← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 306

Sashe 94

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa wasa zancen sati biyu yake batun sharewa bai gida run bayan tafiyan wuni dako kila ya kwana yabar zaria dashi sai gashi kwanansa goma sha biyu da tafiya .
Wanda yai daidai da tafiyana don tafiyana kwana goma sha,ukku ke nan yanzu hakan yasa matan yaya din a cikin damuwa .
Ga iya dake sake masu zancen cewa saboda bakin ciki sun kora mata jika ya tafi shida ba lafiya ya isheshi a jiki ba amma masifansu yasa yabar gida dole.
Irin wanan maganan da iya keyi yasa Nusaiba ta fito fili ta nuna damuwanta ga tafiyan nasa inda itama ta fara nuna damuwanta ko waya basu samun shi gaba daya ya daina amfani da sim din da aka sanshi dashi da farko .
Daga Abuja ya wuce matatar mai don yin wasu cikin takardu daya dade yana neman daman cika hannu a cikinsa.
Sai gashi kwatsam an kirashi yazo ya cika takardan an bashi daman yin hakan a lokacin don shi ya kwasa zuwa fatakwal din.
Kwanasa hudu ya gama abinda ya kaishi daga can ya nufi lagos a lagos din ya samu aiyuka da yawa da suka shagal dashi wanan yasa su a zatonsu suke ganin ya bar gidane saboda matsalan daya faru din.
Saidai Habu yana da labarin komai da yake gudanarwa don ya sanar dashi abinda ya taso masa don haka duk surutan da akeyi ido kawai Habu din ya zuba masu baicewa kowa kala ba.
Nikan na zata ya hakkura da zancenane don jinshi shiru da nayi har anty salma namin sheri wai na kore yayana da hali ya kama kansa dani.
Har take cewa Ni dama nasan za,a rina wai ansaci zanin mahaukaciya don matansa sun riga da sun girgizaki dashi Ramaah.
Dama kuma ance kuskure daya mutum keyi a rayuwansa mai ban haushi don haka shi tun farko yayi kuskuren rashin daukan mataki a lokacin.
Saidai ni a waje ke Ramaah irin matakin da yake son dauka din shine ake kira da gyaiyya don yafi wanda kika so ya dauka zafi don shi naso ki nuna masa aiba komai har su fahinci akwai kauna a tsakaninku ta gaskiya.
Amma yanzu ai ba zasuji haushin komai ba tunda basu san kunyi hakan dashi ba kuma bame fada masu balle hakan ya damesu.
Ajiyan zuciya na sauke ina lumshe idona a lokacin banjin komai a raina saina daukan fansa matukar ban dauki wanan fansan a garesu ba ina iya hade zuciyata duk sanda nayi arba dasu kuwa.
Idona da suke a lumshe na,dan bude ina kallonta nace wanan saiba din ko don ita da saare zan iya hakan a yanzu anty .
Nafisa ke fada min sunce wai kunya yasa na bar gari wai da bakinsu suke fadin sherinsu yayi aiki saura anty maria komai dadewa sai sunsa tabar gidan nan.
Kutumuu,lesi ai uban kuturu yai kadan wallahi gida kuma zaki koma cikin sa tsunbul ba maria ba har ke sai sun gani a gidan tsakiyansu kuwa.
Munyi hakan da kwana biyu na gaji sosai ranan don practical din da mukayi a training center din mu donshi ma na kwanta da wuri ranan.
Misalin sha biyun dare a daidai wanan lokacin wayata dakr ajiye a karkashin filo ta dinga kara da alama kirane ke shigowa a lokacin.
A cikin barci naji sautin karan yana shiga kunnena tare da verbiration din da yake fita daga wayan.
Dan guntu tsuki naja tare da mika hannu cikin magiyan barci saboda dadin barcin da nake ji a lokacin.
Jikina gaba daya tsami yayi nakai hannu na dinga lalubo wayar kasan filo ba tare dana tsaya duban mai kiran nawa ba na kara a kunnena bayan na dauka.
Muryan yaya na tsinkayo yana fadin Ramatu Rahama tabbas kinci sunan ki don na fara sheda hakan a gareki.
Ai na zata ba zaki daga wayan ba saboda dare yayi duk da dai dare baiyi ba a wajen matafiya ni gani nan yanzu haka airport ina jiran Jirgin mu ya tashi.
Kalman da yake fada din yasa na gane yana shirin tafiyane wani waje lokacin shirun da yaji nayine yasa ya kara fadan hello kina jina kuwa ?
Da kyat na iya bude bakina da yai min nauyi na amsa da ina ji yaya Allah ya tsare hanya aje lafiya a dawo lafiya Allah kuma ya bada sa,an tafiya.
Masha Allah nagode kwarai Rahama kece kadai na kira a duk yan uwa ina sheda maki zancen tafiyan nan don ina kyautata zaton jin hakan dama a gareki.
Rahama ke din Alherice a gareni sosai na fahinci hakan a yan kwanakin nan tabbas akwai alheri a taraiyana dake Rahama domin naga hasken dake tunkaro rayuwata tun zancen nan bai kankama ba sosai a tsakanin mu.
Kiyi hakkuri da yayanki Rahama ki karbi bukatata dani dake din taraiyan mu akwai alheri sosai a cikinsa in sha Allahu zakice na fada wata rana.
Kinsan meyasa nace hakan a gareki dole kinsan ina da dalilin hakan dana fada don kuwa nina san irin farin cikin da Allah ubangiji ya jefani a cikinsa cikin yan kwana kin nan.
Rahama abinda na dade ina mafalkin samunsane Allah ya banshi a wanan lokacin .
Don haka zuciyana taban ke din alherice a garemu baki daya don bani kadai ba kowa dake kusa damu wanan alherin zai shafa insha Allahu.
Kalaman dayake fada min sunyi matukar daure min kai a lokacin saboda ban fahinceshi ba sam don haka sai nake fadi a yar siririyar murya da Allah ya kara tabbatar muna da alherin ya amsa cike da jin dadi da amin Rahamata.
Sai naji abin wani bambarakwai a kunnuwata wai nice yaya yake kira da Rahamarsa haba dai maza ashe haka suke saboda soyayya sai babban mutum ya zamo yaro a gabanka.
Akwai wayewan kai a yar fahintan da naiwa rayuwan mutum biyu a yanzu ma,ana miji da mata ko saurayi da budurwa.
A tsakaninsu akwai kyautatawa da burge juna a lokacin taraina koda akwai sabanin hankali idan Allah ya hada wanan burgewan yana nan a zukatansu.
Jin nayi shiru na shiga dogon tunane yasa yake fadin kina jina Rahama ina son dana dawo wanan tafiyan in sha Allahu za ayi komai a tsakanin mu.
Fatana ki kwantar da hankalinki ki cire wani shakku da tsoro a zuciyar ki kada ki tsaya duban rayuwan wani ki duba tamu da nake kokarin ginawa a yanzu.
Sam ban yarda da tsarin anty Salma na cewa ki zauna a hostel ko a kama campus ba nafi bukatan kai tsaye ki dawo Zaria a matsayin matar jafar.
Gabana naji ya fadi da wanan kalman da sauri na tareshi da fadin a,a yaya don Allah kayi hakkuri ban taba wanan tunanen ba kuma ba zanyi a yanzu ba.
Kai din a yayyuna nake daukanku yaya ba irin wanan zancen a tsakanin mu don Allah kamar yadda ka fada a baya ba a daukan hukunci a cikin fushi yaya.
Haka kuma matanka basuyi karya ba yaya kaidin ba tsaran aurena bane sun fadi gaskiya da sukace naje na nemi daidai dani dan daji.
Nima ai daga dajin asalina yake ko habu bai fada maku asalin mu daga kauye mahaifin mu ya fito yazo nan zaria ba.
Sun san kin fisu da komai Rahama hassadan hakan yasa suka sakaki a gaba har sherinsu ya haska min hanyan da ban gani da farko saida kalamansu ya haska min hanya sun kwakwasa min kofa da zan bude sabon shafi a rayuwata.
Don haka a cikin kalamina Rahama ba gudu ba ja da baya don a shirye na fito da makamaina kan mai uwa da wabi zanyi lokaci guda.
Kasake nayi ga bugun zuciya dake harba min lokaci guda tunane barkatai suka taru min a kasan zuciyana .
Tabbas idan na samu yaya a miji na more a rayuwata saidai bahaushe yace ana barin halas don kunya dolene naki karban tayin yaya a kaina don tsira da mutuncin yar uwata dake aure a gidansu .
Yau badon hakan ba kai tsaye zan amsa tayin nasa sai dai wani sashe na zuciyana yana mai ban shawara da mai zai hana inbi shawaran anty salma ko girgiza imanin su indanyi.
Muryanshi naji yana fadin zan barki Rahama an fara sanar muna da mu karaso kusa jirgin mu yana kan layi.
Saina samu muryata da fadin to yaya Allah ya kaika lafiya ya bada sa,ab tafiya amin Rahamata in kuma dawo lafiya in sameki a shirye da tarona.
Muka kashe wayan da karfin gaske nake jin zuciyata ta bugawa hakan yasa na sauke ajiyan zuciya ina lumshe idanuwa tunane barkatai nayisa a lokacin kan in yarda ko kada in yarda .
Washegari da safe haka na tashi ina jin zuciyana tayi min nauyi don kwana tunanen dana zaunayi dogon riga dinkin dinkin atamfa mai A sharp na saka a jikina sai dan karamin gyale dana dora a kaina .
Abujane fa birnin taraiya Abuja ko dame kazo anfika saidai kayi naka banjintar ka bari wani yazo da tasa kalan .
A falo na samu anty Salma zaune tana ba yaranta abinci tun daga fitowana take fadin oya zo na zata ai kina kwancene wanan dan naki dan rigima wai ba zaici abinci ba haka zai tafi school da yunwa.
Murmushi nayi na karasa na karbi abincin a hannunta ina lalashin yaron kafin ya soma karba yaci daga hannuna har suka gama na rakasu har bakin mota suka tafi.
Falon na dawo don sai goma zan fita tana waya na kwashe kayan zuwa kitchen nakai na fito bayan mun gaisa da yan aikinta dake dauka ni din yar uwatarcen ta jini kamar yadda take fada a kaina din
Don haka suke kirana da small hjy zama nayi a gefenta din ta juyo tana fadin kai Ramaah wai kinga yadda kikayi wani fresh dake kuwa wanan aiko yau kika koma zaria ba zasu ganeki ba
Waini kan ya zancen mutumin nakine kwana biyu banji zancensa ko kin fita batunsane wai gaskiya Rahama ina sonki da guy din nan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

3️⃣5️⃣
Chapter 94 · 0% Book details