← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 306

Sashe 146

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya shiga tsakanina da ita tun yanzu kada ta koma tana shakkata har a zata ina mata wani mugun riko. Dakin Asmau ya kwana a ranan don saiba tunda ya shigo ta shige daki a zatonta zai biyota irin da suka saba tun tana jin motsinsu a falon har yakai ta daina ji ta leko ta samu daga shi har Asmaun basu falon a lokacin. Duk yadda taso ta taushi zuciyarta yadda kowa ke bata shawara ta kasa hakan a lokacin cikin daren nan ta kira yarta tana labarta mata abindake faru. Nan dai ta bata hakkuri akan ta bari da safe zata je gun wani malami suji yadda za ayi inya kama tazone da kanta saita san karyan da tayi tazo kaduna din suje tare. Zancen yar uwar nata ta yarda dashi har taji dan sanyi a zuciyarta inda ta kwana tana tunanen daga mijin har mu biyun don ko Asmau ba kyaleta zatayi ba tunda tagane tana munafuntar ta ko ita fitar da ita gidan zatayi ta huta da wata kishiya. Kaiya koda ta samu sa,an hakan ai wata zai dauko mata abinda mata basu gane ba ke nan don Asmau dai bata tare mata komai ba a rayuwanta. Don itace take kwarar Asmau ma idan za a fada tsakani da Allah amma tace dani din da take ganin shigowana gidan da bakar tsafi mu na fulani na juye kan miji ya koma gareni gaba daya yanzu da Asmaun da bata dauka bakin komai ba duk zatai muna kan mai uwa da wabine lokaci guda ta huta. Ita dai butinta shine ta bude ido taga ita kadaice a wajen miji sai yarta ban mantawa da case din da sukayi lokacin akan cikin da Asmaun ta samu ita bata samu ba kafin mijin ya kwanta ciwo. Case sosai akayi don saida kawu dauda shiya yazo gidan da sunan sulhuntasu aka zauna da mijin dasu akai case din. Wai ashe ita Saiba data haihu tace zatayi planning don karta samu ciki yarta karama mijin ya kaita sukaje sukai planning din. Sai gashi kwatsam taga Asmau na laulayin ciki tace sun munafunceta ita dashi ta tayar da bala,i ta hana zaman lafiya a tsakaninsu. Inda planning din ya sako mata reaction dinsa tana jini akai akai nan kuma hankali ya dawo ya tashi sukayi ta zuwa asibiti sai da kyat ta samu lafiya. Bai shigo gidan mu ba don yasan mun fita school sai karfe biyar na yamma yaje ya daukoni school muka dawo tunda na tunkaro motan naga yadda ya kura min ido nasan ya tsargu shima. Ina zuwa kan na bude motan nake cewa dashi ina wuni yaya ya mutanen gida kuma ? Ya dan washe yana fadin shigo mota mana kafin mu gaisa kya tsaya waje kina gaidani muje saimu gaisa a hanya ya bude min nashiga na zauna yaja motan muka tafi. Saida muka hau titi da kyau yake fadin ya kuka kwana nace lafiya kalau yasu mama dasu iya kuma suna lafiya iya ai tace dani wanan zuwan bazan koma ba saina kawota gidanki. Allah sarki nima haka nace ai kafin kabar gari zanje ina son zuwa na gaidasu ai don baka nan ne banje ba amma abin na cikin raina sosai. To dake da ita bansan wa zai fara zuwa ba sai kiyi hakkuri tazo gidan naki inyaso daga baya sai in kaiki ki gaidasu ko ? Abinda kace yaya shi za,ayi naga yayi murmushi ya kai hannunshi saman nawa yana murzawa yace iya sarkin rigima na kula ita kadai ke mara min baya sai salima da Habu game dake Rahama ? Nace to ayi hakkuri kowama zai mara ma idan sun fahince ka daga baya rashin fahintane a yanzu din don anyi masu ba daidai ba ?. Haba dai ni abinda ke ban mamaki dayane shine wai yadda mama ta kasa fahintar manufata har take zargin wai bani cikin hankalinane. Na zata manace zata fara farin ciki da wanan abin sai gashi makiran yaran nan sun shiga sun fita suna neman hadani da ita a yanzu kuma ? Bandai tambayeshi suwaye ba shi kuma bai fadi sunansu ba nace anty Yanda fa da Abba suna lafiya ko ? Wai maria kike nufi sai naga ya bugi bakinshi yana fadin wai sorry sister nake nufi nama rasa yaya zan kirata a yanzu sai abin ya ban dariya nace to ai surukarkace mana ba dole bane saika saya mata suna koka kirata da maman Abba kawai idan kana jin nauyintane a yanzu ? Fine sunan yayi min sosai maman Abba din zaifi sauki an wuce wajen yanzu ai maman Abba din yafi min saukin komai sosai wallahi. Bamu je gida ba naga ya dauki hanyar cikin gari wani waje mukaje ya tsayar da mota dan nisa da mutane ya fita ya shiga wajen . Ya dan jima a ciki sai can na hangoshi ya fito da ledoji ga wani a bayansa sun nufo wajen motar mu kai tsaye ya bude bayan motan aka loda mai kayan a ciki ya sallami wanda ya rakoshi din yana mai godiya. Yana zama yake fadin sorry na barki zaune ko na danyi murmushi na dago kai ina fadin ai baka jima sosai ba ya tayar da motar muka bar wajen. Mun hau titi yake fadin naso na dan tsaya in saiwa Asmau magani jiya taban tausayi sosai da dare shine naso in biya in karba mata magani wajen abokina. Bari dai in saukeki sai in dawo haba dai idan hakan yafi sauki muje mana Allah dai ya sauketa lafiya naji yace amin tana wahala sosai don tace min duk kwanakin nan haka take fama da dare. Allah ya bata lafiya na kara fada cikin rashin wani abu a kasan raina da nake tunane watau a dakin Asmaun ke nan ya kwana ba saiba ba yadda nake tunane da farko na zata gun saiba ai zai sauka ashe ba haka abin yake ba. Munje ya karbo maganin mun kamo hanya yake fadin yanzu da bakowa a gida ita habiba fa dawa take zama ke nan ? Na dan nisa ina fadin nima tunanen da nakeyi kenan a raina don nasan ta dawo tun karfe biyu gashisu anty salima basu gidan yau don da kota dawo suna gida zata samesu. Kai gaskiya hankalina bai kwanta da hakan ba don kinga diya mace ce kuma gashi ba wani gida kuke hurda dasu da zata zauna kafin ki dawo ba. Bayan haka nima ba zanso tana shige shigen gidaje ba gaskiya gara dai din a samo wata mace da idan ta dawo tana gidan tare da ita. Saidai banson kuma ai yawa a hana min hutawa na a gidan koda yake bari zan daiyi tunane akan hakan asan abinyi da zai dace. Mun isa gidan ban tsaya ba son fitsarin daya cika min marata a lokacin na shiga gidan saida na rage maratane na fito na samu ya shigo da ledojin an aje a falo. Biba kuma ta gyara gida har ta dora girki ruwa yana batu tafasa lokacin hakan yasa natsaya na tuka muna dan semo da zamuci. Haka kuma na dibar mata kayan miyan da zata daka muna inyi amfani dashi kana nafito na nufi dakinshi na sameshi yana zaune bakin gado yana waya ganin hakan na juya zan fice dakin da hannu ya kirani na dawo ya nuna min waje in zauna. Zaman nayi a gefenshi dan nisa kadan dashi kafanshi yasa ya tokaro kafata hakan yasa na kalloshi yayi murmushi yake tambayata da hannu wai na kara matsowa na make kafadata alaman a,a. Ganin zai kamuni yasa na mike tsaye da sauri na fice ina dariya kitchen na koma na samu biba ta hada miyan tana soya markade na tsaya na karasa na hada. Ina gab da karasawane naji yasa min kira a falo na amsa na fito bayan na fada mata yadda zatayi ta sauke idan yayi. A zaune na sameshi falon naji yace dani why kike guduna tun shekaran jiya Rahama na fahinci hakan. A,a ba hakana bane yaya ina dai guje muna shiga hakkine shiyasa amma ai ban gujeka ba akan me zan gujeka kuma ? Zonan ya fada yana nuna min kusa dashi duk da akujeran dake gefenshi na zauna a lokacin haka yasa na dan matsa kusa dashi din naji yace Allah sarki. Kisa a ranki mijin ki Rahama ba jahili bane duk nasan wanan kada ki tunanen hakan a kan mu don Allah baice don bake keda girki kada in tabaki ba. Iyaka dai kada mu wuce gona da irine a halaka da har zan shagala in manta da wata a gabana ko a da Rahama ni jafar banyi hakan a tsakanin abokan zamanki ba balle yanzu da shekaruna suka karu. Na san me nakeyi na kuma ji dadin hakan da kika san wanan a zuciyar ki don haka ki saki jikinki idan zaki saka amma tabaki saina taba gaskiya don ni mutum ne mai son hutu a jikin matana dake kusa dani lokacin. Ban daiyi wani magana ba yake fadin ga wanan kayab mana kira habiba ta dauke makushi zuwa ciki ki duba ki gani ban zaunu ba balle na san abinda za a karo maku na amfani. Mun gode na fada yayi murmushi tare da mamakin komai yayi min irin hakan na amfanin gida zanyi mashi godiya kamar ba kanshi yaiwa ba abinda bai saba dashiba ke nan ga matansa. Alam din wayanshi yayi kara ya dauka yana fadin bari yaje massalaci yayi sallah ya mike ashe yana da alwalanshi ya fita. Bayan ya fita na kwashe kayan naga lemukan sha masu sanyi a ciki har naman kaji da dai yan abin makulashe su yughut nakai kitchen na adana na tafi sallah. Bayan isha,i ya dawo gidan abinci nayi mai tayi baiki ba don ya samu biba tana cin nata a falon ya zauna ya soma ci yakai rabi wayanshi yai kara ina aje mashi ruwan sha a lokacin ya dauka naji yace gani tafe ya karasa cin abincin nasa ya mike. Yake fadin zan je gida wai Asmau ce ke jin jiki nace Allah sarki agaida ita dasu mama zasuji yace ya kara min saida safe ya fita.
Chapter 146 · 0% Book details