← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 304 OF 306

Sashe 304

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zance dai tun ana ji kamar karya saiga abu ya tabbata Alhazai sunata shirin tafiya saudiya don yin ibada wa yanda sukai nasaran zuwa sune yaya Auwal da ya Isah yaya barakha da Asmau matarshi su mama su hudu sai iya da yaya Rukkaiya. Kamar yadda ake samun kalubali idan haka ya faru dole sai anyi tsegumi shima ya samu a wajen mahaifiyarshi don ta nuna rashin jin dadinta tayi fada don me zaikai har mutum uku maka dakin mama lokaci daya ga dan uwanta da suke uwa daya uba daya bai kaishi ba ? Kome kawu yayi mashi dai jininsune don shiyasha nono ya sake mata baiyi magana ba a lokacin don sai ana gab da tafiya aka san masu sauke faralin ya hana kowa ya fito fili ya fadi donshi kowa ya kama bakinsa da zancen. Saida ta kara tayar da zancen a gaban yan uwansa gashi ga habu ga yazid ga iya dasu salima ta soma korafi akan ya nuna mata yanzu yakai tunda har dan uwanta badai daraja a idonsu ya biyawa kowa nasa makka yaki biyawa dan uwanta don ya tozartasu . Ace dakin mama harsu ukku zai biyawa makka mama tudu ta fitane gareshi ko takaita daraja a wajenta a,a mama kada kice haka don Allah ? J da kike gani ni yanzu ban iya cewa komai akanshi yasan dalilin da yayi hakan a garesu ba wani magani ko munafuncinsu daya cishi. Mutanen nan suna nunawa a gaban kowa shi dan dakinsu abinsa idan ya taso tun baikai haka ba sai idan karfinsu ya kare akanshi da baida lafiya nan gaban kowa yaya Ai take kuka tana fadin dama ita aka dorawa ciwon bashi ba. Akwai soyayyan dayafi wanan har dan uwanka zai sadaukar da ransa akanka ka kasa mashi komai matar nan tana iya kokarinta damu tun muna kanana yanzu haka yadda yaran mu suka saba da maman tudu mama basu saba dake ba hakana don hattaransu da kikeyi akan uwayensu mama kikan manta da yayan mu jininkine su ?. Shi kuma kawun da kike magana a kai kowan mu nan yasan irin ta,asan da kawu yaiwa rayuwanki ya haniki zaman lafiya damu yayan ki haka kuma bai son ganin cigaban mu wanan a baiyane yake kowa ya san hakan mama don haka kada ki matsa muna kan kawu don Allah kawu dan uwankine ba dan uwanmu ba . Kai habu ka shiga hankalinka kafin na fyatoka daga hancina ba yau ba na kula dakai da tsatsauran ra,ayinka akan yaya idan kai ba zaka taimaka mashi ba ka bari wanda yayi niyar hakan yayi. Tunda shi Yazid yace ba zai taba yafe kudinsa dake hannun yaya ba ga kuma Saratu yanzu ta taso da zance kudinta take so ta koma gidan mijinta tunda kunki taimaka mata ku . Yaya J yana zaune yanata charting bai dago kai ya dubesu ba amma hankalinsa na kan abinda kowa ke fadi wurin a lokacin saida yaji yazid yace mama kudin nan kudinane fa ? Ubana ya mutu yabar min gadon su kuma banyi da kowa nace abashi kudina ba wanda yai fushi da matakin dana dauka ya biya mashi man in rabu dashi matukar bai biyani ba wallahi sai yayi fursuna akan kudin nan haka kawai zaiyi na iya kyaleshi koshi sai ya biyani a lahira don ban yafe mashi ba. Nasan zaka aika donshi nake son dan uwaka ya biya kudin tunda na fahince kai abin kunya baya gabanka yazid nemansa ma kakeyi ka yafa. Aban kudina in rika mama yadda kowa ya rike nasa nima in rike abina nagaidai babu ruwanki cikin zancen idan kuma za a biya mashine a ban kudin yanzu. Shirun da yaji anyi a falon yasa ya dago kai kallonshi sukeyi a lokacin yasa yace wa wai dani ake maganane banji ba ? Ka daiji abinda yake fada game da kawunku idan ya matsa zankai ga mashi baki yasa nake kyale yazid da iya shegenshi. Baki kuma mama akan kawu zakiyi mai baki har idan kinyi muna hakan ai kamar kin cutar da rayuwankine mama ka bashi kudinsa tunda tozarci yake neman muna. Ni mama a,a ba wanan akawarin a waje ko kin manta daga ina kudin suka fito suka koma hannun kawu da har yanzu kudin suna hannuna da sunfi abinda ake nema yanzu a kawu. Kawu da munafuka din nan saratu nan suka tasaki gaba da sunan cewa kudin nake wandaka dasu har naje na auro Rahama. Ni auren Rahama gareni alherine ba tsiya ba tunda ina ganin haske ga taraiyana da ita akan me zan dauki kudina ince na biyawa kawu kudin yazid . Ai gara in nayi niyar taimakawa yazid din insan kyauta na bashi kudin da biyan bashi ba mutumin da bai kaunar ya ganni da rai zan biyawa bashi mama ba wanan zancen kuma tsakanina dashi gaskiya inda yakai mashi kudinsa ya fito dasu don sunan a boye tunda ba abinda yayi dasu. Barakha dai tunda ta rokeni gafara ta kuma fada min dalilinta na goyon bayan haka ita kan bance ban taimaka mata ba yanzu. Auren Rahama bani kadai ba duk wani wanda yake tare dani ya karu dashi amma aka rufe ido akaso tozartani cikin duniya saida Allah ya rufa min asiri ban taba taba wanan kudin ba da sunan wani abu a rayuwana don nasan irin azabab da Allah ya tanadar akansu. Ya basu kudinsu ko kuma yaje gidan yari akansu ni wanan ba zancena bane gaskiya don ban cikin maganan tun farko an tsameni a zancen yanzu ko idan nasa kaina ninaso hakan . Duk abin da kowa yayi min ina sane ina dai hakkurine a zauna lafiya amma kada mutum ya daukan ban fahinceshi ba kai Habu kwanan nan bada jimawan nan ba na kiraka akan ka taimaka min da kudi muna asibiti da Rahama za ayi mata aiki kememe kaki kulani balle ka taimaka min. Shiko yazid dana kirashi cewa dani yayi shi ina yaga kudi zai dai turo min dan abinda yake dashi ya turo min da dubu hamsin sai bare wanda ban hada komai dashi ba ya iya ban dubu dari hudu lokaci guda ga barakha da bata aikin komai sai sana,an hannu ta iya turo min da dubu dari. Kai ammako anji kunya haka akayi baka fada ba iya kona fada maganin me fadin zai min a lokacin tunda badashi banda wanda zai ban . A tunane shi dan uwa Allah kan baka sune don rufin asirin juna sai yanzu na fahinci abin a yanzu ba haka yake ba don kowa kanshi ya sani a yanzu. Wanan zance kamar almara fa Jafaru daga habu har shi yazid da bazarwa suke rawa a yanzu bada taka ba da har zaka shiga hali haka su kasa taimaka maka ? Gasu ai shiyasa na fada a gabansu yanzu ba kawune kadai yayi min abinda ba zan manta ba har dasu da nake gani rabin rayuwatace su don na shiga jerabawa suka iya min hakan. Dubu kingani ko kinga irin abinda nake fada maki ko kinga abinda matsalolinki suka jawowa rayuwan ki tun kina raye kin daiji irin abin ko ? Na fada maki irin halaiyan nan na banza bi mutum suke su nadeshi su shafi har wanda baiji bai gani ba yau ina laifin yaron nan a wajen ku ? Kai Habu ya dago da idonsa da sukai ja yace ni nasan anyi hakan amma ban dauka cewa abin serious bane sosai a lokacin yasa ban turo kudin ba amma yayi hakkuri don Allah ? Ba dole ba dole yayi hakkuri idan baiyi hakkuri ba kasheku zaiyi tunda hamnuka bai rubewa ka yarda. Wai iya baki bari ayi magana kin hana sai kace kece mama dakuwa tayiwa salima din tana fadin daga uwar naku harku waye silan zuwanku duniyan nan. Iya munzo akan zancen auren salima ina son kafin tafiyan ku insha Allahu za ai aurensu jin hakan yasa mama dagowa da sauri tana fadin sati biyu kamar hauka ? Aure haka ba shiri komai a dai bari har Allah ya dawo damu lafiya zaifi yace wani shiri mama ki dai sakawa yarki albarka amma duk wani shiri ai an gama komai ina ganin yanzu abinda ya saura sai wanan cincin din da kukeyi din nan ai koshi na gama da wanan bangaren ko insha Allahu komai na saya. Shine zuwa kanon da mukayi kwanaki dasu zaman su gida haka yana damuna saida ta nisa tace angama komai kace fa a bangaren ka ko shi ya gama ginansane ? Ya gama ina ganin yaushe sukace zasu kawo kayan akwatunama yana tambayan kanwar tashi tace yace a cikin satin nan dai zasu kawo. Allah dai ya saka maka da alherinsa yasa kafi hakan a rayuwanka jafar kayi yadda duk akeso ayi Allah ya baka zuria masu rama maka ya amsa da amin . Itama mama ta amsa tare da fadin har ita Nafisan ke nan yace insha Allahu wanan dan uwan mahaufiyarta dayaje karatu waje ya dawo dashi za ayi a nan kaduna zai ajeta. Wani nisawa mama tayi ta shiga dogon tunane can ta dago tana fadin amma wanan duk tsarinkane ko tunda ka gaji da ganinsu gida ? In ma tsarinsane aina alherine tunda aure ya hada Allah kadai yasan ladan da zai samu a wanan abinda kayi Jafaru Allah ya biyaka da alherinsa kaji. Mikewa J yayi yana fadin to mama mu zamu tafi wa yan nan dana lissafa maku sune zaku tafi tare bana saudiya insha Allahu badi kuma idan ranmu yakai sai a duba wa yanda ya dace suje. Mama bata iya magana a lokacin don yadda zuciyarta yayi mata nauyi da zantukan da sukayi dasu na kawu yafi tsaya mata a rai yadda har suka tashi yaran gaba daya suka tsani dan uwanta a yanzu. Yadda yace hakan ya faru ansha buki ankai amare komai nasu iri daya saidai kala daya bambamta da kuma abinda kowa ya sayawa kanshi anyi lafiya an kare lafiya amare sun tare dakinsu abin gwanin ban sha,awa dasu. Saratu kuma tasha zunde hakan yasata zama daki don ta zama mujiya a cikin mutane yawan zunde yasata boyewa don wanda ma bai sani ba sanadin bukin nan yasan abinda ya dawo da ita gida. Bayan an gamane dama mama
Chapter 304 · 0% Book details