Sashe 306
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
amma tarbiya ba guda ba kowa na fadi. Dan matsalan da aka samu shine fadan da akayi da Saratu yaya Habu kuma yaci mata mutuncu tun ranan akan naman laiyane datace wai naman da aka bata bai mata ba tazo har gida taci min mutunci ina fada mata ni banda labarin komai akai su yaya suka raba aka aiko min tace attabau laifinane tunda yaya ya bar muna shanu da raguna shine don an raunata za a kawo mata nama kadan. Karshe dai na biye mata mukayi cacan baki da ita Aminu ya kira yaya Habu yazo gidan ya sameta yaci mata mutunci sosai tabi hanya tana kuka. Da yaya ya dawo yaji abinda ya faru yaje nemanta ashe tana jin ya dawo ta gudu ta boye bata yarda sun hadu ba dashi. Labarin abinda ya faru da mama suna dawowa yabi gari nasan kuwa yan gidane ke fada akaji aka sauya zancen kawu yazo taron ta don anyi belinshi shi yake tambaya ashe haka tasha matsala a can tace eeh nasan ba komai bane Allah yati min haka in gane gaskiya. Yaron nan Jafaru Allah ya kara mashi albarka dashi da zurianshi jafar yayi min komai duk da Jafaru danane dole in nemi gafaranshi ko alhakinsa da ake sa inci yana hanani ganin rahama a rayuwana. Baidai ji dadinta ba ranan har ya tafi zance zuwa makkan nan ya kawowa mama sauyi sosai a rayuwanta dkn naga zuwata biyu gidan mu ko tsaraba ita da kanta ta kawo muna har gida ta kuma wuni a nan ita da anty barakha sai dare suka koma gida. Asmau ta dawo makka ta samu nasa yara makaranta inda na koya masu abubuwa da dama dole tasan yaran sun samu natsuwa a yanzu abinda banji dadi ba shine da taso ta nuna min wai tafi a yanzu. Ko don tana ganin taje makka ni bai kaini bane oho sai taso idan an hadu tayi min irin sakin maganan nan na gugar zana na daiyi gaba na baya sai hange a raina nace taji dashi nasan abin da nakeyi ni. Mama bata ragawa sararu ba kan abinda tayi min gashi taji ga Aminu mijinta tazo kwanashi ukku a gidan lokacin da basu nan hakan ya batawa mama rai tace sai ta koma dakinta. Ta kira kawo tace ta gaji yaba yara kudinsu ita ta gaji da abin kunyar dake faruwa hakana yayi mamaki sosai da mama ta iya budan baki ta tambayeshi kudin . Gaba daya yasan komai ya lalace mashi a yanzu gareshi wai ashe dama akwai kaddara da mutymin nan ya boye yana jiran abu ya lafa ya fito dasu yaci bulus duk da dai ba duka aka samu kudin ba sun dai samu abinda suka samu a wurunshi yazid yace ya hada da gidan iya ta mara mashi baya ya karbe gidan. Ashe ya biya muna makka ni da salima nafisa lawisa kanwarsu yar wajen ummah sai matar yazid da maria sai kannisa maza su ukku da zamu dasu dashi kanshi. Kiri kiri yaki biyawa saratu makka kamar zatayi hauka yace bai biya tunda bai isa da ita ba ga auren yayan yaya barakha da za ayi kafin tafiyan mu makka din Ni ba abinda yai min dadi sai yan uwana maza da karatun su yanzu yaci gaba a nan da dawowansu a kusa dani yayi muna dadi sosai yaso ya hada da ummah muje mijinta yace shi zai biya mata ta bangareshi tunda yana dashi. Anyu buki da sati ukku muka fara shirin tafiya mama taso Amir ya zauna hannuta amma yaya yaya yace mama zata zo ta zauna dasu a gida da yar wajen yaya Ai babba. Haka Asmau tace akawoshi gidansu yace a,a shine hakam ya dan hadasu hatsaniya tace yaki ya kawo mata dana amma ita ya kwashi nata takai min na zauna dasu. Yace yakai daya kai din bashi ba har ita taji dadin ganin yaran yadda suka dawo suka samesu ai don haka ba zai kawo Amir ba ta kashemashi shida yunwa nata ma ya kwashesu yakai ma mama dubu yace har ya dawo. Dole ta kyale muka tafi muka sauke farali munyi aiki sosai muna can labari yazo muna dan wajen Asmau ya fada tankin ruwa ya mutu. Hankalinmu ya tashi sosai da jin hakan shiya fara tambaya ai gidan ba tankin ruwa wai ashe bayan rafiyan mu uwar tazo ta kwashesu taje dasu gidanta wai zasuyi sallah a can shine wanan abun ya faru dashi. Haka muka dawo cikin bacin rai saidai nikuma muna dawowa ciki ya baiya a gareni ciki na biyu ke nan haka nayi ta fama lauyi ga tajiigindin duniya wanda ba a rasawa a kullum dake faruwa na haihu lafiya na kara samun namiji again nan kishin Asmau ya tashi saida yaya yayi mata iyaka dani ta shiga hankalinta. Na kusa haihuwa kuma ciwon yar wajen Saiba ya tashi itama ta rasu nan hankalina ya tashi sosai Allah dai ya taimakeni na haihu a lokacin. Na dan huta da haihuwa don tazaran shekara ukku ban haihu ba nasake samun wani cikin na haifi wani dan yanzu haihuwana biyar da nake maki labarin nan shagunana biyu manyan store daya a nan zaria daya a kaduna. Sau daya muka hadu da saiba ba don farin sani ba ba zan shedata ba muna dakin yaya kubura wajen buki suka shigo wai suna tallan kayan mata tunda tayi arba ta gan mu nuda Yanda da matar yazid da yanzu muke aminai ta saka kafa ta fita falin bamu kara ganinta ba. Sai dai ince Alhamdullahi don muna zaune lafiya da Asamau Allah kuma yana ta budawa mazajen mu Saratu daice a gida itama auren yaki ta koma tafito har sau ukku a karshe dai auren ya mutu iya kuma ta amsa kiran mahalincin mu muna da shekara biyu da dawowa makka lokacin. Alhamdullahi da fatan an dauki wani darasi a cikin dan takaitattacen labarina na fahinci rayuwa bai tafiya ga mutum daidai sai tare da dan uwansa da duk maison ya ga haske a rayuwa ya rike zumunci in mace ko namiji don naga hakan a rayuwan gidan mazajen Alhamdullahi muna cikin rufin Asirin Allah sosai a yanzu fiye da lissafinki mai karatu da fatan zaki yafeni inda nayi kuskure Allah ya bamu ikon cikawa da imani amin ya Allahu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA.
ZAINAB IDRIS MAKAWA.