Sashe 111
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni mamaki nakeyi yadda anty salma take faman rawan kai a kaina haka sai kudi take kashi ga gyaran jiki da sauransu duk saboda zancen tarewana wanda nake sa rai bai wuce karshen satin nan da za a shiga. Duk da naji tana waya bayan mama tayi min buki a nan Abuja sai a koma can kaduna kuma ummah ta hada min walima daga can za a kaini gidan miji . Tankar ban wajen a lokacin saida ta gama wayantane ta kallo tana fadin waike haka zakita zama da angon nakine ba magana ? Shirun kifa ya fara ban tsoro Rahama aita magana kina zaune baki furta komai wanan wace irin amaryace wai ? To na dai bada dinkunan ki da zakiyi amfani dasu idan kinje kada ki fara idan kinje kice zakiyi amfani dako daya daga cikin tsofin kayan ki da aka sanki dashi gidan nan. Haka kuma kada ki yarda ki zauna gida ba kamshi ko jikin ki kwaliya ko baya gari ki kasance mai gyara Rahama don yana daga cikin abinda mazan yanzu ke so gyaran jiki. Abinci kuma nau,in daban daban zaki dinga dafawa kada kiyi rowa Rahama don haka duk wanda zaizo gidan ki ya kasance kin dan bashi wani abin sakawa a baki don Allah. Ban son ki da dogon hurda da kowansu a yanzu don kada ki yarda dayansu tace zata shige maki ki yarda sam irin hakan yana kawo matsala daga baya don haka ki kama kanki da kowa don Allah. Gidan ki babbane amma akwai maigadi kina kuma da makwabta makwabci ba kowane kake saurin yarda dashi ba balle nasan baki da matsala a wanan wajen don ke din kurace dama baki da saurin yarda da mutane. Rahama don Allah ki sauke komai a zuciyar ki kiba mutumin nan sallama abinda ya kawoshi gareki ke nan neman rayuwan inganci kada ki yarda a samu matsala a wajen ki Rahama. Kin daiji abinda mama ke fada muna kullum kada mu yarda mazajen mu su kuka damu a zuciyarsu idan muna son riban aure. Maza tankar magene sunfi taushi a inda aka san darajansu ko mutuntasu bawai ladabi da biyayya kawai ke kai mace da zama mowa ba sai mace ta iya kissa da na kwatar miji maza suna son haka kin dai gani da Alan,guguro yadda sai nayi dakyat yake barin gidan nan mu din kada ki manta da rainon mamace fa. Ya kama ace tun akan mama mun koyi rayuwa basai wani ya tsaya yi muna nasiha irin haka ba don mama a gaban mu kike ganin yadda takeyi da daddy bata hada komai da daddy ba a duniyan nan. Shiru nayi har ta gama ina saurarenta ni ina zan iya wanan abubuwan ga Jafar mutumin da ban wani saba dashi ina ma nasan abinda yake so da wanda baiso ?. Nikan dai ganinan zaki iya kirana da amaryan danko amaryan da aure yanzo mata kwatsam ba shiri shine wai ake so kuma naje na ririta mijin a hakan ? Kumshi ni kaina naji mamakin yadda kayan hadinshi ke kamshi kai mutanen maiduguri Allah ya hore masu sanin sirin kamshi a rayuwansu. Wallahi tun kamshi na damuna har nazo na saba don dole na wanka daban dana fito ga na tsuguni yana jirana haka za a yafa min wani bakin zani na zauna sai na bushe a hakan. Ina mikewa zata ban wanda zan fara murzawa a matse matse da kataruna hardasu hammata ni kaina saida na koma kamar zanyi kuka wani lokaci har kai akwai wanda tsohuwar zata rufe iya kaina da kasko tana turaramin kai in gajarce maki jin kaina nake kamar bani bace tundai da akai min gyaran kai din. Inda sumana na fulan ya samu gyara yayi baki wulk dashi sai kamshi ke tashi ga wani kasala dana zauna naji sanyi yanzune zan fara gyangyadi a wajen. Zan iya cewa Alhamdullahi Alhamdullah gaskiya dan irin ni,iman da Allah yai min lokaci guda na fahinci gaskiyan maganan da hausawa keyi na dare daya Allah kanyi bature wanan gaskiyane hakan. Cikin dan taki ubangiji yai min wani irin baiwa da ban taba sanin ina dashi ba sai a wanan lokacin gidan daddy na kwana ana gobe zamu tafi nan mukayi wani ganawan siri da mama da anty Salma mu biyu irin abinda da suka fada min a ranan yasa na kwana gabana yana faduwa. Washe gari da wuri muka dauki hanyan kaduna cikin tsalalun motocin gidan daddy dana mijin anty Salma mota hudu mukai tafiya dasu zuwa gidan mahaifiyata kaduna. Bisa rakiyan mama da yan uwa da abokan arziki data fadawa ni din yar dan uwansune daya rasu yabarmu . Manyan mata kanuri mazauna Abuja su shidda sai kawayen anty salma da ita kanta sune sukayi min rakiya mun sauka a gidan ummah anyi walima . Ni saida naji mamakin ummah ta waye ta zama yar kaduna a haraban gidansu akai walima ana gab da tashi saiga dagin ango sun iso suna bada hakkurin makaran da sukayi din. Wai ashe sai a na gobe yaya habu ya fada masu zancen tarewan wasu ma a ranan sukaji amma sunyi kokarin zuwa din duk da saida akai dan rigima don mama ta hau kawu ya samu ya lalabata tabada bakin azo din daga nan a dauki amarya. Nafisa tace yanzu mama tana can ta hake sosai taga inda za a ajekine Rahama don basu san da zancen gidan ki ba sai idan mun koma ko innata ban fadawa ba kinsan inna da surutu. Nayi murmushin yake zakice ba wani abu mai muhinmanci muke tataunawa ba da ita a lokacin don ko motsi banyi ba ina kallon yadda suka zuba min ido suna kallon sauyawata lokaci guda haka. Anzo da Salima da Saratu da sauran yan uwansu da suke uba guda karfe hudu bayan anci ansha aka dunguma zuwa zaria wajen kai amarya . Koda muka isa direct family house dinsu muka nufa saisu mama muka sama a gidan duk da gwargwado dangi sun dan taru lokacin. Wai mama tana can gidan Iya ita da wasu na kusa da ita nayi mamakin ganin harda anty Barakan zamfara ta samu zuwa bukin donni ban zata zasu yi hakan bama sai ina ganin komai makare akeyinsa ai. Hjy Yabi yar uwa kuma kawa ga mama tace akwasa a sameta can gidan daga nan a ba uwargidayena girman su kusan magariba muka kwasa zuwa gidan . A falon iya aka taru aka shiga gaisawa mama tana kallon bazata ko hajiyoyin ai abin kallone da kawayen salma. Taji mamakin ganin Salma nayi min yare ina dan amsawa a cikin kanuri iya sai haba haba takeyi damu tana kokarin ganin fuskana na boye. Tace yar fillo wayau kikai min haka kika kwace min angona ko da ina da ja amma yanzu na sake ance mai waje yazo mai aro ya tashi don haka nasake na barki da Jafar na kara noke kaina kasa cikin kunya. Hjy Yabi take tambaya ina kishiyoyin nata suke sai matar kawu ke fadin suna bangarensu ya fada maku inda za a sauke amaryan ? Basu fahinci me take nufi da zancenta ba hakan yasa sukace a gidanta mana ko ko a wani wajen ake fara sauka don su basu sani ba ko ana wani al,adane a nan ? Au ashe ya fada maku inda zaku ajeta din ai shike nan idan mun tashi daga nan gidanta zamu wuce da ita ai dama mama muka biyo nan din mu kawo mata amarya anty Salma ta fada. Basu wani tsaya ba suka mike duk da lokacin sallah yayi muka kwasa zuwa part din uwayen gidan nawa matan yaya jafar. Da irin kudansu na kanuri mai kada zuciya ya yamutsa hankalin wanda akaiwa girshi muka nufi part din matan yaya jafar din. Zakice basu san da zancen ba suna falo dukkansu muka shigo ita Asmau wani rigar abayane a jikinta sai ita saiba data saka wasu lace haka baki da adon golden jikinshi. Asmau kan tayi muna sannu da zuwa amma ita saiba ko kallo bamu isheta ba ba wani dogon gaisuwa hjy yabi ta fara fadin amaryace muka kawo kamar yadda al,ada yake . Da fatan samun zaman lafiya a tsakanin ku kuyi hakkuri da junan ku a zauna lafiya kwarai kuwa inji matar kawu ta dora da fadin amarya aiba bakuwarsu bace sun santa ta sansu. Matar kawu karma tazo da zaman lafiya mana mune dai ba wasu ba ai ta san mu mun kuma santa sai a dora inda aka tsaya. Mikewa anty salma tayi tana fadin su tashi zuje kada dare yayi muna aka barta nan tare da wasu yan gulma tana fada kamar karya. Bamu koma dakin iya ba muka nufi wajen motocinsu muka shiga ni dai kaina na rufe gwaggo Yatu najana duk abinda akeyi dai ina jinsune. Muna zama motan naji an soma fadin wai dama basu sanda zancen gidan bane anty salma na fadin bar yan iska idan basuyi hankali ba mace gidansu zata kwana ai wallahi. Sai gudan su hjy yabi ke tashi da karan motoci muka bar gidan na sauke ajiyan zuciya ina dan bude fuskana anty salma na fadin akara fesa turare wai zarni falon su Asmau keyi yasin da kyat idan batayi amai ba lokacin. Tare da matar kawu aka zo kawoni gidan dasu inna da anty Baraka basu jima ba suka tafi nan muka samu su Salima da Nafisa da maria an kawo abinci da abinsha kala kala gidan don taron baki wanda salima da Nafisa suka kai kwangilan dahuwan don fita kunya. Hjy Dubu yaron yau kaji tsoronsa kinga gida hjy dubu gida ai iyakar Aljannan duniya ke nan wannan gida ke kinga gida kuwa ? Kai lalai dan yau ka barshi inda ka ganshi ni sai ince wanan abu an dade ana shiryashi mune dai aka rufewa hakan. Kya fada kema hafsatu aisu salima na can ana sakin hanci kiji wai kamshin yar nan har yanzu dakin nan keyi don Allah kamar tana zaune wajen nan. Ga dai magana nan yana fitowa fili shine za ace wai a kyaleshi kada ai magana kada zumunci ya lalace zumunci ya dade bai lalace ba ya fito muna da hakkin mu ya bamu abin mu. In ma ya kama a saida wanan kayan