya shigo kwatsam kuma na gaidashi ya amsa ya samu waje ya zauna a cikin gajiya. Na mike tsaye naje kitchen na dauko mashi ruwan gora da kofi na kawo mashi gabanshi ya dube ruwan yana fadin anya kuwa zansha ruwan nan banci abinci ba tun karin safene a cikina fa ? Na waro ido cikon mamaki ina fadin garin yaya kaiko kasan fa jikinka ba lafiya ko banza ni magani da bakasha bama shine nake tunane ai ashe har abinci bakaci ba. A kasale yake fadin kinsan Asmau bata da wayau taga na wuni a gidan ko ruwa ban samu ba a wajenta balle abinci ina can muna fama da rikicin yazid da kawu tun safe don yazid yakai kawu koto. Subbahanallahi na fada cikin kaduwa yace wallahi na mike ina fadin Allah ya sauwaka na nufi kitchen don dauko mashi abincin rananshi dama na aje muci da darene. Na dawo na zuba mai na zauna a kusa dashi ya soma ci yana fadin kinsan yazid tun ranan da sukazo nan da mama tace mashi wawa shine yayi fushi ya samu kawu gida sukayi ba dadi zancen kudinsa. Kudinsa ke wajensa ke nan ya dauki ruwa ya kora ya aje yana fadin duk abin nan baki sani ba a nan ya koro min kan zancen tun farko. Shi nake fada maki wanan kawu din ba mutumin kirki bane ya dade yana cutan mu ai yanzu mama ta gani koda yake duk abin nan kamar bayansa take goyo har yanzu. Yanzu sunso nasa baki nabawa Yazid kudin don rashin tausayi bayan kudin dayasa mama tayi ta karba da sunan nema min magani yana debo ganyen banza yana kawo muna. Shine na nuna masu ni a yanzu banda komai ga yazid ya hau gashi gobe za a koma kotu shine hankalinsu ya tashi iya kuma taki sa baki a zancen. Sai cewa tayi yaje ya nemowa yaro kudinsa duk inda ya sakasu jin haka ita kuma saratu ta sawa mutane kukan banza munafuka kamar bada ita aka shirya hakan ba. Na salima na fada masu yanzu kudin sun kusa ninkawa don na kara mata kudi a lokacin ake juya mata abinta lafiya lau. Lalai yau ashe kunyi shari,a babba ni karshe dai don kada suce zasu jani gobe zuwa kotunsu na nuna masu banda lafiya don haka ba zanje ko ina ba. Amma yaya dakasa baki a zancen ko baka bada kudin ba a maida case din nagida zaifi shiru yayi yaci gaba da cin abincinshi. Saida ya gama yake fadin nasa baki in biya ke nan hakan ya nuna bansan zafin kaina ba tun lokacin ai ido nasa masu nasan haka za a kare don nafisu sanin waye kawu ? Amma ita mama sam kome yayi daidaine a wajenta saboda ya gama da ita shida wanan bakar matar nasa hafsatu munafuka ke nan ta karshe. Dazun iya ke fada min ta kamasu suna fadin wai kece kikazo min da farar kafa komai ke samuna a yanzu nan iya tayi masu tas ta fita. Wa,iyazu billahi ni kuma nikan me nayiwa mutanen nan haka basu kaunata ina ruwanki da kaunar wasu tunda ni ina kaunarki. Nagane nufinsu ba yau ba duk abinda suke kitsawa a kunnena yake basu sani ba Allah dai ya ban lafiya donsu yanzu a zatonsu duk na koma banda komai tunda basu ganin ina facaka irin da. Addu,a nayi a raina Allah ya bashi lafiya ya koma harkokonsa da yakeyi Allah kuma ya buda mashi fiye da baya ubangiji ya fitar dani daga zarginsu. Ashe in ba a son mutum komai ana iya mashidon kawai a bata mashi suna nikan naga makirci ga mutanen nan da shekaruna bakai ace ya dauka ba. Amma nasan na farko mace tasa tsoron Allah a cikin lamarinta na biyu kuma ta rike gaskiya komai dacin ta ta kama kanta da mutuncinta ta zauna lafiya da kowa. Mun gama ya mike don yin alwala nikan cike da bacin ran wanan kazafin daya fada min suna min gashi Yanda tunda sukazo da yara sau daya ta dubani bata dawo ba har wanan ranan ni kuma banje gidanta ba. Saidai mukan danyi waya da ita wani lokacin ta kirani ko ni in kirata hakan kuma ban saka komai a raina ba iyaka na dauka a yadda ta dauka din tana gudun ace mun hade kai. Ko wani magana ya tasone ace da ita don ita tun muna yara Allah yayita da ruwan ciki sosai a cikin mu don tsoronta har ya baci donshi yasa ma nasa a raina zan daina biye mata don bafa zata gyara ba. Anty salma na kira akan zancen ta bani shawara tare da kwantar min da hankalina akan zance na in sharesu yadda nakeyi su da kansu zasu biyoni. Indai daure in fita batunsu kada kuma in fasa alheri ga wanda yazo wajena inda nake. Mun gama na kira yar aikin ummah itama mukasha hiran mu ta fada min wasu dabaru namu na mata da zan kara dauka. Ya shigo ya sameni kwance muna waya da ita yake fadin na zata barci kikeyi naji shiru ga danki nan ya shigo yana neman ki ! Hakan yasa na fito falon a ranan na fahinceshi sarai so yake mu kasance tare dashi dama tunda na dawo haka yake min idan yana son kasancewa dani da daren.